Almundahana: LP Ta Nada Sanata Ireti Kingibe Domin Binciken Tsohon Shugaban Jam’iyyar
Published: 8th, May 2025 GMT
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar.
Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar tare da batanci da haddasa rikici.
Sanata Usman ta Kara da cewa, Abure yana aikata laifufuka wanda suke kalubalantar mutunci Jam’iyar da kuma yin karo da manufofin dimokuradiyya. Don haka, majalisar zartaswa ta Jam’iyar ta dauki matakin kaddamar da bincike kan wannan munanan halayya.
Bugu da Kari Sanata Nenadi Usman tace majalisar zantaswa na Jamiyar Labour bayan dogon nazari akan hukuncin da kotun koli ta Kasa ta yi na ranar 4 ga watan Afrilun 2025, Jam’iyar ta nuna matukar damuwarta akan Yadda Julius Abure yake amfani da sunan shi a matsayin Shugaban Jam’iyar bayan wa’adin jagorancin shi ya cika.
Ta ce, abubuwan da Julius Abure yake yi ya sabawa dokar Kasa kuma ya ci mutuncin Jamiyar. A sabo da haka ne tace kundin tsarin mulkin Jamiyar na shekarar 2019 (Wanda aka yi wa Kwaskwarima) ya Basu damar daukan kwararan matakai da hukunci akan Julius Abure.
Daga bisani, Sanata Nenadi Usman ta nuna rashin amincewarta akan Yadda Julius Abure yake cin mutunci jagoran jam’iyar Labour na Kasa, Peter Obi da Gwamna Alex Otti. Tace Abure da mukarabansa wadanda wa’adinsu ya kare, basu da hurumin magana da yawun Jam’iyar kuma baza su iya dakatar da Gwamnan ba ko wani mamban Jamiyar.
Ta kuma shaidawa ‘Yan Nijeriya cewa, Jam’iyar ta sanar da Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) akan shirye-shiryenta na gudanar da zabuka a matakai daban-daban tare da gudanar da babban taron Jam’iyar na kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara
Matsalar tsaro san rufe kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma ɗauke sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu an mayar da ita zuwa Ilorin, hedikwatar jihar.
Ƙananan hukumomin biyu na Kwara ta Kudu da arewacin jihar na daga cikin wuraren da matsalolin tsaro suka fi taɓarɓarewa duk da ƙoƙarin gwamnati da hukumomin tsaro.
Rufe kasuwannin dabbobiSanarwar farko ta fito daga Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi bakwai na Kwara ta Kudu, inda suka bayar da umarnin rufe duk kasuwannin Kara a yankin.
Shugabannin —Abdulrasheed Yusuf (Ifelodun), Benjamin Jolayemi (Isin), Azeez Yakub (Irepodun), Awelewa Gabriel (Ekiti), James Fadipe (Oke-Ero), Sulyman Olatunji (Offa), da Akanbi Olarewaju (Oyun)— sun ce matakin ya zama dole don hana shigar ’yan ta’adda cikin kasuwanni.
Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyuSun bayyana cewa, ko da yake jami’an tsaro sun yi nasarar ragargazar wasu ƙungiyoyin ta’addanci, har yanzu ana gudanar da sauran rina a kaba, don haka rufe kasuwannin ya zama dole.
Sauran kasuwannin kayan amfanin gona kuma an taƙaita harkokinsu zuwa ƙarfe 6 na yamma.
Shugabannin sun amince cewa matakin na yin illa ga tattalin arziƙi, amma kare rayuka ya fi muhimmanci.
Sai dai wannan umarni ya haifar da suka daga masu ruwa da tsaki. Shugaban Miyetti Allah na jihar, Alhaji Shehu Garba, ya ce matakin bai yi nazari ba kuma bai ba ’yan kasuwar shanu dama su ba da shawara ba. Ya ce hakan zai durƙusar da harkokin kasuwanci, ya kuma ƙara tsananta halin ƙuncin tattalin arziki.
A sakamakon taron da sarakunan gargajiya suka kira a fadar Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya Alebiosu, shugabannin ƙananan hukumomi sun janye umarninsu.
An cimma matsaya cewa a buɗe kasuwannin dabbobi daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranakun kasuwa. Haka kuma an yanke shawarar yin shawarwari da shugabannin kasuwar shanu don tabbatar da tsaro.
Sai dai wani mazaunin Ajase, Idrissu Musa, ya ce wannan matakin zai shafi harkokin kasuwannin shanu matuƙa, domin yawanci kasuwancin yakan fara ne daga ƙarfe 5 na yamma zuwa bayan ƙarfe 10 na dare.
Shi ma wani ɗan kasuwar shanu, Sulymane Mohammed, ya ce rufe kasuwa ba zai shafi ’yan bindiga ba, domin ba kasuwa suke bukata ba, amma dubban mutane da ke dogaro da ita ne za su shiga cikin matsala.
Matsar da sansanin NYSCA gefe guda kuma, hukumomin NYSC tare da amincewar gwamnati sun sanar da cewa, an ɗauke masu yi wa ƙasa hidima na NYSC dafa sansaninsu na dindindin da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu, zuwa Kwalejin Kimiyya (Kwara Poly) da ke Ilorin saboda rashin tsaro.
Mazauna Lafiagi sun bayyana rashin jin daɗi da wannan matakin. Yinusa Michael ya ce, “Yankin ya kan bunƙasa tattalin arziki duk lokacin da ’yan bautar ƙasa suke nan. Suna kuma taimakawa wajen koyarwa a makarantunmu. Maimakon matsar da sansanin, gwamnati ta nemo mafita.”
Zanga-zanga da ƙalubaleRahotanni sun nuna cewa wannan ya biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Offa ƙarƙashin jagorancin Sanata Lola Ashiru, wanda ya jaddada muhimmancin tsara mallakar ƙasa domin rage rikice-rikice.
Bayan kwana kaɗan, matasa da shugabannin al’umma a Isin sun toshe hanyar Ilorin–Omu-Aran–Kabba domin nuna rashin jin daɗi kan yawaitar garkuwa da mutane. Sun yi zanga-zanga daga ƙarfe 8 na safe tare da rufe hanyar, abin da ya dakatar da zirga-zirga.
Wasu mazauna sun tsere daga ƙauyukan da abin ya shafa, inda wasu suka koma Ilorin ko hedikwatar ƙananan hukumomi domin samun kariya.
Matsayin gwamnati da jami’an tsaroKwamishinan ’yan sandan jihar, Adekimi Ojo, ya ce yanzu an daƙile ayyukan’yan bindiga, saɓanin da, inda ya gode wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da ya kawo batun ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu. Wannan ya kawo karin motocin sulke 16 da ƙarin sojoji a jihar.
Gwamna AbdulRazaq ya ce gwamnati na ƙoƙarin kawar da ’yan ta’adda a yankunan da abin ya shafa tare da haɗa kai da masu ruwa da tsaki.
Wani tsohon kakakin ’yan sanda a jihar, Ajayi Okasanmi, ya yi kira ga al’umma da su rungumi haɗin gwiwar tsaro.
Ya ce, “Ko wane makami ne, ba zai yi tasiri ba idan al’umma ba su bayar da haɗin kai ba. Ba za a sami zaman lafiya ba har sai kowa ya ɗauki tsaro a matsayin nauyim da ya rataya a kansa.”