2025-07-01@22:57:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4365

«Miyagun Laifuka»:

    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa. Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar...
    A yau Talata ne gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gudanar da bikin daga tuta, da bikin murnar cika shekaru 28 da dawowar yankin musamman na HK karkashin ikon kasar Sin. Da yake jawabi yayin taron, kantoman yankin Lee Ka Chiu John, ya ce tun bayan kama aikinsa, gwamnati mai ci...
    Lokaci bai kura wa sauran kasashe na koyi da Sin ba. Sun gwada aron tsare-tsaren kasashen yamma, kuma babu inda hakan ya kai su. Don haka za su iya tsara irin dabarun da ya dace da yanayinsu domin kyautata makomar kasashensu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba. A wata hira...
    Wakilan kasashen duniya a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna girmamawa ga wadanda suka yi shahada a harin wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Iran Masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka da wakilan kasashe daban-daban a Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da bayanai kan mutanen da suka yi...
    Magajin garin birnin Tehran ya bayyana cewa: Karyar ‘yan sahayoniyya ya tonu na cewa ba su kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran ba Magajin garin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ali-Ridha Zakani ya tabbatar da cewa: Karairayi da ‘yan sahayoniyya suke yadawa dangane da rashin kai hare-hare kan...
    Mummunan kisan kiyashi kan ‘yan darikar Alawiyyan Siriya, kuma wadanda aka yi wa kisan gilla a kasar a watan Maris sun kai mutane 1,479 A cikin binciken da ya yi na baya-bayan nan, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cikakkun bayanai na kisan gillar da aka yi tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris...
    Tawagar likitocin kasar Sin ta 24 wadda ke jamhuriyar Nijer, ta ba da horon fasahar likitancin gargajiya ta Sin a babban asibitin Nijar dake birnin Yamai, wanda ya jawo hankulan mahalarta kusan 50, ciki har da manyan ma’aikatan kiwon lafiya na asibitin, da dalibai daga kwalejin likitanci ta jami’ar Yamai da kuma masu sha’awar likitancin...
    Yau Talata ita ce ranar cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS. A cikin lokacin sanyi na shekarar 2012, jama’ar kasar Sin sun wayi gari da ganin motocin gwamnati kalilan ne ke kai-komo a kan tituna, kuma an daina amfani da kudin gwamnati wajen shirya liyafar cin abinci a gidajen...
    Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da ƙaddamar bincike a game da harin da dakarunta suka kai kan wata cibiyar intanet da ke yankin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbin fararen hula a jiya Litinin. Hukumar kare lafiyar fararen hula ta Falasɗinu, ta ce wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta harba a jiya...
    Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba. Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na...
    Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Gwamnan...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin zai gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis mai zuwa, da misalin karfe 10 na safe domin yin bayani kan shagulgulan al’adu da za a yi na bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa da kuma yakin duniya...
    Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa...
    A karshe a madadina da iyalaina da maaikatana Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Marigayi Alh Aminu Dantata da gwamnatin Kano da al’ummar Kano da Afrika baki ɗaya. Asibitin Kwararru Na Best Choice yana nan a mazauninsa na dindindin dake Plot 782/783 tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir Eli Rayya kuma muna aikinmu ba dare ba...
    Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu. Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota. Hakazalika, ya bayyana cewa...
    Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan...
    Wannan ya tayar da masa hankali, sai ya kira ‘yansanda da ke kusa da wajen. Bayan ‘yansanda sun zo sun tono ƙasar sosai, sai suka gano wata jaririya raye tana kuka, a naɗe cikin wani yadi. Kabiru ya ce gwamnatin ƙaramar hukumar ta ba shi damar kula da jaririyar har sai ‘yansanda sun kammala bincike....
    Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar. Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu...
    Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya.  Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran...
    Sojojin kasar Somaliya sun sanar da kai wani farmaki a kudancin kasar da ya yi sanadiyyar kashe 19 daga cikin ‘yan kungiyar ‘al-shabab’.  Sanarwar wacce tashar talbijin din ‘almayadin’ ta nakalto ta ce, sojojin na Somaliya sun kai harin ne a jiya Litinin da dare a yankin Jubayi, wanda kuma bayan kashe ‘yan kungiyar an...
    Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) ta sanar da cewa; Da akwai ‘yan kasar Sudan miliyan 4 da suke rayuwa a kasashen makwabta da suke fuskantar hatsarin yunwa. Sanarwar hukumar ta kunshi cewa mutanen sun fice daga kasarsu ne tun asali saboda neman abinci da kuma mafaka daga yakin da ya barke a cikin Sudan...
    Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, a shekarun baya-baya nan, an gwada sabbin kayayyayin fasahohin zamani kamar mutum-mutumin inji mai siffar dan Adam, da gilas na zamani, da na’urorin ba da jinya dake hade da kwakwalwa da inji da sauransu, a dandalin bikin baje koli na kayayyakin shige...
    Isra’ila ta bayyana shirin ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen Siriya da Lebanon da suka daɗe ba sa ga maciji da juna a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan na zuwa ne bayan samun lafawar rikici tsakanin Isra’ila da Iran. Kasar Isra’ila ta ce za ta ƙulla hulɗa da ƙasashen da suka daɗe suna zaman doya...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane...
    Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin...
    A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli...
    Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce...
    Cibiyar nazarin harkokin jigilar kayayyaki da sayayya da bayar da hidimomi ta hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, alkaluman yawan kayayyakin da masana’antu ke sayarwa (PMI) na kasar a watan Yuni, sun kai kaso 49.7, karuwar maki kaso 0.2 kan na watan da ya gabata. Duk da cewa akwai sauye-sauye a...
    Iran ta bukaci gudanar da binciken gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai gidan kurkukun Evin A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar, jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed...
    Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga...
    Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da...
    Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon kwana guda a wasu sassan jihar. Wannan na zuwa ne bayan wani hargitsi tsakanin jami’an tsaro da wasu ɓata-gari a yankin Kakuri. Wuraren da dokar ta shafa sun haɗa da Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, da Kakuri GRA. Wata sanarwa da Gwamnatin...
    Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar...
    Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar. Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa ​​da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin...
    Sabon Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Ali Bukar Dalori, ya shiga ofis, inda a halin yanzu yake jagorantar taron Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar.
    Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar...
    Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta...
    JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma...
    Sojojin HKI sun kai falasdinawa akalla 72 ga shahada a safiyar yau Litinin, daga cikinsu har da yara kanana da kuma wadanda suke jiraran a basu taimakon abinci a cibiyoyinsu a cikin Gazzar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau litinin a Gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa a wurare...
    Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.   Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile...
      Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus.   Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga...
    Rahotannin da suke fitowa daga Amurkan sun ce, wani mutum mai dauke da bindiga  yankin Cotinai dake jihar Idaho ya bude wuta akan ma’aikatan kashe gobara a lokacin da suke kan aikinsu na kashe wutar da ta tashi a dajin Kootenai.  Jami’an tafiyar da sha’anin Mulki a yankin ya bayyana cewa; har yanzu ba a...
    ‘Yan sandan Tehran sun sanar da kama wani dan leken asirin kungiyar leken asirin Isra’ila ta “Mosad” a cikin daya daga tasoshin jiragen kasa na birnin Tehran. Dan leken asirin wanda aka watsa furucin da ya yi, ya bayyana cewa aikinsa shi ne kera jiragen sama marasa matuki da kuma ‘yan kananan jirage, a yammacin...
     Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu...
    Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar  musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta da Pakistan din ta dauka akan harin da HKI ta kawo wa Iran, haka nan kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga Iran. Janar Musawi ya  kuma yi ishara da...