Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare
Published: 9th, May 2025 GMT
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa.
Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar da aka yi watsi da ita Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitociMista Alausa ya bayyana cewa wannan matakai ya samu ne sakamako nazari da aka yi wajen sanya ƙaƙƙarfan jari a manyan makarantun ƙasar.
Ministan ya ce daga yanzu babu batun bai wa ’yan ƙasar kuɗaɗen ƙaro ilimi daga ƙetare, saboda yanayi da ake ciki da ma kyawun tsari da ake da shi a cikin ƙasar.
A cewarsa, dukkannin kwasa-kwasan da ’yan Nijeriyar ke zuwa wasu ƙasashen domin nazarin su, akwai su a cikin jami’o’i da ma kwalejojin fasaha masu nagarta da ake da su.
Ministan ya ce kuɗaɗen da ake kashewa wajen daukar nauyin karatun ɗaliban a ƙetare, zai fi dacewa a sanya su wajen inganta jami’o’in da kwalejojin da ake da su.
Sanarwar na zuwa ne a yayin da Hukumar Bunƙasa Arewa maso Yamma NWDC ta soke bayar da tallafin karatu ga ɗaliban da suka fito daga yankin.
Makonni kaɗan da suka gabata ne Hukumar ta NWDC ta fitar da sanarwar cewa tana neman haziƙan ɗalibai da suka fito daga yankin domin ɗaukar nauyin karatunsu a wasu ƙasashe ƙetare.
Sai dai wata sanarwa da hukumar ta fitar safiyar wannan Juma’ar, ta ce an soke tsarin, inda za ta mayar da hankali kan wasu ababen domin bunƙasa yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Hukumar Bunƙasa Arewa maso Yamma karatu
এছাড়াও পড়ুন:
Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi
’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum.
Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja.
Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a KatsinaMaharan, sun kai harin ne a kan babur, inda suka buɗe wa ’yan sandan da ke bakin aiki wuce.
Wani matashi da ya zo wucewa ta wajen ya rasa ransa.
Bayan haka, maharan sun kwashe bindigogin jami’an sannan suka tsere.
Daga baya, da misalin ƙarfe 11 na safe, suka sake kai wani hari a shingen da ke kan hanyar Ilafin, Isanlu a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, inda suka kashe wasu ’yan sanda biyu na rundunar MOPOL 70.
Mutanen yankin sun ce wannan hari ya jefa su cikin tsoro, suna ganin cewa maharan na neman bindigogi ne domin su ci gaba da kai hare-hare.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, Dokta Joshua Dare, ya yi Allah-wadai da hare-haren.
Ya bayyana harin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Ba wannan ne karo na farko da irin wannan hari ya auku ba.
A ranar 9 ga watan Satumba, an kashe jami’an tsaro guda biyar; ciki har da ’yan sanda uku da ’yan banga biyu, a wani hari kwanton ɓauna da aka kai musu a yankin Egbe da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma.
Gwamnatin Jihar Kogi, a baya-bayan nan ta zargi wasu matasa da taimaka wa ’yan bindiga a yankin, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai ce komai game da sabon harin ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.