Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38.

 

A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa.

 

Wannan Jaridar na da ra’ayin cewa, ‘yayan Kotun uku da Mai Shari’a Alkalan Kotun Thomas Okosun da ya yanke wannan hukunci, sun canci yabo kan tsaywar da suka yi kai da Fata na yanke wannan hukuncin, duk da matsin lambar da suka fuskanta, inda suka tabbatar da ikon da Hukumomin FCCPC da NDPC suke da shi.

 

Kazalika, abinda ya kara nuna mahimmancin hukuncin Kotun, musamma shi ne, yadda Kotun ta yanke hunci na irin bin ka’idar kundin tsarin mulkin kasa da kuma irin karfin ikon da Hukumar FCCPC take da shi.

Bugu da kari, yin watsi da Kotun ta yi kan jayayyar da Kamfanin na Facebook da kuma son yin zagon kasa kan matakan binciken Hukumar hakan ya nuna cewa, Hukumar za ta iya za ta iya yin amfani da ikonta a kan batun da ya shafi Kamfaninin kasa da kasa.

 

Hakazailka, Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa SERAP ta ce, Zuckerberg, ba wai kawai zai biya tarar bane, har da tabbatar da ya yi adalci da kuma biyan wadanda Kamfaninsa, ya yiwa kutse a cikin runbun sirrinsu, duba da cewa, wannan wani bangare ne, na hukuncin da aka yanke.

Wannan batu ne, da ya shafi ‘yancin ‘yan Adam wanda kuma ake da bukatar a tabbatar da anyi adalci.

 

Za a tabbatar da wannan yanke hukuncin na Koton ne kawai, idan an karfafa shi.

A karkashin sashe na 55 na dokar FCCP, Kamfanin na Facebook, na da ‘yancin daukaka kara kan wannan hukuncin da Kotun ta yanke.

Kazalika, Kotun ta bai wa Kamfanin na Meta, wa’adin kwakuna 60, ya biya tarar da Kotun ta ci shi, wanda sai dai, a bisa tarihin manyan Kamfaninin da kan batun yanke hukuncin Kotu, mai yuwa a samu targanda, wajen biyan tarar.

Idan har Nijeriya ta dauki wannan yanke hukuncin da Kotun ta yi da mahiimanci, dole ne ta shirya karfafa tsarin, wanda hakan zai sanya mai yuwa, sauran manyan Kamfanonin duniya, su bayar da na su hadin kan.

 

Sarkakiyar da ke cikin wannan Shari’ar, ta nuna yadda ake samun rashin daidaito a bangaren tafiyar da bunkasa tattalin azrki ta hanyar amfani da kimiyyar zamani.

Wannan tarar da dala miliyan 220 ba wata abace da ta taka Kara ta karya ba, idan aka yi la’akari da irin dimbin kudaden shiga da Kamfanin na Meta ke samu.

 

Misali, zango farko na 2024 Kamfanin ya samu kudin shiga da yawansu ya kai sama da dala biliyan 40.

Wannan jimlar kudin, ya jefa dimbin tambayoyi a zukantan jama’a na cewa, wannan tarar za ta Kamfanin na Meta, za ta dakatar da sauran manyan Kamfanonin duniya, dakatar da nuna halinsa na rashin bibiyayya saboda irin dimbin kudaden shigar da suke samu.

 

Abinda yake da mahimanci kan cin wannan tarar da Kotun ta yi shi ne yadda Kotun ta nuna cewa, Hukumar ta FCCPC itama ta na da karfin iko, akan manyan Kamfanonin na fasar zamani.

Ya zama wajbi, mu yabawa kokarin Hukumar ta FCCPC, kan mayar da hanhali da ta yi, musamman wajen gudanar da cikaken bincike kan wannan batun.

 

Kazalika, hukuncin da Kotun ta yanke, abu ne da nuna cewa, kusten da Kmafanin Meta ya yi a cikin rumbun sirrin masu amfani da kafar, abu ne, da ya sabawa dokar kasar nan.

Tun farko, an faro gudanar da wannan binciken ne began in 2020, amma sai 2025 ne, Kotun ta yanke hukunci na karshe.

Wannan yanke hukunci, zai zama tamkar wani darasi, ga sauran kasashen duniya da suma ke ciba da fusknatr irin wannan kalubalen.

Bugu da kari, wannan hukuncin ya kuma tabbatar da ‘yancin da ‘yan Nijeriya suke da shi, kan amfani da kafar sada zumunta ta zamani.

 

Ba wai kawai biyan tarar ba, dole ne Kamfanin na Meta, ya samar da sauye-sauye kan kare hakkin sirrin masu amfani da kafar da kuma kiyaye dokar kasar nan.

Haka sauran kamfanonin fasaha da ke gudanar da ayyukansu a kasar, dole ne su koyi darasin cewa, yanke wannan hukunci, abu ne da suma ya wajaba su kiyaye.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kotun ta yanke wannan hukunci a tabbatar da yanke hukunci

এছাড়াও পড়ুন:

Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore

Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Kasa sun kutsa inda ake tsare dan gwagwarmaya Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da karfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba.   Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da karfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a kokarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba..   A jiya Laraba ne dai Sowore ya amsa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa ya yi masa don ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da zanga-zangar da tsofaffin ‘yan sanda suka yi a makon jiya   Ana kuma son karin bayani kan zargin da Sowore ya yi na cewa, Babban Sufeton na Kasa ya kara wa jami’an ‘yan sandar da ke aiki a gidansa girma ba bisa ka’ida ba.   Sai dai ya yi watsi da zarge-zargen inda ya bayyana su a matsayin borin kunya da hukumar ‘yan sandan take don “dauke hankalin jama’a daga abin kunyar da Babban Sufeton na kasa Kayode Egbetokun da kuma hukumar ‘yan sandan ke aikatawa.   Tuni dai Kungiyar kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da kamun da hukumar ‘yan sandan ta Najeriya ta yi wa Sowore wanda ta ce ya sba wa ‘yancinsa na fadin albakacin baki.   Haka kuma Amnesty International ta bukaci a saki Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.   Shi ma dan gwagwarmaya Bello Galadanci da aka fi sani da Dan Bello, ya yi tir da kamun da aka yi wa Sawore tare da kiran a sake shin an take kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026
  • Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Wutar Lantarki Ta Kasa
  • Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
  • Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
  • Amurka Ta Kwace Kudaden Jami’ar Jahar California A Los Angeles Dala Miyon $584 Saboda Falasdinu
  • Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore
  • Kotun Ta Umurci Gwamnatin Neja Ta Janye Hukuncin Da Ta Dauka Akan Gidan Rediyon Badeggi
  • Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru
  • Gwamnatin Sin: Gwamnatin Jama’a Domin Jama’a
  • Nafisa ta cancanci kyautar Dala 100,000 da gida da OON — Pantami