A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci – Ganduje
Published: 8th, May 2025 GMT
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Nijeriya.
Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa a ziyarar jaje ga gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a kan harin da aka kai wa rundunar sojijin barikin soja da ke Buni Gari.
Ganduje ya ce dole ne yaƙi da ’yan tada ƙayar baya da ’yan fashi da makami su tafi tare da haƙiƙanin lokaci domin samun nasara.
Ya bayyana cewa abin takaici ne irin yadda ’yan tada ƙayar baya da ’yan fashi suke aikata munanan ayyuka a faɗin ƙasar nan.
“A yanzu za a yi amfani da albarkatun da ake da su don maye gurbin irin kayan aikin da aka lalata.”
Da yake jawabi, gwamna Buni ya ce gwamnati a matakai daban-daban na duba yadda ake amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.
“Mu, a matakin ƙasa da gwamnonin yankin Tafkin Chadi, muna yin nazari sosai kan yadda maƙiya ke amfani da jirage marasa matuƙa aikata ta’assar wadda dole mu haɗa kai da jami’an tsaro don duba matsalar,” in ji Buni.
Ya ba da tabbacin cewa za a tattauna hakan a mataki mafi girma musamman da shugaban ƙasa domin daƙile ayyukan tada ƙayar baya da ’yan bindiga.
“Wannan matsala ce ta ƙasa domin a lokacin da suka kai hari a sansanin soji da kuma ƙwace makamai, ba za a iya sanin inda za a yi amfani da su ba, don haka ya kamata a ɗauki waɗannan hare-hare a matsayin hare-hare ga al’ummar ƙasa baki ɗaya ba wai Jihar Yobe kaɗai ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abdullahi Umar Ganduje Gwamna Buni
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu a daren ranar Juma’a bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari da bam a wani wsjen cin abinci da ke garin Konduga, a Jihar Borno.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin.
’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a KanoYa ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji na gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Ya ce, “Wani mutum ya kutsa cikin taron mutane da misalin ƙarfe 10 na dare tare da bam, wanda ya tarwatsa kansa kuma ya kashe sama da mutum 10.”
Wani masani kan ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa mutum 24 ne, suka rasu a sanadin harin, inda ya ce mace ce ta kai harin ƙunar baƙin waken.
Ya ƙara da cewa fashewar ta yi tsanani wanda sai kan matar aka samu.
Bayan harin, an tura tawagar sojoji, ƙwararrun masu binciken bam na ‘yan sanda, ’yan sa-kai, da ƙungiyar CJTF zuwa wajen.
Sun yi bincike amma ba su samu bam na biyu a wajen ba.
An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) domin a kula da su.
An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin kuma likitoci sun tabbatar da rasuwarsu.
Makama, ya ce ana ci gaba da tantance sunayen waɗanda abin ya rutsa da su domin a miƙa gawarwakinsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza.
Kai harin ƙunar baƙin wake na ɗaya daga cikin dabarun da ƙungiyar Boko Haram ta fara amfani da su a farko-farkon fara ta’addancinta a Najeriya.