Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali
Published: 9th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, da sanya kwanciyar hankali da kyakkyawan kuzari a duniyar mai fuskantar sauyi da tashe-tashen hankula.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin ziyarar da ya kai kasar ta Rasha. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba mai dorewa, cikin koshin lafiya kuma a babban mataki, sakamakon kokarin hadin gwiwa daga bangarorin biyu. Ya kuma yaba da kyakkyawar makwaftaka da kawance na dogon lokaci, da hadin gwiwar moriyar juna a matsayin wani muhimmin yanayi na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudummawa da daidaita ci gaban tattalin arzikin duniya tsawon shekaru, kana kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha wajen kiyaye tsarin cinikayyar duniya bisa ra’ayin bangarori daban daban, da kiyaye tsarin masana’antu da samar da kayayyaki cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Tattaunawar Cinikayya Da Za A Yi Tsakanin Babban Jami’inta Da Na Amurka
Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce sabuwar gwamnatin Amurka ta dauki jerin matakan kakaba haraji na ba gaira ba dalili, lamarin da ya kawo tsaiko ga dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, tare da kawo kalubale mai tsanani ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Kuma domin kare hakkoki da muradunta, Sin ta dauki matakan mayar da martani.
A cewar kakakin ma’aikatar, a baya bayan nan, bangaren Amurka ya bayyana shirinsa na tattaunawa kan batun harajin da sauran batutuwa masu nasaba da shi ta hanyoyi da dama. Kuma bayan nazartar sakonnin Amurka, kasar Sin ta yanke shawarar tattaunawa da ita, bisa la’akari da burin al’ummun duniya da muradun kasa, da kuma kiraye kiraye daga masana’antun Amurka da masu sayayya na kasar. Kuma a matsayinsa na jagoran tawagar Sin a tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Amurka, mataimakin firaministan kasar He Lifeng zai gana da sakataren Baitul malin Amurka Scott Bessent.
Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba Korar Ma’aikata: Likitocin Birnin Tarayya Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 3Kakakin ya ce matsayar kasar Sin bata sauya ba, idan aka tilasta mata shiga fada, to a shirye take, idan kuma tattaunawa ake son yi, kofarta a bude take.
Ya kuma yi gargadin cewa, duk wani yunkuri na fakewa da tattaunawar a matsayin wata dama ta matsin lamba ko barazana, toh, kasar Sin ba za ta cimma wata yarjejeniyar da za ta kai ga sadaukar da ka’idojinta, ko lalata tsarin adalci da tsare gaskiya a duniya ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp