An Zabi Birnin Esfahan Na Kasar Iran A Matrsayin Cibiyar Yawon Bude Ido A Asia Na Shekara Ta 2025
Published: 12th, May 2025 GMT
Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa.
Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin
Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare 15 na kayakin da tarihin da take kula da su don muhimmancinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Gana Da Tokwaransa Na Kasar Saudiya A Jiya Asabar
Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza.
Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan.
Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi.
A wani bangare Aragchi ya fadawa tokwaransa inda aka kwana dangane da tattaunawar da kasar take yi da kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya.