Iran Ta Ce Ana Yin Nazari Kan Lokacin Gudanar Da Zagaye Na Hudu Na Shawarwari Tsakanin Iran Da Amurka
Published: 7th, May 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai dangane da haka da zarar an tantance lokaci da wuri.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Har yanzu ba a sanya ranar karshe da za a gudanar da shawarwarin na gaba ba, amma ana duban shawarar da Oman ta gabatar na gudanar da tattaunawar a farkon mako mai zuwa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Kakakin ma aikatar harkokin wajen Iran Iran da Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Kasa Na Sin Sun Yi Jigilar Fasinjoji Sama Da Miliyan 100 A Lokacin Hutun Ranar Ma’Aikata
Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, tare da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, kwanciyar hankali da kuma tsari. A yau, yawan fasinjojin da ke kan hanyarsu ta dawowa daga hutun ta jiragen kasa na ci gaba da karuwa, inda a yau ake sa ran za a yi jigilar fasinjoji miliyan 21.1 ta hanyar jirgin kasa na kasar, yayin da ake shirin kara jiragen kasan fasinja 1896 a kan adadin jiragen da ake amfani da su a baya wajen jigilar fasinjoji. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp