Aminiya:
2025-09-24@17:20:02 GMT

An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma

Published: 8th, May 2025 GMT

Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis.

Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya.

Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane

Robert Prevost zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV).

Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fadar Vatican

এছাড়াও পড়ুন:

Talata ce ɗaya ga watan Rabi’ul Thani — Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025.

Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai.

A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance.

Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗan sandan bogi a Kano
  • Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82
  • Talata ce ɗaya ga watan Rabi’ul Thani — Sarkin Musulmi
  • Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya
  • Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani  Sabon Makami Na Sirri
  • APC Da PDP Na Zargin Juna Kan Amfani Da Addini Wajen Neman Nasara A 2027
  • Shettima ya tafi New York don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Hau Turbar Hadin Gwiwa Da Samun Moriyar Juna A Sabon Lokaci