2025-11-06@05:45:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7588

«Italiya»:

    Gwamnatin Tarayya ta ce ƙofofinta buɗe suke ta sayar da dukkan matatun manta na Warri, Fatakwal da Kaduna ga ’yan kasuwa domin ƙarfafa gasa a fannin tace mai a Najeriya. Mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wata hira da Bloomberg TV a gefen taron...
    Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama  A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.   A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu...
      “Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.   Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na...
    Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja. Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da...
      A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan...
    Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Jirgin ƙasa ya...
    Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta...
      Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...
    Wani jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a shataletalen Abbatuwar Phototake da ke birnin Jos a Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da mutuwar direban da wani fasinja guda ɗaya, tare da jikkatar wasu mata biyu. Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na...
      Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda...
    Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko.   A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora...
    Ƙungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) tare da Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Gabas (NEDC), sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kan mata game da cutar sankara a Jihar Gombe, domin kare mata daga kamuwa da cutar. Dokta Halima Usman Faruk, ɗaya daga cikin likitoci mata da suka halarci wajen taron ta ce, cututtukan sankarar...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana numfashi a doron duniya. Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a. Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri. Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya. Abba ya yaba...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa daƙile hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka Mamdani...
    Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta Super Eagles, Eric Chelle, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Nigeria za ta lashe kofin nahiyar Afrika na 2026. Gasar da za a buga a kasar Maroko, Challe ya jadda kwarin gwiwarsa, bisa kafa hujja da zaratan yan wasan da Nigeria ta ke da su....
    Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne  “bisa umarnin alkali.” Ya kara da cewa...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza.   Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar...
    China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci. A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru...
    Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar,...
    Daga Khadijah Aliyu  An fara shirye-shirye  gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar,...
    Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta musanta iƙirarin da Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya. A wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a ranar Talata, ƙungiyar ta ce kalaman Trump ba su da tushe kuma suna iya haddasa tashin hankali da rikice-rikicen addini a yankin da...
    Zohran Mamdani ɗan jam’iyyar Democrat ya lashe zaɓen magajin garin birnin New York. Mista Mamdani shi ne musulmi na farko da ya lashe zaɓen maganin garin a tarihin birnin. Ɗan asalin Asiyan shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya zama magajin garin birnin mai muhimmanci a Amurka. Hakan na zuwa ne a ranar da ake...
    Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku. Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a...
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta...
    Kwamishinan Habbaka kiyon Dabbobi na Jihar Kano, Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fara ziyarar wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Ajingi da Dawakin Tofa. Ziyarar ta yi daidai da shirin gwamnati na kaucewa rikici, musamman sakamakon yuwuwar shigowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar cikin jihar. A Ajingi,...
    Pars Today – Wakilin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kalaman shugaban Amurka game da gwajin makaman nukiliya a matsayin abin tsoro. A cewar Pars Today, Amir Saeed Iravani, jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya rubuta a ranar Talata ga Shugaban Majalisar Tsaro da Sakatare Janar na Majalisar...
    Pars Today – Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa an gudanar da bincike mafi girma a tarihin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) a Iran, ba tare da an lura da wani karkata ba. Ya kara da cewa Washington da Tel Aviv suna kokarin dorawa duniya iko ta hanyar karya dokokin kasa da...
    Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirinsa na ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.150, don cike gibin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025. Buƙatar na kunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata. An yi musayar...
    Sai dai Sanata Barau Jibrin ya ce, “Ni ɗan Nujeriya ne, kuma zan faɗi ra’ayina. Ba na jin tsoron Trump. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci.” Maganarsa ta sa wasu Sanatoci dariya kafin Akpabio ya rufe tattaunawar, inda ya roƙi ’yan jarida su tabbatar da sahihancin labarai kafin su wallafa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan...
    An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen...
    Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa.   Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da...
    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba. Jaridar Vanguwar ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar, yana cewa ƙungiyar EU na jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da...
      A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Na Goyon Bayan Najeriya...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin...
    Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar. Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar...
    Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar. Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise...
    Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Yarima Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa, jam’iyyarsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP bai dawo kan mulki ba a babban zaben 2027. A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ke yawo a Facebook, an ga Abbas yana jawabi...
    A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage...
    Dan wasan gaban Paris Saint-Germain (PSG) ɗan asalin ƙasar Faransa, Ousmane Dembele, zai kasance cikin tawagar da za ta fafata da Bayern Munich a wasan Champions League da za a buga yau Talata. Dembele, wanda ya zura ƙwallo a wasan da PSG ta doke Bayern Munich da ci 2–0 a gasar Club World Cup zagaye...
    Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar...
    Ya ce, “Wannan ba yana nufin ba a kashe Kiristoci ba ne.” Abin da muke faɗa shi ne, ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba – ana kashe Musulmai ma,”   “Addinan biyu sun tabbatar da hakan, akwai kashe-kashen rayuka da yawa da ke faruwa a Nijeriya tsawon shekaru 16 da suka gabata da kuma fiye...
      Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.   Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin...
    Ƙasar China ta soki abin da ta kira yunƙurin Shugaban Amurka Donald Trump na yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a matsayin...
    KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE Daga Abdullahi Shettima. Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da...