2025-09-18@17:35:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6309

«Karuwa»:

    Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta...
    Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun shirya horar da aikin ceto yayin ambaliya,  a Ƙaramar Hukumar Auyo. Taron horaswar ya haɗa masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban,...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu...
    Hukumar bunkasa ilimin gaba da sakandare ta jihar Jigawa ta shirya taron tattaunawa ga jami’an gudanar da shirin koyawa dalibai musamman wadanda suke da nakasu a jarrabawar NECO ko WAEC wato Remedial program don su sami nasarar cin jarrabawar da za ta basu damar ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandare. Da yake...
      Shugabar ma’aikata ta jihar Kaduna, Madam Jummai Bako ta yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da fasahar Artificial Intelligence, A.I yadda ya kamata domin bunkasa ayyukan yi da gudanar da ayyukan.   Misis Bako ta yi wannan kiran ne a wani taron bita na yini guda da ofishin shugaban ma’aikata tare...
    Sabuwar mutum-mutumi ta fasahar AI da aka kirkira kuma aka nada mukamin minista a ƙasar Albania ta yi jawabi a karon farko a gaban majalisar dokokin kasar. A ranar Alhamis ce dai ministan ya bayyana gaban majalisar, inda ya kare rawar da zai taka a gwamnati, yana mai cewa, “Ban zo don na maye gurbin...
    Tun a ranar 7 ga watan Satumba, 2025, wani mutum mai suna Hussaini Manager ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Kafin Hausa cewa an sace masa mota ƙirar Golf mai launin shuɗi mai lambar MGA 108 JG a Agura Motor Park, Kafin Hausa. Bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen na yin sojan gona...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da...
    Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin gyara da sake duba hanyoyin kiwo 37 tare da filayen kiwo takwas a faɗin jihar. Wannan aiki na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage rikici da ake samu tsakanin manoma da makiyaya. HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Microsoft ya ƙwace shafukan...
    A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa...
    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa, SEMA, tare da hadin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, sun shirya gwajin yadda za a gidanar ayyukan ceton ambaliyar ruwa a karamar hukumar Auyo.   Gwajin wanda ya tattaro masu ruwa da tsaki daga...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai...
    Gwamnatin jihar Kano ta aika dalibai 588 zuwa jihohin Arewa 13 a karkashin shirin musayar dalibai na shekarar 2025/2026.   An kai daliban zuwa jihohinsu da suka hada da Adamawa, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kebbi, Taraba, da Nasarawa. Bugu da kari, an kai dalibai daga Yobe, Kaduna, Sokoto, Borno, da Kwara lafiya zuwa inda suke,...
    Wani makami mai linzami na Yemen ya tilastawa jirgin saman fira ministan gwamnatin Isra’ila saukar gaggawa Kafofin yada labaran yahudawan swahayoniyya sun watsa rahoton cewa, an tilastawa jirgin saman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu yin saukar gaggawa a lokacin da ake atisayen soja bayan harba makami mai linzami daga kasar Yemen zuwa yankunan...
    A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa...
    Ya jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa. Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman...
    Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu. Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu...
    Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar.   Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa. Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar...
    Hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO ta fitar da jarabawar SSCE dalibai dubu 818, 492 suka sami kiridit 5 zuwa sama da suka hada darasin Ingilishi da Lissafi.   Adadin bisa ga sakamakon ya nuna dalibai kashi sittin da biyu sun smai nasara.   Magatakardar NECO kuma Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne...
    Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Gumi kan mumunan al’amuran da suka salwantar da rayukan mazauna kauyen Fas su 19 a makonnin da suka gabata.   Malam Mumini ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da suka kai ziyarar jaje ga al’umma, inda...
    A lokacin gudanar da bincike, an samu layin waya guda 21 da takardun rijistar layi guda 29 a wajen Suleiman, wanda ya ce yana harkar rijistar layin ne. Ya amsa cewa shi ne ya bai wa waɗanda “aka sace” waya da lambar da aka yi amfani da ita wajen neman kuɗin fansa. Binciken ya nuna...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024. “Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce...
    Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wata ganawa da takwaransa na kasar Masar ya bayyana cewa: Iran da Masar sun mallaki wasu al’adu guda biyu masu cike da tarihi masu alfahari da fa’ida, kuma fadada hadin gwiwar da ke tsakaninsu zai kara taimakawa wajen tabbatar da moriyar al’ummomin kasashen biyu da ma sauran al’ummomin yankin....
    Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta ce ma’aikatanta hudu sun mutu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad da ke Legas, a ranar Talata. Aminiya ta rawaito yadda gobara ta mamaye ginin da ke dauke da banki, hukumomi da wasu kamfanoni. Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.   Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar...
    Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF). A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar. An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na...
      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za...
    Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi...
    Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na  jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025. Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma...
    Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.   A nasa bangaren, mahaifin budurwar,...
    Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing. Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban...
    Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin...
     Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro. Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya...
    Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe. Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta...
     Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya...
    Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250  ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi. Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince...
    Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin...
    Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba...
    An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa. Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce...
    Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara...
    Kungyar Hamas ta bayyana cewa: Gmanatin mamayar Isra’ila ta ƙirƙiri ƙarya don kare kisan gillar da ta yi a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tabbatar da cewa: Zargin da kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila ya gabatar dangane da yin amfani da hasumiyai a birnin Gaza domin aikin soji ba komai ba ne illa...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban...
    Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu. A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000. Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya...
    Gwamnatin  kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi...