2025-07-13@07:28:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1100

«daya daga cikin»:

    An nada Dabide Ancelotti, dan gidan tsohon kocin Real Madrid kuma kocin babbar tawagar kasar Brazil Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin Botafogo, in ji kulob din na birnin Rio de Janeiro, Ancelotti, mai shekaru 35, ya shirya fara aikin horarwa na farko bayan ya zama mataimakin mahaifinsa a kungiyoyin Real Madrid, Eberton, Napoli da Bayern Munich. Zai maye gurbin Renato Paiba wanda aka kora bayan Botafogo ta fice a zagayen 16 na gasar cin kofin duniya, Dabide Ancelotti ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa karshen shekarar 2026, ya koma kasar Brazil domin kasancewa cikin masu horar da ‘yan wasan kasar Brazil tare da mahaifinsa, amma an sauke shi daga matsayinsa don ba shi damar karbar ragamar horar da...
    Dakarun rundunar “Shahid Izzuddin al-kassam’ da kuma ” Sarayal Kuds” sun sanar da kai jerin hare-hare akan sansanonin ‘yan sahayoniya a yankuna mabanbanta na Gaza. A bayanin da dakarun ” Kassam” su ka fitar sun bayyana hare-hare masu yawa da su ka kai wa ‘yan mamaya, da su ka hada da tarwatsa motocin buldoza biyu samfurin D9 a unguwar Zaituna a cikin birnin Gaza. Haka nan kuma sun kai wani harin a ranar 6 ga watan Yuli wanda su ka rusa tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar amfani da wata nakiya mai tsananin fashewa. Bugu da kari , Kassam ta ce a ranar 9 ga watan Yuli din ta kai wani harin akan sansanin da kwamandoji masu bayar da umarnin...
    Gwamnatin Adamawa ta ayyana dokar ta baci ta hana zirga-zirgar mutane na tsawon sa’o’i 24 a Karamar Hukumar Lamurde da ke Kudancin jihar. Bayanai sun ce wannan lamarin na zuwa ne bayan samun rahotannin mutuwar kimanin mutane hudu a wani sabon rikici na kabilanci da ya auku a yankin. Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil Sanatan Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC DW ta ruwaito kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje yana ba da shaidar matakan da suke dauka domin dakile rikicin. Kazalika Kwamishin ’yan sandan jihar, Dankombo Morris ya kaddamar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin. Kana Kwamishinan ya ba da umarnin jibge ’yan sandan kwantar da tarzoma a yankin...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan kwashe makonni biyu, inda ya ziyarci ƙasashen Saint Lucia da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X. Sanatan Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025 don ziyarar aiki a waɗannan ƙasashe biyu. Da farko ya je Saint Lucia domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Caribbean, da kuma ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen kudancin duniya. A ranar 4 ga watan Yuli, Tinubu ya tashi daga Saint Lucia zuwa Brazil, inda ya halarci taron BRICS...
      Ko za ka iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a Unguwar Adakawa cikin birnin Kano, na yi makarantar firamare a Adakawa, daga nan kuma na tafi zuwa makarantar sakandire (Gwammaja One), bayan na sauke Alkur’ani, daga baya na tafi sai na wuce zuwa ‘School of Health Technology’ ta Kano. Bayan nan, sai kuma na tsunduma harkokin kasuwanci da siyasa, kazalika ina da mata biyu da kuma ‘ya’ya goma a halin yanzu.   Kamar wane irin kasuwanci kake yi? Ina harkar takalma ‘yan Kofar Wambai, wadda ita ce sana’ar dana fara koya, sannan kuma ita ce sana’ar da dangina suke yi.   Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Tun ina yaro...
    Ya jaddada buƙatar samar da tsarin adalci da zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar cin moriyar ci gaban fasaha da samun rance cikin sauƙi daga ƙasashen duniya. Ya kuma bayyana yadda Afirka ke fuskantar manyan matsalolin muhalli duk da cewa ba ta fitar da gurbataccen hayaƙi sosai. A gefe guda kuma, Tinubu ya bayyana shirye-shiryen gyaran da gwamnatinsa ke yi, ciki har da amfani da makamashi, yaƙi da sauyin yanayi, gina birane da kuma inganta harkar kiwon lafiya ga kowa. Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran ƙasashe masu tasowa. Jawabin Tinubu a taron BRICS na 2025 ya nuna matakin farko da Nijeriya ta taka a matsayin ƙasa mai ƙawance da BRICS. Nijeriya ta...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya tunatar da cewa a bara, Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a ya nemi fassarar doka daga Kotun Ƙoli, inda kotun ta tabbatar da cewa kundin tsarin mulki ya tanadi ’yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi.   “An samu hukunci daga babbar kotun ƙasa da ke nuna cewa kundin tsarin mulkin mu ya tanadi buƙatar ƙananan hukumomi su samu ’yancin kai – su kasance masu cikakken iko da damar aiki a fannoni daban-daban, ko siyasa ko kuma kuɗi,” inji shi.   A cewar sa, bai wa ƙananan hukumomi dama za ta ƙarfafa dimokiraɗiyya a matakin ƙasa da kuma samar da cigaba a cikin al’umma.   Idris ya nuna damuwa kan yadda tsarin ƙananan hukumomi ya raunana a tsawon lokaci,...
    Wasu da ake zargin Jami’an Hukumar Farin Kaya (DSS), sun kama fitaccen mai barkwancin nan a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Sun kama shi ne bayan isowarsa filin jirgin saman, wanda hakan ya jawo hankalin mutane da dama, ciki har da fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin. DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar Jos Sai dai Ɗan Bello cikin wata hira ta wayar tarho da ya yi da kafar DCL, ya bayyana abin da ya faru, inda ya ce: “Dana sauko wasu mutane wanda kana ganinsu ka san hukumomi ne...
    Hukumar Tsaro ta DSS ta saki matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano. Jami’an DSS sun kama Dan Bello ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kuma wasu majiyoyi na zargin daga Abuja jami’an suke. Aminiya ta gano saukar matashin da ke zaune a ƙasar China a Najeriya ke da wuya jami’an DSS suka yi awon gaba da shi. Sai dai kuma rahotanni da muka samu daga bisani sun nuna cewa jami’an tsaron sun sake shi, bayan ya yi ’yan mintoci a hannunsu. Bayan nan ne Ɗan Bello ya wallafa hotonsa da tare da matashin lauya ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima a cikin mota. A ƙarƙashin hoton da ya wallafa...
    Hukumar Tsaro ta DSS ta saki matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano. Jami’an DSS sun kama Dan Bello ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kuma wasu majiyoyi na zargin daga Abuja jami’an suke. Aminiya ta gano saukar matashin da ke zaune a ƙasar China a Najeriya ke da wuya jami’an DSS suka yi awon gaba da shi. Sai dai kuma rahotanni da muka samu daga bisani sun nuna cewa jami’an tsaron sun sake shi, bayan ya yi ’yan mintoci a hannunsu. Kawo yanzu dai babu bayani daga hukumomin tsaro ko Ɗan Bello game da dalilin tsarewar da aka yi masa da kuma abin da ya wakana tsakaninsu....
    Wata majiya ta tabbatar da cewa, a yayin da tsohon shugaban majalisar dattawan ya je Jihar Binuwai domin daurin auren jikarsa, “watakila zai yi ganawa da shugabanni da masu goyon bayan tafiyar a shiyyar.” Aregbesola ya samu tarba daga magoya bayansa a lokacin da ya isa Jihar Legas jim kadan bayan kaddamar da jam’iyyar a Abuja. A nasa bangaren, Atiku ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC na jihar Gombe a Abuja karkashin jagorancin tsohon minista kuma Sanata Idris Abdullahi a Abuja, a yammacin ranar Juma’a. Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa shugabannin jam’iyyar “sun dawo ne domin tuntubar yankunansu tare da kafa hanyar kulla alaka da jama’a yadda ya kamata.” “Yan Nijeriya sun riga sun yi taro,...
    “Bayan ’yansanda sun yi gaggawar shiga yankin domin kwantar da hankulan jama’a tare da dawo da zaman lafiya, a halin yanzu akwai mutane shida da ake zargi suna tsare a kan lamarin.” Ya kara da cewa, ‘yansandan sun hada kan shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya wajen tattaunawa, wanda hakan ya taimaka wajen kwantar da hankula. “Bayan faruwar lamarin, sai muka gana da shugaban al’umma a wurin, sarkin gargajiya yana tare da mu, muka tattauna kuma muka yi kokarin gano abin da ya faru, suka tabbatar mana da cewa za a wanzar da zaman lafiya,” in ji shi. Ya ce har zuwa ranar Alhamis, Kasuwar Gosa ta koma ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tsauraran matakan sa ido kan ‘yan...
    Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna. Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu Haruna, ya shaida wa Aminiya cewa direban da ya ɗora wa masara buhu 463 domin kaiwa kamfanin Olam da ke Ilorin a Jihar Kwara, ya gudu da kayan. “Kuɗin kayan sun kama Naira miliyan miliyan ashirin da ɗaya da dubu ɗari shida da tamanin da shida da ɗari huɗu. “Wallahi jarin nawa ke nan ɗungurungum na dora a motar,” in ji ɗan kasuwar, wanda ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba. Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya kai sama da kashi 30 cikin 100, duba da cewa; noman da ake yi a karkara na ci gaba yin karanci. Idan har an rabar da wadannan Taraktoci yadda ya dace tare da horar da manoman da za su amfana, an kuma tabbatar da ana bai wa Taraktocin kulawar da ta kamata da sayar da su cikin rahusa, hakan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.” Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya ga munanan ayyukan da HKI take aikatawa wanda yake cin karo da yarjeniyoyin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.” Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; Abinda Jamus din ta aikata zai mayar da ita wacce za ta amsa tambayoyi a matsayin wacce take yin zuga a aikata laifi. A lokacin da HKI ta fara kawo wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hare-hare dai shugaban...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa na shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma sauran al’ummun duniya. Kowa ya san yankin Taiwan wani bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma wannan shi ne matsaya daya da al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 ciki har da jama’ar yankin Taiwan da yawansu ya kai miliyan 23 suka dauka, wanda kuma ra’ayi ne daya tilo da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai. Sanawar Alkahira da sanarwar Potsdam da dai sauran takardun shari’a sun aza ingantaccen tubali ga dokar kasa...
    Rundunar sojan mamaya ta sanar da kashe  daya daga cikin jami’an sojojinta dake karkashin rundunar “Golani” a yankin Khan-Yunus dake Gaza. Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin mamayar HKI su ka snar da cewa wani daga cikin mayakansu mai mukamin  Captain ya halaka a Gaza, kuma tuni sun bude bincike akan abinda ya faru. Rahoton tashar talabijin din ” Cane” ta HKI ya ambaci cewa, sojan da aka kashe yana cikin wadanda su ka kai hari a garin Khan-Yunus a jiya Alhamis. Sojojin mamaya sun kai hari ne a cikin wani gida a ci gaba da kashe ‘yan gwgawarmaya da suke yi, sai dai ginin gidan ya rufta da su, bayan da nakiyar da take cikinsa ta fashe. Tun...
    Taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan, mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya”, ya ja hankalin baki daga kasashe da yankuna 140 da suka hada da ‘yan siyasa da ministocin gwamnatoci da kuma wakilan bangarori daban daban, inda suka yi musayar ra’ayin tare da cimma matsaya a fannoni da yawa, da kuma fitar da sanarwar Beijing, bayan kammala taron. Sanarwar ta bayyana cewa, mu’amalar wayewar kai muhimmin karfi ne wajen inganta ci gaban wayewar kan bil’adama da bunkasuwar zaman lafiyar duniya. Kuma ya kamata kasashe da kabilu daban-daban su...
      A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari. Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna...
    Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta musu dakile harin. A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin Bayero ya taba bi ta wannan hanyar ba. “Bayan isowarmu daga gidan Dantata domin jaje, wasu matasa sun mamaye titin da duwatsu da makamai a Kofar Kudu. “Lokacin da muka isa Kofar Kudu, sai suka fara jifan mu, amma aka yi sa’a, mun yi nasarar fatattakar su zuwa cikin gida, kuma...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu ci gaba da kai wadan nan hare-hare har zuwa dakatar da kissan kiyashin Falasdinawa a Gaza. Yahyah Saria kakakin sojojin kasar ta Yemen sun bayyana cewa, sojojinsa sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistic maim  suna Zulfikar wanda kuma ya fadi a kan tashar jiragen saman na Lod Airport kusa da Yafa ko tel’aviv. Ya ce makamin ya sami bararsa kuma ya sa...
    Ƙwallon da Chinwendu Ihezuo ta zura a minti na 89 ya isa ya kai babbar tawagar mata ta Nijeriya da akeyiwa lakabi da Super Falcons zuwa matakin Kwata Fainal na gasar cin kofin Afrika ta mata da hukumar CAF ke shiryawa ta shekarar 2025, Super Falcons ta doke kasar Botswana da ci 1-0 a wasan da suka buga yau Alhamis da karfe 8 na dare agogon Nijeriya a Casablanca. A fafatawar da aka yi a filin wasa na Stade Larbi Zaouli, Ihezuo ce gwarzuwar wasan, sakamakon kwallo daya tilo da ta jefa a ragar kasar Botswana dake Kudancin Afirika, Nijeriya ta lallasa Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga, duk da cewa an tafi hutun rabin lokaci...
    Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adam. A cikin sakonsa, Xi ya jadadda niyyar Sin na hadin gwiwa da kasashe daban-daban, don tabbatar da shawarar raya wayewar kan duniya bisa tushen adalci, da koyi da juna, da mu’ammala da yin hakuri da juna, ta yadda za a kafa nagartaccen tsarin mu’amalar wayewar kan bil Adam a duniya, matakin da zai gaggauta bunkasa wayewar kan bil Adam, da bunkasar duniya cikin lumana. Shugaba Xi ya kuma yi fatan mahalarta taron za su zurfafa mu’amala, da cimma matsaya daya, da taka rawar ganin wajen karfafa cudanyar al’ummun kasa da kasa, da...
    Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da Amurka take bawa HKI yasa tana da hannun a kissan kiyashin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan umurnin takunkuman da aka dorawa Francesa Albanese, jami’a mai kula da tattara bayanai na musamman a kan Falasdinu ga hukumar kare hakkin bil’dama da MDD. Rubio ya bayyana cewa sanadiyyar rahoton ta ne kotun ICC ta fidda samacin kama Banyamin Natanyaho, da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yoav Galant. Banda haka takan bada rahoto kan yadda Amurka da...
    Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan  sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren. Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari. A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
    Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata. Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni. Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100. Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe. A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da ‘ya’yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma...
    Babban sakataren kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya godewa shugabancin JMI, wato Imam Sayyif Aliyul Khaminaei kan goyon bayan da yake bawa kungiyar babu kakkautawa don yakar makiyar kasar HKI. Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon, a karon farko tun bayan shahadr shugaban kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah a shekarar da ta gabata. Babban malamin ya kara da cewa, taimakon da Imam Khaminae yayiwa kungiyar Hizbullah, ya kai matsayinda ba zamu tambaya, ko roka ba. Musamman bayan fara yaki a cikin watan Octoban shekara ta 2023, kuma ta bada wadannan taimakon ba tare da ta shiga yakin kai tsaye ba. Sheikh Qasem ya bayyana cewa, bamu...
    Wannan nasarar ta sa Chelsea ta ƙara samun kuɗi fam miliyan 22 wanda ya ƙaru kan fam miliyan 60 da suka riga suka samu a gasar. Hakan yana nuna cewa suna samun riba daga siyan Joao Pedro da suka yi a fam miliyan 55. Fluminense ta nuna rashin jin daɗi lokacin da alƙalin wasa ya soke bugun daga kai sai gola da aka ba su, bayan duba na’urar VAR. Amma Chelsea na fuskantar damuwa da yiwuwar raunin ɗan wasan tsakiya Moises Caicedo ya samu. Chelsea za ta kara da Real Madrid ko Paris Saint-Germain a wasan ƙarshe a ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.”   Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba.   “Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta...
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa mai shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma yaudarar jama’ar duniya. Ko Lai ya manta da cewa, a ran 19 ga watan Mayun da ya shude, shekaru 9 a jere ne babban taron hukumar lafiya ta duniya WHO ya ki yarda da shirin da wasu kasashe tsirraru suka gabatar na halartar Taiwan taron. Yawancin kasashen duniya sun nanata matsayinsu kan kiyaye kudurin babban taron MDD mai lamba 2758, da nace wa ga bin ka’idar kasar Sin daya tak a duniya,...
    Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya. Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada...
    A matsayin sabon babban manaja, Musa ya buƙaci haɗin kai da goyon bayan kowa don tabbatar da gaskiya da amana a dukkan harkokin kulob ɗin. Ya kuma roƙi magoya bayan ƙungiyar su ci gaba da marawa kulob ɗin baya a wannan sabuwar tafiya ƙarƙashin jagorancinsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.   Yana...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
        Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bukaci hukumomin tsaro da Sarakuna da kuma kungiyoyin matasa su dauki matakan gaggawa wajen dakile gina gine-gine a karkashin manyan layukan lantarki da kuma hana lalata kayan hasken lantarki.   Babban Manajan TCN na Yankin Kaduna, Injiniya Nasir Mansur Fada, ne ya yi wannan kira a yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar da masu ruwa da tsaki a hedikwatar TCN da ke Mando, Kaduna.   Taron ya samu halartar Sarakuna da jami’an tsaro da kungiyoyin masu zaman kansu domin bin umarnin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa domin ci gaba da kokarin da TCN kiyi na dakile mamaye filayen layin lantarki da kare dukiyoyin kasa.  ...
    Kakakin ma’aikatar harkokin  wajen kasar Iran Isma’el Baka’e ya yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen a ranar Lahadi. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya litinin ya kuma yi tir da hare-hare kan a Hudaydah, Ras-Isa, as-Salif da kuma tashar wutan lantarki na Ras al-Kathib. Har’ila yau Baka’ee ya yi allawadai da kai hare-hare kan cibiyar tattalin arziki na kasar ta Yemen a Hudaida, wadanda suka hada da kayakin jama’a wadanda suka hada da gadoji da hanyoyiu da tashar Jiragen sama, da tashar jiragen ruwa da kuma rumbunan ajiyar abinci. Wandanda gaba dayansu yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Hare-harin...
    NiMet ta ce duk wanda ke zaune a wuraren da ruwa ke taruwa ko wuraren da aka bayyana yana da haɗari da su koma wuri mafi aminci. An kuma shawarci jama’a da su tanadi kayan gaggawa kamar abinci mai yawa da ruwa da kayan taimakon gaggawa da fitila da na’urar adana lantarki ta ‘power bank’. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
    Kamfanin dillancin labarun “Reutres” ya bayyana cewa; Cibiyar da take tafiyar da ayyukan agaji a Gaza, wacce Amurka ta kafa ta, ta bayar da wata shawarar da take cewa; a kafa wa mutanen Gaza hemomi na wucin gadi da za su zama masomin yin hijirarsu zuwa wani wuri daban, a cikin yankin ko a wejensa. Rahoton kamfanin dillancin labarun na Reuters ya ambato wata majiya mai karfi tana cewa; An gabatarwa da shugaban kasar Amurka shawarar tilastawa mutanen Gaza yin hijira, kuma a cikin kwanakin nan an tatauna wannan batu a fadar mulkin Amurka ta “White House.” Har ila yau rahoton ya kunshi cewa,tun daga watan Febrairu cibiyar ta fara kokarin tara kudaden da za su kai dalar Amurka biliyan...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin mamaya  Nasir al-Lahham, a gidansa da yake a garin Beithlaham. Majiyar ta kara da cewa; Jami’an kungiyar leken asirin ta “Shabakh” sun dade suna binciken dakin watsa labarin da Lahham yake watsa shirye-shiryensa. Tashar ta “Almayadin’ dai ta bayyana cewa kamun da aka yi wa ma’aikacin nata yana a karkashin Takura mata ne da HKI take yi, domin a cikin watan Oktoba na 2023 ma dai jami’an tsaron sun kai hari cikin gidansa, su ka ci zarafin maidakinsa da kuma kama ‘ya’yansa Basil da Baasil.
    Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi. Shafin labarai na Isra’ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da matsaloli masu alaƙa da damuwa da kuma rasa abokai biyu a yaƙin na Gaza. Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno TRT ya ruwaito cewa an gano gawar sojan a cikin wani daji kusa da birnin Safed a arewacin Isra’ila bayan ya kasa samun sukuni da yadda zai yi...
    Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno Turji: Gwamnatin Sakkwato ta ba da sharadin sulhu da ’yan ta’adda Wani mazaunin...
    Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin.
    Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren  HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
    Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe  kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da ‘yanto da kasa, kuma wajibi ne akansu, ko da kuwa an dauki lokaci mai tsawo sannan kuma sadaukar da kai ya yawaita.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Isra’ila abokiyar gaba tana ci gaba da mamaye yankuna 5 na Lebanon, don haka babu yadda za a yi mu mika kai.” Haka nan kuma ya yi tambayar cewa; Ta yaya za a tsammaci za mu ki...
    Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu. Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.” Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne. “Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna...
    Majalisar Dattawan Nijeriya ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan gabanin cikar wa’adin dakatar da ita da ta yi tsawon watanni shida. Majalisar ta ce ala tilas ne dakatacciyar Sanatar ta bayar da hakuri tare da neman afuwa a hukumance gabanin cika umarnin da ta wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar na dawo da ita. Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Shugaban Kwamitin Labarai da Harkokin Jamaa na Majalisar Dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ta yanke a kan Sanata Natasha. Ya yi bayanin cewa, a yayin yanke hukuncin da ta bayar da...
    An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 192,000 tare da jikkata yawancinsu mata da kananan yara. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar harkokin wajen kasar a Quito babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza. Masu zanga-zangar sun yi kira da a kawo karshen yaki da kisan...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na Farko ya ce; Al’ummar Imam Husaini a Iran ba za su bari makiya su cimma mummunan burinsu ba Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Muhammad Reza Aref ya rubuta a cikin wata wasika cewa: Domin kare martabar Iran da kasar al’ummar Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba barin mafarkin masu kyama ya tabbata ba. Aref ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram a jajibirin ranar Ashura inda ya rubuta cewa: “Saboda Iran da kasar da tushen al’ummar Mabiya Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba bari mafarkin makiya...
    Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi. An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga...
    Kamfanin jiragen sama na UAE airlines ko emirate ya sake farfado da zirga zirga zuwa kasar Iran bayan da aka rufe sararin samaniyar kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata. Jaridar National ta kasar Amurka ta bayyana cewa kasashe da dama a duniya sun dakatar da zirga zirga zuwa JMI saboda yakin da HKI da Amurka suka kai mata daga 13 ga watan zuyi har zuwa kwanaki 12. Labarin ya kara da cewa kasashen Iraki da Jordan sun dakatar da zuwa kasar Iran saboda yaki kuma saboda gwamnatin Iran ta hana jiragen sama tashi ko kuma zuwa kasar. A ranar Alhamis ne JMI ta gabata ne hukumomin Iran suka bude sararin samaniyar kasar wanda ya nuna...
    A baya bayan nan, firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko, ya zanta da kafar CMG ta kasar Sin, inda ya jinjinawa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wadda ya bayyana a matsayin mai cike da hangen nesa da burikan samar da ci gaba, wanda hakan ya yi daidai da hikima, da managarcin tunanin jagoranci na shugaba Xi Jinping na kasar Sin. Mista Sonko, ya ce Senegal ce kasar farko a yammacin Afirka da ta karbi wannan shawara. Kuma abu ne mai muhimmanci ganin yadda shawarar ke kara ingiza cimma nasarori ga dukkanin sassan. Sonko ya kara da cewa, cikin ‘yan shekaru kalilan, tarin kasashen Afirka sun cimma manyan nasarori na hakika, daga aiwatar da shawarar. Ya ce shawarar ba wai ta...
    Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa. Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa,...
    Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar. Har ila yau wani jirgin maras matuki na abokan gaba ya kai wani harin akan wata mota a yankin “Safful-Hawa” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. A garin Shab’a kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wani gida, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutanen dake cikinsa. Majiyar asibiti a garin Marja’iyyun ta ce an kai...
    Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai girma gwamna, da gagarumin nasarorin da ya samu a hukumance, da kuma jagoranci mai tsari da yake kai domin ci gaba da tsara tafiyar dimokuradiyyar kasa. Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8) Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren yada labarai...
    Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya amfanin da kayayyakin da wa’adin amfani da su ya ƙare, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali. Wani da ya samu kansa a cikin irin wannan hali shi ne Bitrus da ke Maidugurin Jihar Barno, wanda bayan kammala aikinsa na yau da kullum gab da almuru, ya koma gida a gajiye, ga kuma yunwa, inda ya ji cikinsa ya fara ƙugi. Kawai sai ya garzaya wani ɗan shago a bakin hanya ya sayo ƙaramar robar madarar yogot da kuma biskit domin rage yunwar da ta taso, kafin ya ci abincin dare. Sayen su ke da wuya, ya buɗe robar ya fara kwankwaɗar madarar, yana haɗawa da biskit ɗin a hanya, kafin...
    “Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban. Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000. Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000. Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa. Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan...
    An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya. Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa kan mace ta farko da ta biyu sai kuma laifin lalata da mace ta uku. ‘Yansanda a ƙasar Birtaniya sun ce ya kamata Thomas ya bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 5 ga watan Agusta, tuhumar ta biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar, wanda ya fara a watan Fabrairun 2022 bayan da ‘yansanda sun samu rahoton fyaɗen. Partey dai ya bar...
    Sheikh Na’in Kasem shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar bata bukatar Izini don kare kasar Lebanon daga makiyanta. Yama fadar haka ne ga wanda suka cika kunnen duniya kan cewa dole ne kungiyar ta mika makamanta ga gwamnatin kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Sheikh Kasim yana fada a wani jawabin da ya gabatar a ranakun Ashoora na Imam Hussain (a) ta kafar Bidiyo. Ya kuma kara da cewa wadanda suke maganar kungiyar Hizbullah ta mika makamanta ga gwamnatinsa kasar, ya fiye masu sauki su fadawa yan mamaya su fice daga kasar Lebanon su kuma dakatar da hare-haren ta’addancin da suke kawo mata. Ya kara jaddada cewa kungiyarsa zata ci gaba da rike makamanta sannan...
    A bana ake bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ana kuma daf da gudanar da sabon zagayen taron jagororin Sin da EU. Sakamakon hakan, jerin ayyukan cudanya a matsayin koli tsakanin sassan biyu na kara jan hankali. A baya-bayan nan, an gudanar da dandalin tattaunawa na manyan jami’ai tsakanin Sin da EU karo na 13 a birnin Brussels na kasar Belgium. Kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugabannin EU, tare da ziyartar kasashen Jamus da Faransa. Bangaren Sin ya jaddada cewa, bunkasar tafarkin ci gaban alaka tsakanin Sin da EU ya nuna kyakkyawar dangantakar sassan biyu maimakon adawa da juna, kuma hadin gwiwarsu shi ne...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin wasu sabbin hadimai 19 da za su yi aiki a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman domin ƙara inganta aikin gwamnati a jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu Yanzu adadin hadiman da ke aiki da Gwamna Abba sun zarce mutum 300. Hadiman sun haɗa da Masu Ba da Shawara na Musamman, Manyan Mataimaka na Musamman, Mataimaka na Musamman da kuma Masu Taimaka Masa. Gwamnan ya fara naɗa hadimansa ne a ranar 16...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun mayar da cibiyoyin bada agaji zuwa filin yakin kashe Falasdinawa a Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da mayar da cibiyoyin bayar da agajin jin kai zuwa wani mummunan tarko na aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa, wanda hare-haren baya-bayan nan da suka kai kan fararen hula sunka yi sanadiyar hasarar rayuka da dama tare da jikkata wasu masu yawa. Wannan mummunan al’amari ya janyo gargadin Majalisar Dinkin Duniya cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana kai wa masu fama da yunwa hari. Jiragen yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amfaniu da manyan bindigogi suna barin wuta kan mai uwa da wabi kan Falasdinawa da suka taru domin karbar kayan jin kai. Gwamnatin mamayar Isra’ila...
    Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ADC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Sabuwar haɗakar ta haɗa da fitattun ’yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa Sauran sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran shugabannin jam’iyyun adawa. Sun ƙaddamar da sabuwar haɗakarsu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a ranar Laraba. A...
    A ɓangare guda kuma, kotu ta samu Natasha Akpoti-Uduaghan da laifin saɓawa umarnin kotu ta hanyar rubutun zaulaya da ta yi a shafinta na Facebook a ranar 7 ga watan Aprilu, inda take bayar da haƙuri amma ta hanyar zaulaya ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Alpabio. Kotun ta ce rubutun cin fuska ne ga umarninta, sannan ta umarci Natsha da ta rubuta saƙon bayar da haƙuri a shafukan jarida guda biyu da shafinta na Facebook. Har ila yau, kotun ta ci tarar Natsha naira miliyan biyar bisa rubutun da ta wallafa a shafin na ta na Facebook. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta sami dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natsha Akpoti-Uduaghan da laifin raina kotu, sanna ta ci ta tarar naira miliyan biyar. Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta ce Natasha ta wallafa wata wasikar zambo ta ban hakuri ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, duk da umarnin kotun na baya. ’Ya’yana na da ’yancin mallakar filaye a Abuja – Wike Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC A cewar kotun, wasikar zambon, wacce Natasha ta wallafa a shafinta na Facebook ranar bakwai ga watan Afrilu, rain ice ga umarnin da kotun ta bayar a baya ga dukkan bangarorin guda biyu. A kan haka ne...
    Bayan an rufe sararin samaniyar kasar Iran saboda yaki na kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa kasar a ranar 13 ga watan yunin da ya gabata, a yau Jumma’a a bude zirga-zirgan jiragen saman a duk fadin kasar daga karfe 5 na safe zuwa 6 na yamma daga ranar Jumma’a 4 ga watan July 4, 2025. Sake dawo da zirga zirgan jiragen sama yana daga cikin matakan da hukumomi a Iran suka dauka don dawo da nutswa a cikin kasar bayan yakin kwanaki 12 da HKI. Hukumar zirga zirgan jiragen sama na kasar ta dakatar da sauka da tashin jiragen samane jin kadan bayan da HKI ta awkawa Iran da ya ki a ranra 13 ga watan yuni don lafiyar...
    Kazalika, gazawar Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da kuma sauran hukumomin na jihohi na sauke nauyinsu, hakan ya nuna a zahiri, na irin kalubalen da ake fuskanta, na rashin sauke nauyinsu, na bayar da agajin na gaggawa. Misalii, an ruwaito cewa, a sansanin na ‘yan gudun hijira na Yelwata, musamman yadda suke kwana a kan tandarmin kasa, tare da kokawa da cizon Sauro, ‘ya’yansu ke ci gaba da zama a cikin yunwa, wanda hakan, ya kara harzuka su, fita yin zanga-zangar. Bisa wasu akaluma da aka samu daga Biniwe, sun nuna cewa, a sansanin na Yelwata, an samu haihuwa 15 da kuma mata da suka samu juna biyu, su 122, wadanda kuma suke ci gaba da rashin...
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan masu dawowa daga binne gawa a kauyen Rim na jihar Filato, inda suka datse wa daya daga cikin matasan da ke wurin hannu daya. Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne wani mutum ne a kauyen Bachit da ke da makwabtaka da su inda suka yi arba da maharan wadanda suka tare su suka bude musu wuta, sannan suka datse wa daya daga cikin mutanen hannu daya. Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Wani Hadimin Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, mai suna Timothy Dantong, wanda yake cikin mutanen da suke dawowa...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin taron manema labarai na yau Alhamis, kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yongqian, ta ce ba su da wata masaniya, game da cewa shugaban Amurka na shirin jagorantar wata tawagar ‘yan kasuwa zuwa kasar Sin. Sai dai kuma duk da hakan, a cewarta har kullum matsayar Sin a bayyane take, cewa tana fatan ita da Amurka za su bi turba guda, kuma karkashin jagorancin yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka amince da su, za su rungumi ka’idojin mutunta juna, da zama cikin lumana, da gudanar da hadin gwiwar cimma moriyar juna, ta yadda za a ci gaba da cimma matsaya guda. Har ila yau, sassan biyu za su kai ga rage sabani, da karfafa hadin gwiwarsu, da bunkasa alakar...
    Kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin Iran sun shirya tsaf don kare juyin juya halin Musulunci da kasarsu A yayin ziyarar da ya kai wa iyalan shahidi kwamandan tsaron cikin gida na kasar Iran Kanal Mohammad Alizadeh; Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Jajirtattun sojojin kasar Iran a shirye suke da dukkanin karfinsu wajen kare kyawawan manufofin juyin juya halin Musulunci da kuma dukkanin yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin kowane irin yanayi da kuma fuskantar duk wani mai neman wuce gona da iri. Manjo Janar Amir Hatami, babban kwamandan sojojin kasar Iran, tare da rakiyar Hujjatul-Islam Ahmad Jalili Safat, mataimakin shugaban bangaren rukunan siyasa ta sojojin kasar, Manjo Janar Muhammad...
    Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
    Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta Jota ya rasu yana da shekara 28 a duniha. Hatsarin ya faru ne a hanyar A-52, kusa da garin Palacios de Sanabria. Jota yana cikin motar tare da ɗan uwansa, André Silva, wanda shi ma ya rasu. Silva ɗan wasa ne da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon kafa ta Penafiel a ƙasar Portugal. Rahotanni sun...
    Rundunar Sarayar Kudus dake karkashin kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da kai wa matsugunin ‘yan share wuri zauna na Sydriot hari da makamai masu linzami da su ka yi sanadiyyar kashe da jikkata sojojin mamaya.  Su kuwa kafafen watsa labarun HKI sun samar da cewa, an tsinkayo harba makamai masu linzami guda 3 daga Gaza zuwa Sydriot. A gefe daya dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da cewa sun kai wasu hare-haren da makamai masu linzami zuwa yankin Q20 a sansanin ‘yan share wuri zauna na ” Nir-Ishaq” da “Miftahim. Bugu da kari dakarun na “Sarayal-Kuds’ sun sanar da kai wa tankar yaki samfurin Mirkava hari ta hanyar wata nakiya mai karfi akan hanyar Zannah,dake gabashin unguwar Shuja’iyyah a birnin...
    Ko da yake ba a bayyana irin rashin lafiyar da ta kama shi ba, wannan bayani ya kawo ƙarshen jita-jitar da ke yawo game da lafiyar Buhari, musamman bayan da mutane suka lura da jinkirin dawowarsa daga ƙasar waje. Buhari ya bar mulki a watan Mayun 2023 bayan ya kammala wa’adinsa na biyu. A lokacin da yake shugaban ƙasa, ya saba shafe lokaci a Birtaniya domin neman lafiya. Shehu dai bai faɗi ranar da Buhari zai dawo gida Nijeriya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Ko da yake ba a bayyana irin rashin lafiyar da ta kama shi ba, wannan bayani ya kawo ƙarshen jita-jitar da ke yawo game da lafiyar Buhari, musamman bayan da mutane suka lura da jinkirin dawowarsa daga ƙasar waje. Buhari ya bar mulki a watan Mayun 2023 bayan ya kammala wa’adinsa na biyu. A lokacin da yake shugaban ƙasa, ya saba shafe lokaci a Birtaniya domin neman lafiya. Shehu dai bai faɗi ranar da Buhari zai dawo gida Nijeriya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic. A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar. A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar...
    Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus. Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba. David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Zaman ya gudana ne a harabar tsohon gidan gwamnatin jihar. Hon. Nanloong Daniel, wanda ke wakiltar mazaɓar Mikang wanda kuma tsohon jagoran masu rinjaye ne a majalisar ta tara, ya samu amincewar dukkanin ’yan majalisar 24 don jagorantar su. Daniel shi ɗan jam’iyyar APC ne. Zaɓen nasa ya biyo bayan wani zaman sirri da aka yi tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang,...
    Babbar Kotun Jihar Filato da ke zamanta a Jos, ta yanke wa dalibin nan na makarantar GSTC Bukuru, Odey Emmanuel, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe malamin makarantarsu a kan abinci. Alkalin kotun, Mai Shari’a S.J. Bakfur, ya ce an sami Odey ne da laifin na kisan kai wanda kotun ta ce ya saba da tanade-tanaden sassa na 188 na 189 na kundin dokar manyan laifuffuka ta jihar Filato ta shekara ta 2017. Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu A cewar alkalin, masu shigar da kara sun gabatar da hujjojin da suka iya gamsar da kotun cewa wanda ake zargin...
    Lokaci bai kura wa sauran kasashe na koyi da Sin ba. Sun gwada aron tsare-tsaren kasashen yamma, kuma babu inda hakan ya kai su. Don haka za su iya tsara irin dabarun da ya dace da yanayinsu domin kyautata makomar kasashensu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi. “Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka...
    Hakazakika, an zakulo Mata dalibai daga wasu zababbun makarantun sakandare a jihar da kuma wasu daidaikun Mata a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.   Da yake kaddamar da Rabon Kayan, Shugaban Ma’aikatar Fadar Gwamnatin jihar Kaduna Malam Liman Sani Kila, ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu na tallafawa Mata Da Matasa a fadin kasar baki daya.   Hakazakika, ya jinjinawa Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani bisa bubbasar da takeyi wajen tallafawa Mata Da dalibai Mata Da masa abin a Yaba ne Yana Mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta himmatu wajen ciyar da aikin Noma a jihar Kaduna.   Kila ya kuma jinjinawa Hajiya Hafsat Uba wajen jajircewata wajen...
    Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa ta bai daya, tare da raya tattalin arziki na teku mai inganci da dai sauransu. A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kafuwar babbar kasuwa ta bai daya a ciki kasar Sin ta dace da bukatunmu na bullo da sabon tsarin neman ci gaba da samun bunkasa mai inganci, don haka ya kamata a aiwatar da aikin bisa manufar kwamitin tsakiya, da daidaita ayyuka...
    Bayanai daga makusantan fitaccen attajirin nan da ya riga mu gidan gaskiya, Alhaji Aminu Ɗantata sun nuna cewa an ɗage jana’izarsa da aka shirya gudanarwa bayan sallar La’asar a ranar Talata. Yanzu an mayar da jana’izar zuwa bayan Magariba a haramin birnin Madina. Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu A wata zantawa da ya yi da BBC, Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya bayyana cewa tuni gawar Alhaji Aminu ta isa birnin na Madina. “Alhamdu lilLah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya...
    Malaman addinin musulunci daga mazahabar sunna kima 1300 sun tabbatar da cewa gwagwarmaya da HKI wajibi ne a addinin musulunci kuma wajibi ne a Sharia. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanin da malaman suka fitar bayan taron da suka gudanar na cewa tallafawa falasdinawa wadanda HKI take kashewa wajibi ne a sharia. Kuma suna kira ga dukkan malaman sunnan su gane haka su kuma bayyanawa sauran musulmi musamman ahlussa kan cewa jihadi a kan yahudawa sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasar Falasdinu wajibi ne ga wanda yake da ikon  hakan. Bayanin ya kara da cewa abinda Falasdinwa suka yi a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023M da kuma fara yakin Tufanul Aksa yana dai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin. Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ibtila’in ambaliyar. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s). Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.s) shi ne wanda ya samar da gwarazan mazaje na musamman da shahidai da su ka fuskanci ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce;  Matasan da su ka yi watsi da duniya  su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin. Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki watanni biyu bayan ibtila’in ambaliyar. Domin sauke shirin, latsa nan
    Isra’ila ta bayyana shirin ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen Siriya da Lebanon da suka daɗe ba sa ga maciji da juna a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan na zuwa ne bayan samun lafawar rikici tsakanin Isra’ila da Iran. Kasar Isra’ila ta ce za ta ƙulla hulɗa da ƙasashen da suka daɗe suna zaman doya da man ja, amma ta ce babu batun tattauna makomar tuddan Golan da ta ƙwace daga hannun Siriya. Zan yi takara a Zaɓen 2027 — Peter Obi An sanya dokar hana fita a Kaduna Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar wanda ya bayyana hakan a wannan Litinin din ya ce ƙasarsa tana da yaƙini kan karya lagon ƙasar Iran lokacin fito na fito na tsawon...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...