Karamar Hukumar Birnin Kudu ta nuna gamsuwa da yadda aikin tantance yan fansho ya gudana a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammed Uba ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an gudanar da aikin tantance yan fanshon jim kadan da kammala aikin a sakatariyar Karamar hukumar.

Yace karamar hukumar ta gamsu matuka bisa yadda aikin ya gudana cikin kyakkyawan tsari mafi dacewa.

Alhaji Builder Muhammad Uba ya kuma yabawa hukumar asusun adashen gata na fansho kan yadda take biyan hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya akan lokaci ta hanyar basu hakkokin su.

Shima a nasa jawabin, Daraktan kudi da mulki na karamar hukumar, Malam Haruna Ibrahim Kwaimawa ya godewa Karamar Hukumar bisa karamci data nuna a lokacin aikin tantancewar tare da godewa yan fanshon yankin bisa hadin kai da suka bayar a lokacin aikin.

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Yan Fansho

এছাড়াও পড়ুন:

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba

Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila.

Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Kashi 81.8 cikin 100 kuma sun bayyana cewa, “kafa kasa mai cin gashin kanta, mai cikakken ‘yanci ta Falasdinu bisa kan iyakokin da aka shata a shekarar 1967, tare da gabashin Kudus a matsayin babban birninta” ta zama wata matsaya da aka cimma a tsakanin kasashen duniya.

A cewar bayanai daga hukumomin kiwon lafiya na Gaza, hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane 65,283 tare da jikkata wasu 166,575 tun bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinu a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023. A kuri’ar jin ra’ayoyin, kashi 90.8 cikin 100 na wadanda suka yi Allah-wadai da ta’asar da Isra’ila ke tafkawa, kuma sun yi imanin cewa, ya kamata Isra’ila ta gaggauta dakatar da hare-harenta na soji a zirin Gaza. Kazalika, kashi 92.1 cikin 100 sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki tare da yin taron dangi wajen taka birki ga farmakin sojojin Isra’ila a Gaza. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin Gyaran Hanya Ne Ya Haddasa Hatsarin Jirgin Ƙasan Abuja–Kaduna – NSIB
  • Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran
  • An Yanke Wa Sojojin Da Suka Sayar Wa ‘Yan Ta’adda Makamai Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Borno
  • Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
  • An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno
  •  Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi