2025-08-09@17:53:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4529

«kasar Sin ya»:

    Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma.   Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun yan siyasa na yankin da suka rasu.   Yayi bayanin cewar, za’a gina makarantun tsangayar ne a garuruwan Danzomo da Shabaru da kuma Rukutu wadanda za’a sanyawa sunan wadanda suka rasu da suka hada da marigayi Sanata Dalha Ahmad Dan Zomo da marigayi Musa Waziri Kamus da kuma marigayi Ali Ado.   Haka kuma majalisar ta amince da gyaran masallatan Juma’a na Hannun Giwa da...
    Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar duniyar wata da aka raba ma wasu hukumomin bincike 7 na kasashe 6. Kana bisa gudanar da bincike kan kasar da na’urorin binciken duniyar wata na kasar Sin, wato Chang’e-5, da Chang’e-6, suka dawo da ita, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na sauran kasashe, sun gabatar da sakamakon bincike fiye da 150. An ce, tsarin da ake bi wajen neman samun...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da suka rasu. Wannan biyan zai shafi tsoffin ma’aikatan jihar, ma’aikatan wucin-gadi, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da malaman firamare. Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Ana sa ran biyan kuɗin zai fara daga kan watan Disamba 2024 zuwa Maris ɗin 2025. Gwamna Idri, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar ma’aikata da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima. Ya ce biyan haƙƙoƙin ma’aikata ba wasa ba ne, kuma gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da suka rasu. Wannan biyan zai shafi tsoffin ma’aikatan jihar, ma’aikatan wucin-gadi, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da malaman firamare. Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Ana sa ran biyan kuɗin zai fara daga kan watan Disamba 2024 zuwa Maris ɗin 2025. Gwamna Idri, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar ma’aikata da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima. Ya ce biyan haƙƙoƙin ma’aikata ba wasa ba ne, kuma gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen...
    Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara. Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024. Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno  Ana tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba. A...
    Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun.   ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai. “Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba,...
    Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo. Lashen ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da sabani da suka samu da sojan. A yayin da yake kokarin warware rikicin, sai sojan mai suna Dauda Dedan, ya soka masa wuƙa. Ya ce, “Mun samu rahoton lamarin daga hedikwatar Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da tabbacin cewa za a kamo sojan da ya tsere domin...
    Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu ƙasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban ƙasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alaƙar tarihi tsakanin ƙasar Laberiya da Amurka. Bugu da ƙari, Trump ya katse maganar shugaban Ƙasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri. A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar, ba domin neman ƙarfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka ɗin damar samun ma’adanan da take...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon. A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa. Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, ta wayar tarho a yau Jumma’a 8 ga wata. A tattaunawarsu, Putin ya bayyana ra’ayin kasar Rasha dangane da rikicin Ukraine a halin yanzu, da yadda Rasha ta tuntubi Amurka kwanan nan, inda ya ce, Rasha ta yaba sosai da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin shawo kan rikici ta hanyar siyasa. A nasa bangaren kuma, Xi ya jaddada matsayin kasar Sin, tare da bayyana cewa babu wata dabara mai sauki da ke iya magance matsaloli masu sarkakiya. Ba tare da la’akari da duk wani sauyi da za a fuskanta ba, kasar Sin za ta tsaya ga neman sulhu da gudanar da shawarwari....
    Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya.   Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...
    Shugaban tsangayar Kula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu A Kwalejin Likitanci Ta Ƙasa (NPMCN), Farfesa Ayodeji Oluwole, ya bayyana hanyoyin da shirin ke bi wajen aiwatar da aikin: ” Wannan horo ya samar wa likitocinmu da fasaha ta zamani, kuma a cikin shekaru biyar, muna sa ran raguwar mutuwar mata masu juna biyu. “Babban abin da ake buƙata shi ne a rage yawan mace-macen mata masu ciki a Nijeriya da Afirka, mun horar da likitoci kusan 220 da masu ba da shawara 140 a duk yankuna shida na siyasa. “A yanzu haka, likitocin suna samun horo a babban asibitin ƙasa dake Abuja; hakan na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin gwamnatin tarayya na kula da lafiyar mata masu juna...
    Wannan irin jita-jitar tana kokain zana shi da kwatankwacin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani rikici da ya ɓarke ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai suna Irmiya Yohanna, mai shekara 40, tare da hallaka shanu da tumaki 39, a ƙauyen Kaduna da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, a Jihar Bauchi. Haka kuma  ’yan sanda sun ceto shanu 249 da aka yi ƙoƙarin kashewa. Obi ya ziyarci Bauchi, ya ba da tallafin N15m don inganta ilimi PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa, a ranar 7 ga watan Agusta 2025, Irmiya ya tafi gonarsa amma bai dawo gida ba. Bayan yin bincike, aka gano gawarsa a kwance a gonarsa. Bayan samun rahoto daga Sarkin ƙauyen, Emmanuel Bulus, ’yan sanda ƙarƙashin...
    Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a fannonin hidimar gida da masana’antu da kayan ajiya. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin jakadancin kasar a Philippines, sun gabatar da korafi da babbar murya dangane da kalaman da aka jiyo jagoran Philippines na yi game da batun yankin Taiwan na Sin. Kakakin wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce, yayin ziyarar da ya gudanar a kasar India, shugaban na Philippine ya shaidawa ‘yan jarida cewa, idan har yaki ya barke tsakanin Sin da Amurka, tabbas kasarsa za ta shiga, saboda kasancewarta a kewayen yankin, da ma ‘yan Philippines da dama dake zaune a Taiwan, wadanda ya zama wajibi a aiwatar da matakan mayar da su gida. Jami’in Sin ya kara da cewa kasar Sin daya ce tak...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi. Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe. Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe Bayan saukarsa ya wuce Makarantar Kiwon Lafiya da Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Malikiya da ke Bauchi. A yayin ziyarar, Obi ya gana da ɗaliban makarantar, inda ya roƙe su da su dage wajen karatu domin aikin jinya da kula da lafiya yana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa. Ya ce: “A yau, nasarar...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33. Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da...
    A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin ya sauya sheƙa zuwa ADC, ya koka kan yadda gwamnatin Kaduna ba ta kula da haƙƙoƙin ma’aikatan jihar da rashin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu da ƙalubalen rashin tsaro wanda hakan ke hana manoma zuwa gonakansu. Ya soki tsarin rabar da takin zamani na gwamnatin jihar ke gudanarwa ba tare da ta magance ƙalubalen rashin tsaro ba daga tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda. Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama. ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara guduws bayan yunƙurinsu na kai hari sansanin sojoji ya ci tura. Da suka hangi jiragen yaƙi na sojojin sama, sai suka fara tserewa daga maɓoyarsu, amma an kashe da yawa daga cikinsu ta hanyar ɓarin wuta. Wani mazaunin Rann ya ce da farko sun...
    A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu. Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu An kama su lokacin da suke ƙoƙarin yaudarar wani mutum a wajen ATM na bankin Fidelity da ke Damaturu. Ana zargin matasan da amfani da wasu dabara wajen damfarar mutane ta hanyar nuna kamar suna taimaka musu, amma daga baya sai su sauya musu katin ATM. A wani...
    Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar. A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya ce...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki daya sannan a samar wa fararen hula agaji a wajen yankunan da ake gwabza yaki.” Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 Kazalika, wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk hukuncin da majalisar tsaron kasar ta yanke zai bukaci...
    Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya, don sayarwa”, in ji Ibrahim. Kazalika, Ibrahim wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ya jaddada cewa; idan aka samu goyon bayan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma goyon bayan sauran hukumomin, hakan zai bayar da damar gyara Gandun Dazukan da ake da su, musamman wajen kare su daga kwararowar hamada. Shugaban ya ƙara da cewa, akasarin noman...
    Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka wa mazauna birnin wahalar da suke sha a harkar sufuri. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano Ya ce, “Wannan aikin na gina layin dogo na zamani ya kai Dalar Amurka biliyan daya, kwatankwacin Naira tiriliyan daya da rabi. “Ga wadanda suke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, musamman kasashen Turai da nahiyar Asiya,...
    Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da Agusta 2024 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa. Farkon kashe kuɗaɗen a ranar 14 ga Yulin 2023, lokacin da aka biya naira miliyan 846.03 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na wucin gadi. Kwanaki biyu daga bisani, an sake kashe naira miliyan 674.82. A wannan watan kaɗai, jirgin ya laƙume sama da naira biliyan 1.5. A watan Agusta, kashe kuɗaɗen sun ƙaru. An kashe...
    Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci. Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa, yadda aka bar iyakokin ƙasar sakakai ne, ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasa, inda wasu’yan ta’adda daga wajen ƙasar, ke yin amfani da damar, wajen shigowa tare da kuma shigo da muggan makamai da yadda masu ra’ayin riƙau na addini, daga ƙasashe kamar su, Mali da Jamhuriyar Nijar da Chadi, ke shigowa ƙasar, su kuma ci Karensu ba babbaka. Misali, ‘yan ta’addar ƙungiyar Lakurawa,...
    Sakamakon kama Mu’azu Ɓarga, yanzu haka abokan ta’asar tasa sai tsallakewa suke domin tserewa kamun rundunar ‘yan sanda, duk da gudun da suke rundunar na ci gaba da farautarsu har kuma an samu nasarar ƙara damƙe mutane biyu cikin sama da mutane arba’in da Ɓarga ya bayyana wa ‘yan sanda. Wannan tasa a ranar Juma’ar da ta gabata Al’ummar Sheka ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Muryar Jama’ar Sheka ta ziyarci Shelkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai domin jinjina wa ƙoƙarinsu. Cikin shahararrun mafaɗatan da suka gamu da ajalinsu alokacin arangama daban-daban akwai matashin da ya addabi al’ummar Unguwar Ɗorayi mai Suna Barakita, sai kuma wani mai suna Khalufa ɗan unguwar Ƙofar Mazugal Da kuma wani guda da ke tafka irin wannan...
    Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a  kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya  a jiya Alhamis.AMREF Flaying Doctor,  jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi jim kadan bayan tashinsa. An ce matukin bai yi korafin ko akwai Malala a cikin jirgin ba, kuma wani wani gargadi sai kawai anji ya fadi. A halin yanzu dai ba’a san sababin faduwarsa ba, kuma jami’an tsaro basu bada wani bayani har yanzun yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, ku kuma sunaye da kamanin ko matsayin mutanen da suke cikin jirgin ba. Har’ila...
    Daruruwan mazauna kauyen Jimrawa da ke karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar kan matsalar tsaron da ta addabe su. Hakan na zuwa ne mako biyu bayan mazauna Gusau din su ma sun yi irin wannan zanga-zangar kan cewa ’yan bindiga sun kashe sama da mutum 100 a kauyukan jihar. Kauyukan da aka kashe mutanen sun hada da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Lilo da kuma Bangi. NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe? Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano Kauran Namoda da sauran kananan hukumomin jihar dai sun jima suna fama da hare-haren ’yan ta’adda, lamarin da ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Sun kara da cewa,”A cikin wannan lokaci, mataimakin kyaftin na yanzu, Ronald Araujo ne zai karbi aikin kyaftin din, Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasanni sama da 400 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2014, ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar zakarun Turai da kuma gasar La Liga shida a kungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12.   Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce karkashin wannan tallafi, iyalai da yaransu za su ci gajiyarsa za su samu ragin kashe kudaden makaranta da yawansu ya kai kusan yuan biliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.8. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar. Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore. Mahaifin Ɗan Bello ya rasu Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano “Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ya saba wa ka’ida. Dole ne a yi tur da lamarin,” in ji Atiku. Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin shugabanci nagari da ake yi a Nijeriya. Wasu rahotanni...
    Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara. Daga cikin adadin, darajar mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 15.31, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.1, adadin da ya karu da kashi 7.3 cikin 100, yayin da mizanin shigo da kayayyaki shi ma ya kai yuan tiriliyan 10.39, kwatankwacin dalar Amurka triliya 1.44, adadin da ya ragu da kashi 1.6 cikin 100.   A watan Yuli, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta...
    Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 “Innalillahi wa inna IlaiHi rajiun. Allah Ya yi wa Mahaifin Dokta Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah Ya gafarta masa. Ameen,” a cewar saƙon da Abba Hikima ya wallafa. Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bellon ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa marigayi ya...
    Bugu da kari, a baya bayan nan ma jaridar Financial Times, ta bayyana yadda a yanzu haka adadin hajojin da ake shigarwa Amurka daga sassan duniya daban daban suka ragu zuwa kaso 13 bisa dari, sabanin kaso kusan 20 bisa dari da kasar ke shigowa da su a tsawon shekaru 20 da suka gabata. Kamar dai yadda kimar Amurka ke raguwa sakamakon matsin lamba da take yiwa sauran sassan duniya abokan cinikayyarta, haka ma wadannan manufofi na kakaba haraji ke fuskantar turjiya, da kyama har daga abokan kasar makusanta. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta bayyana Sadiq a matsayin jarumi, ƙwararre, kuma mai kishin kasa a fannin kafafen sada zumunta. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato Gwamna Abba ya ce mutuwar Sadiq Gentle ta girgiza shi sosai, inda ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai kamun kai, haƙuri, da sadaukarwa ga ci gaban Jihar Kano....
    Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti “Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula...
    Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da Israila ta dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da Gaza nan take. Sakamakon ya kuma nuna cewa, kaso 80.8 na wadanda suka amsa na ganin cewa mafita ga rikicin Palasdinu ya dogara ne da kafuwar kasashe biyu, inda suka yi kira da a dawo da halaltattun hakkokin kasar Palasdinu. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da...
    Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata jira izinin kowa ba Babban hafsan hafsan sojin kasar Iran ya gargadi makiya, yana mai cewa: Suna yi wa shahidai alkawari cewa: Za su ci gaba da bin tafarkinsu, kuma duk wani sabon harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci azamar mayar da martani daban da na baya. Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada matsayin wadanda suka yi shahada a safiyar yau Alhamis a yayin bikin tunawa da ranar shahidan Iraniyawa a hare-haren wuce gona da iri, yana mai daukar su a matsayin ginshikan tabbatar da...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya da Amurka, inda suka jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaro da yankin kasar Iran za ta fuskanci kakkausar martani da ya zarce tunanin makiya, kuma zasu kasance mafi tsanani fiye da abin da ya faru gamakiya da amsu kiran yaki a martanin alkawarin gaskiya na uku. A cikin wata sanarwa da Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka fitar a cikan kwanaki...
    Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, inda suka kai harin kan gidajen fararen hula da kuma tantunan ‘yan gudun hijira. Jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani tanti na ‘yan gudun hijira a yankin Tal, kudu maso yammacin birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla biyar tare da raunata wasu. A yammacin sansanin ‘yan...
    Waɗannan bayanai duk suna ƙunshe ne a cikin jawaban da aka gudanar a gangamin wayar da kai game da wannan cuta, wanda ya gudana a Kaduna.   Lokacin da ta ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wannan gangami, Dr. Maimuna Lawal Garba, ƙwararriyar Likita a fannin hanci, kunni da maƙogwaro, ta fara bayanin ta ne da bayyana abubuwan da suke haddasa wannan cuta ta Kansar Maƙogwaro.   Ta ce, “Muna bai wa mutane shawara su kiyayi shan tabar sigari, barasa (giya). Haka kuma akwai yanayin aikin mutane, misali, masu aiki a wurin yankan katako, wannan ƙurar ta katako tana daga cikin abubuwan da za su iya sabbaba ma mutum kamuwa da wannan cuta.   “Haka kuma akwai (radiation),...
    ’Yan bindiga ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen Bimasa a Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato sun kashe mutum huɗu sun jikkata wasu da dama a daren ranar Laraba. Ɗaya daga cikin jagorori a ƙauyen ya yi wa Aminiya ƙarin bayani ya ce, a daren ranar Laraba da ƙarfe 12:40 na tsakar dare ɓarayi suka shigo ƙauyen akan babura suna da yawa sun fi mutum 10 a nan take suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi kai tsaye suka harbe mutum biyar, huɗu suka rasu an kai ɗaya asibiti. ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara “A haka suka rika harbi ta ko’ina, sun...
    “An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi   Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna kan hanyar zuwa kauyen Yankuzo, inda rahotanni suka ce an kai ‘yan ta’addan da suka jikkata domin yi musu magani.   A cewar majiyoyi da bayanan sirri daga Kauyen, an kashe ‘yan ta’adda fiye da 30 a yayin samamen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    A yau Alhamis aka yi bikin bude gasar wasanni ta duniya ta 2025 a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa  Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki. Onanuga ya bayyana cewa  waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba...
    Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin. An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin. An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno A cewar Eribo, an samu nasarar ne bayan samun wani sahihin daga wani da ya ba da rahoto ya tuntuɓi wani babban jami’in ‘yan sanda, inda ya nuna shakku kan wata mata da ta yi imanin cewa tana da alaƙa da sace jaririyar da ta ji a cikin labarai....
    Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara. An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar. ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore A yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta. Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya iyalai 14 da aikin sake gina Babban Masallacin Gumel ya shafa kudaden diyya da suka kai Naira miliyan 277 da dubu 44. An gudanar da bikin bayar da takardun cekin kudin ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammad Sani, tare da halartar masu rike da sarautu, da shugabannin al’umma da manyan jami’an gwamnati. Da yake jawabi yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, wanda Babban Sakataren Harkokin Gudanarwa da Kudi na Ofishinsa, Alhaji Abdullahi Sa’idu, ya wakilta, ya shawarci iyalan da su yi amfani da kudaden ta hanya mai amfani wajen gina sabbin gidajensu tare da rungumar sauyin wurin zama cikin hakuri da tawakkali. Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa...
    Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su. An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore Majiyoyin da ke kauyen na sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa wadanda suka mutun sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu. Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan...
    Sayar da Nunez zai ba Liverpool damar siyan Alexander Isak daga Newcastle. Sai dai Newcastle ta ƙi karɓar tayin fam miliyan 110 daga Liverpool, saboda tana so ta siyar da Isak ne abkan fam miliyan 150. Liverpool ta riga ta siyo Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kan fam miliyan 116 da kuma Hugo Ekitike daga Frankfurt a kan fam miliyan 79. Hakan ya sa Liverpool ta kashe kusan fam miliyan 250 a wannan kakar kasuwanni. Ta kuma siyar da Luis Diaz ga Bayern Munich ankan fam miliyan 65.5 da Tyler Morton ga Lyon a kan fam miliyan 15. Ɗan wasan Ingila Harvey Elliott ma na iya barin ƙungiyar a bana. A watan Janairu da ya wuce, Liverpool ta ƙi...
    Jami’an tsaro a kasar Lebanon sun bayyana damuwarsu da yiyuwar sojojin HKI su farwa kasar da yaki da nufin kwace kasar da kuma sunan yaki da kungiyar Hizbullah. Jaridar da nation ta kasar amurka ta bayyana cewa, HKI ta jibje sojojin masu yawa da kuma tankunan yaki a kusa da Jabal sheikh da suka mamaye, don mai yuwa ta fadawa kasar Lebanon ta kuma mamaye gabaci da areawacin kasar kafi ta fuskan kungiyar Hiszullah wacce tafi bada karfinta a kudancin kasar. Wasu majiyoyin tsaro guda 2  a kasar ta Lebanon wadanda basa son a bayyana sunayen na fadar cewa sojojin HKI a kan iyakar kasar Lebanon da Siriya sun bayyana cewa a hankali a hankali sojojin HKI suna matsowa kusa...
    Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Kasa sun kutsa inda ake tsare dan gwagwarmaya Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da karfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba.   Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da karfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a kokarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba..   A jiya Laraba ne dai Sowore ya amsa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa ya yi masa don ya amsa...
    Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore   Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Qasa sun kutsa inda  Hukumar ‘Yan sanda ta Qasa ke tsare xan gwagwarmayar neman haqqin bil’Adama Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da qarfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da qarfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a qoqarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.. jiya Laraba ne dai Sowore ya masa...
    Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar. Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu. ‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi ba tukuna. Bayan faɗan ta yi tsanani, an tura ƙarin sojoji zuwa yankin domin ci gaba da matsa wa ‘an bindigar da suka tsere lamba tare da hana su sake kai hari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya. Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Daga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma...
    Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne. “Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,”...
    Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne. “Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,”...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta. Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta ke da su domin ɗaukar nauyin yaƙin da ta ke yi da Ukraine. Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma Trump ya bayyana cewa zai sanya sabbin takunkuman da za su hana Rasha cin gajiyar kasuwanci da wasu ƙasashe. Daga cikin matakan, akwai sanya haraji har kashi...
    “Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.” Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu. “Yawancin shugabanninmu sun shiga ruɗani, babu wanda ya tsira,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fiye da mashahuran mutane 160 ne da kuma ‘yan jarida suka shiga wani kamfen na neman gwamnatin Jamus da ta dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila, inda ya zuwa wannan Laraba  adadin wadanda suka sa hannu kan rakardar ya kai mutane 367. Daga cikin wadanda suka rattaba hannu, wanda kungiyar fafutuka Avaaz ta sanar, sun hada da fitattun jarumai irin su mawaka Nina Chuba da Clueso, da darektan cibiyar German – Turkey Fatih Akin, da fitaccen mai shirya fina-finai a Jamus  wanda ya lashe lambar yabo ta Golden Globe, Ari Folman, da kuma fitacciyar jarumar sinima ta Jamus Sandra Hüller. Kungiyar ta kuma soki lamirin firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu kan aniyar mamaye yankin zirin Gaza gaba daya, tare da...
    Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a daren jiya ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu masu tarin yawa, yayin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kaddadamar da munanan hare-hare a kan a yankuna da dama na Zirin da aka yi wa kawanya, da suka hada da gidajen farar hula da tantunan da aka kafa a mafaka  ga iyalan da suka rasa matsugunansu. A cewar wakilin Al Mayadeen, akalla Falasdinawa biyar ne suka yi shahada, wasu kuma suka jikkata bayan da jiragen saman Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a wani tanti da ke a yankin Tal, kudu maso yammacin Deir al-Balah a tsakiyar Gaza. A sansanin Nuseirat na yammacin Gaza,...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba. Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba. Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki An fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya. Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan. A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba. Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba. Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki An fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya. Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan. A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya...
    Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin. Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da duk wata ziyara da wani dan siyasar Birtaniya zai kai Taiwan bisa ko wane dalili. Kakakin ya kuma nanata cewa, Taiwan bangaren kasar Sin ne da ba zai iya ballewa ba, kana batutuwan da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan Sin da ba sa bukatar katsalandan daga waje. Bugu da kari, ofishin jakadancin ya ce babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar Zirin...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar. Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina “Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar. Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan...
    Ya kuma bayyana cewa, tuni aka mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Birnin Hiroshima na kasar Japan ya yi juyayin cika shekaru 80 da harin makamin nukiliyar Amurka Birnin na Hiroshima ya gudanar da bikin juyayin cika shekaru 80 da kai harin makamin nukiliyar Amurka ta yi a yau Laraba tare da halartar kasashe fiye da 100, inda mahalarta taron suka yi shiru na dan wani lokaci. Kafin a fara yin shiru, a daidai lokacin da bam din nukiliyar Amurka ya fado a kudancin kasar Japan, da dama daga cikin mahalarta taron sun ajiye furanni a wurin taron tunawa da wadanda harin ya rutsa da su. A wajen bikin juyayin, Hiroshima ta sake yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su dauki matakin kawar da makaman kare dangi. Wakilai daga kasashe da...
    “Bari in yi bayani a fili: ba za mu yarda da duk wata dabi’a wacce za ta ruguza dabi’un da muke tsaye a kai ba. Dole ne kowane jami’in gwamnati ya kasance mai lura da al’amuransa, ba wai kawai ofishin ku kuke wakilta ba, har da mutuncin gwamnati baki daya.” In ji Gwamna Abba Kabir   Gwamna Yusuf, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya jaddada cewa, duk wanda aka samu yana taimakawa ko aikata laifuka to zai fuskanci cikakken fushin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Da safiyar Larabar nan ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattaunawa game da batun rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda a jawabinsa game da aniyar Isra’ila ta tsananta hare-haren soji, da mamaye daukacin zirin Gaza, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwa kan hakan, yana mai kira ga Isra’ila da ta kauracewa wannan mataki mai hadari, yana mai fatan daukacin sassan da lamarin ya shafa za su gaggauta kaiwa ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai tsorewa. Geng Shuang, ya kuma jaddada muhimmancin aiwatar da sahihin mataki na dakatar da bude wuta yadda ya kamata, ta yadda hakan zai kubutar da rayukan al’umma, tare da bayar da damar sakin wadanda ake tsare...
    Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.   Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudi har yuan biliyan 1.015, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 142 ga lardunan kasar daban daban, domin gudanar da ayyukan jin kai, sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassan kasar. Rahotanni na cewa ma’aikatar kudin kasar, da ma’aikatar gona da raya karkara, da ma’aikatar albarkatun ruwa ne suka samar da kudaden, wadanda za a yi amfani da su a ayyuka daban daban na tallafawa yankunan da ambaliyar ta shafa, ciki har da birnin Beijing, da lardin Hebei, da Mongolia ta gida da Guangdong. Kana cikin kudin za a samar da tallafin sake shukar da ruwa ya lalata, da ma kayayyakin aikin gona da ambaliyar ta shafa. Kazalika, za a yi amfani da bangaren...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus. Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu. Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Wannan lamari ya tayar da ƙura, wanda hakan ya sa Gwamna Abba, ya ɗauki mataki. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan lamarin. Hakan ta sa ya jaddada buƙatar dukkanin mambobin majalisar da sauran manyan...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare  da zai taimaka wa rayuwarsu. A wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi ƙarancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma’aikata mafi rauni a tsarin CPS. Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho...
    Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin. Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Motar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne. An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati...
    A jawabin da Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya yi ta bakin mataimakinsa, Farfesa Sanusi Rafindadi, ya yaba da yadda taron ke taimakawa wajen wayar da kai game da wannan cuta mai hatsari. Ya kuma gode wa Hajiya Fatima bisa amsa gayyatar jagorantar taron. Shugabar Sashen Kula da Mata, Farfesa Rahanatu Lawal, ta jaddada buƙatar haɗin kan kowa da kowa wajen yaƙi da cutar. Ta ce mata ba za su iya wannan yaƙi su kaɗai ba, dole ne maza su ba su goyon baya. Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi akwai Dakta Aminat Jimoh daga Asibitin Koyarwa na ABU. Ta buƙaci mata da su riƙa duba kansu akai-akai, musamman idan suna da tarihin ciwon a cikin danginsu. Ta...
    Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci da aka yi a birnin Landan na Burtaniya. A farkon makon nan ne dai Nafisa Abdullahi Aminu da Rukayya Muhammad Fema da kuma Hadiza Kashim Kalli suka zama zakaru a gasar TeenEagle ta 2025 da aka yi a birnin na Landan. Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 A cikin wata sanarwa daga bakin kakakinsa, Bayo Onanuga, ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce nasarar ’yan matan abin alfahari ce ga Najeriya. Tinubu ya kuma yaba wa makarantun da daliban suke karatu, inda ya ce nasarar daliban wata...
    Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su. Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas Mutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha. Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga...
    Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar. Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya...
    Ya ce malamin bai fi Sheikh Ahmad Gumi ba, wanda ya gaza yin zaman sulhu da Turji. Guyawa, wanda ya daɗe yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanai, ya ce ba a taɓa yin sulhu da mutum yayin da yake ci wa jama’a zarafi ba. Ya ce: “Za a iya cewa mutum ya yi sulhu alhali yana ci gaba da karɓar haraji daga hannun manoma da tilasta musu noma? Ko kuma yana kashe mutane da ƙond motar jami’an tsaro?” Guyawa ya ƙara da cewa Turji da sauran ‘yan ta’adda kamar Kachalla Choma da Kachalla Haru suna da makamai da kwamandoji da yawa, kuma babu wani abu da ke nuna sun ajiye makamansu. Ya ce malamin da ya faɗi cewa Turji...
    Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cikakken goyon bayan rundunar ‘yan sanda ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano wajen tabbatar da kiyaye dabi’u da yakar munanan halaye a cikin al’umma. CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar wayar da kai da Sakatare na Hukumar, Abba El-Mustapha, ya kai tare da tawagarsa zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano. A yayin ganawar, CP Bakori ya yaba da jagorancin hukumar, musamman kokarin da El-Mustapha ke yi wajen tsara harkokin masana’antar Kannywood da kuma kare tarbiyya ta hanyar sa ido mai tsauri. Ya tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin rundunar da hukumar, musamman wajen dakile cin zarafi da amfani da kafafen sada zumunta...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamad Reza Aref ya bayyana cewa kasar Iran tana goyon bayan dukkan shirin zaman lafiya a yankin musamman tsakanin kasashen Armenia da kuma Azarzaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aref yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Armenia Vahagn Khashaturyan a kasar Tukeministan ake ake gudanar da taron kasashen wadanda basa kan bakin ruwa a duniya a ranar Litinin. Majalisar dinkin duniya ce ta take shrya wannan taron don ci gaban irin wadannan kasashe a duniya karo na 3TH. Aref yace yana fatan zaman zafiya ta dore a cikin kasashen yankin don amfanin kowa. Daga karshe mataimakin shugaban kasan Iran ya bayyana cewa Iran tana goyon bayan kasar Armenia ta...
    ’Yan bindiga sun sace mutum 150 a mabanbantan hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban na jihar Zamfara a cikin kwana hudu. Kakakin Gwamnatin jihar ta Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ne ya tabbatar da hakan ga BBC. Sai dai duk da yake bai bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba, amma ya ce gwamnatinsu na iya kokarinta wajen ganin ta ceto su. Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Haka na zuwa ne a daidai lokacin da malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunna, ya ce kwamitin zaman lafiyar da yake jagoranta ya sami nasarar kulla yarjejeniyar zaman...
    Gwamnatin jihar Legas ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar duk wanda yake haka rijiyar burtsatse a unguwar masu hannu da shuni ta Lekki da ke jihar, ruwan masai yake sha. Babban Sakatare a ofishin da ke kula da magudanun ruwa da tsaftar ruwan sha a jihar, Mahmood Adegbite ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da ruwan sha a jihar a kwanakin baya. DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Mahmood ya kuma ce gurbataccen ruwan sha a unguwar zai iya haifar da barazanar lafiya matukar ba a bi hanyoyin da suka dace wajen...
    Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan.   Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheik Naim Qassem ya jaddada cewa, ba a samu wani abu na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba daga bangarenmu ba, amma Isra’ila ta keta wannan yarjejeniya sau dubbai. Da yake jawabi a wajen taron cika kwanaki 40 da shahadar Birgediya Janar Mohammad Saeed Izadi (Hajji Ramadan), Sheikh Qasem ya bayyana cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana fatan ganin an kwace makaman Hizbullah, ta yadda hakan zai bata damar cin karenta babu babbaka a kan kasar Lebanon. Ya ci gaba da cewa, “Abin da ya faru a Siriya ya yi tasiri matuka kan matakan da Isra’ila ta dauka, wanda hakan ya sanya ta yi nadama wajen tsara yarjejeniyar. Shugaban na Hizbullah ya jaddada cewa, Amurka ce...
    A wata ganawa da ya yi da manyan jami’an tsaro a wannan  Talata don kammala dabarun yakin Gaza, Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da kwace yankin zirin Gaza baki daya da karfin soji, duk da  hadarin da ke tattare da sauran fursunonin yahudawa da ke tsare a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza. Ofishin Netanyahu ya fitar da wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ke tabbatar da cewa Netanyahu ya gudanar da wani zaman  shawarwarin tsaro na tsawon sa’o’i uku, inda babban kwamnadan rundunar sojojin Isra’ila ya bayyana yuwuwar aiwatar da Shirin mamaye zirin yakin Gaza baki. Sanarwar ta kara da cewa rundnar sojin Isra’ila  ashirye take domin aiwatar da duk wani matakin da majalisar tsaron kasa...
    Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan karɓar belin wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da ya yi. Namadi ya yi murabus ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ya kafa kan lamarin. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne don “amfanin jama’a gaba daya” da kuma kare gwamnatin a “yaƙin da take yi da sayarwa da shan miyagun kwayoyi.” Sai dai ya dage kan cewa ba shi da laifi, amma ya yarda cewa ra’ayin jama’a na da muhimmanci, kuma yana da kyau ya kare kimar gwamnatin. Tuni Gwamna...
    Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya.   Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina.   A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa.   Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin da ya rage kwanaki biyu a yi bikin bude gasar wasanni ta duniya karo na 12, shugaban kungiyar shirya wasanni ta duniya (IWGA) Jose Perurena Lopez, ya bayyana shirye shiryen da aka yi a Chengdu a matsayin wadanda suka zarci tunani, yana cewa abu ne da zai kafa tahiri. Perurena ya shaidawa kamfanin dilancin labarai na Xinhua a yau Talata cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata, yana da burika sosai kan gasar, amma yana ganin abun da aka shirya ya zarce tunaninsa. Ya ce suna da tabbacin birnin Chengdu zai gudanar da gasar wasanni mafi kyau a tarihi saboda ingancin wuraren wasa da na masu aikin sa kai da ma na kwamitin shirya gasar, na nuna matukar kwarewa....
    Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun riga mu gidan gaskiya a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya janyo ruftawar ginin gidansu a ƙauyen Dankama da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na dare a ranar Litinin yayin da waɗanda ajalin ya katsewa hanzari ke tsaka da barci. Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri Bayanai sun ce wasu mutum huɗu waɗanda su ma lamarin ya rutsa da su an gaggauta miƙa su asibiti domin samun kulawa. Magidancin da aka yi wa wannan babban rashi, Muhammad Sani Garba, yayin ganawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
    Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544.9. Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi...
    Tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Adamu Maina Waziri, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa gwamnatinsa ta kere ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskar muni, wanda a yanzu ƙasar tana cikin mummunan bala’i.  Waziri, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC (African Democratic Congress), ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV. ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa “Babu ta inda gwamnatin Tinubu ba ta gaza ba. Ta gaza a dukkan fannoni, kama daga kan tsaro, tattalin arziki, yaƙi da cin hanci saboda komai ya tabarbare. Nijeriya ta koma baya...