An gabatar da sabbin shaidu kan Nnamdi Kanu
Published: 7th, May 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta saurari sabuwar shaida kan tuhumar da ake yi wa shugaban ƙungiyar ‘yan a waren Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.
A zaman kotun na ranar Laraba, an tuhumi Kanun da aikata laifuka bakwai, kuma Mai Shari’a James Omotosho ya bayar da damar gabatar da na’urar adana bayanai ta ‘flash’ mai ɗauke da bidiyoyi da wasiƙa mai kwanan wata 17 ga watan Yunin 2021 a matsayin sabbin shaidu.
A ɗaya daga cikin bidiyon da aka kunna a kotun, an ga Kanun na bai wa mabiyansa umarnin afka wa jami’an tsaro, su kuma ƙone ofisoshin ‘yan sanda.
Lauyan masu ƙara, Adegboyega Awomolo (SAN), ne ya gabatar da shaidun ta hannun sashin rundunar tsaron sirri (DSS).
A cikin bidiyon dai ya sanar da kafa ƙungiyar tsaron gabashin ƙasar (ESN), tare da neman magoya bayansa su kare garuruwansu daga abin da ya kira mamayar al’ummar Fulani.
A hannu guda kuma, wasiƙar da ta fito daga hannun Antoni Janar na ƙasa ta bai wa DSS umarnin binciken Kanu kan aikata laifukan haɗin baki, kisa, ƙone-ƙone, da kisan jami’an tsaro.
Wasiƙar ta kuma zayyano wata wallafar bidiyo da ya yi a shafinsa na Facebook lokacin zanga-zangar EndSARS a Legas, in da ya bai wa mabiyansa umarnin shirya jerin gwanon hare-hare.
A cikin bidiyon an kuma jiyo muryar da ake zargin ta Kanu ce yana ba da umarnin kashe duk wani ɗan sanda da aka yi ido huɗu da shi, a kuma ƙone ofisoshinsu.
“Ku fara kashe sojoji yanzu, ku rutsa su, ku haƙa ramuka a titi motocinsu su faɗa su mutu,” in ji muryar.
Ya kuma gargaɗi jagororin yankin tare da ba su umarnin korar Fulani makiyaya inda ya ce za su ɗauki fansar duk ɗan Biafran da ya rasa ransa.”
A wani bidiyon kuma an ga Kanu na bayyana hana zirga-zirga a yankin gabashin ƙasar baki ɗaya, domin tunawa da ‘yan Biafra da suka mutu, tare da bayyana hukuncin kisa ga duk wanda ya saɓawa umarnin.
Daga nan ne Alƙalin kotun ya sanya 8 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron shari’ar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan awaren Biyafara yan IPOB
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifinsa Har Lahira A Jigawa
Ya ce an kama matashin tare da addar da ake zargin ya yi amfani da ita, kuma yanzu ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ya aikata hakan.
“Matashin yana hannunmu, kuma muna ci gaba da gudanar da bincike,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp