Leadership News Hausa:
2025-05-10@01:19:05 GMT

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Published: 9th, May 2025 GMT

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar?

Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan 1 a kudin tikitin shiga a kasuwar cikin gida kadai. Bugu da kari, wannan adadi, ya haura sama da dala biliyan 2 a kudaden shiga a duk duniya. Wannan abin a yaba ne, amma a wani bangare, Wannan rahoton kadai, zai iya fusata gwamnatin Amurka, ganin cewa, kasar tuni ta yi wa kasar Sin bakin fenti da cewa, ita ce babbar abokiyar hamayyarta a bangaren kasuwanci a duniya.

In ba a manta ba, da ma tun bayan rantsar da gwamnatin Trump, ya sha alwashin kakaba haraji kan duk hajojin da ake shigowa da su Amurka. Hukuncin da gwamnatin ta yanke, lallai ba shakka ba ta canja ra’ayi ba kamar yadda ta yi da sauran sanarwar haraji, wanda hakan ya tabbatar da cewa, yakin cinikayyar duniya har da fina-finai.

Tun ba a yi nisa ba, Amurkawa sun fara dandana kudar yakin cinikayya, inda farashin kayayyaki suka fara tsauri ga ‘yan kasar.

Don haka, akwai yiwuwar Amurkawa za su nisanta daga duk wani fim da aka shirya a ketare da zarar sun ga farashin tikitin ya yi tsada. Shin hakan zai iya zama abin da gwamnatin ke so?

Irin wannan hukunci da Amurka ke dauka, hakan yana da mummunan tasiri akan ‘yan kasarta ko da kuwa lamarin zai shafi sauran ‘yan kasashen waje.

Wai mu tambayi kanmu mana, Amurka ta rasa Dattawa da Masana ne wanda za su ba ta shawara kan harkokin tattalin arziki ne, ko kuwa Gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da shawarwarin su ne?

Masana da dama na ganin cewa, wannan mataki na zabga harajin kashi 100 bisa 100 a fina-finai zai haifar da mummunan sakamako ga masana’antar Hollywood, sannan kuma zai gurgunta kyakkyawar alakarta da takwarorinta na duniya.

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Tattaunawar Cinikayya Da Za A Yi Tsakanin Babban Jami’inta Da Na Amurka

Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce sabuwar gwamnatin Amurka ta dauki jerin matakan kakaba haraji na ba gaira ba dalili, lamarin da ya kawo tsaiko ga dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, tare da kawo kalubale mai tsanani ga farfadowar tattalin arzikin duniya. Kuma domin kare hakkoki da muradunta, Sin ta dauki matakan mayar da martani.

A cewar kakakin ma’aikatar, a baya bayan nan, bangaren Amurka ya bayyana shirinsa na tattaunawa kan batun harajin da sauran batutuwa masu nasaba da shi ta hanyoyi da dama. Kuma bayan nazartar sakonnin Amurka, kasar Sin ta yanke shawarar tattaunawa da ita, bisa la’akari da burin al’ummun duniya da muradun kasa, da kuma kiraye kiraye daga masana’antun Amurka da masu sayayya na kasar. Kuma a matsayinsa na jagoran tawagar Sin a tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Amurka, mataimakin firaministan kasar He Lifeng zai gana da sakataren Baitul malin Amurka Scott Bessent.

Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba Korar Ma’aikata: Likitocin Birnin Tarayya Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 3 

Kakakin ya ce matsayar kasar Sin bata sauya ba, idan aka tilasta mata shiga fada, to a shirye take, idan kuma tattaunawa ake son yi, kofarta a bude take.

Ya kuma yi gargadin cewa, duk wani yunkuri na fakewa da tattaunawar a matsayin wata dama ta matsin lamba ko barazana, toh, kasar Sin ba za ta cimma wata yarjejeniyar da za ta kai ga sadaukar da ka’idojinta, ko lalata tsarin adalci da tsare gaskiya a duniya ba. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha
  • Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
  • Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki
  • Amurka ta matsa wa ƙasashe da ke fuskantar haraji su amince da Starlink
  • ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato
  • Gwamnatin Siriya Tana Neman Tattaunawa Da Gwamnatin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
  • Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Tattaunawar Cinikayya Da Za A Yi Tsakanin Babban Jami’inta Da Na Amurka
  • Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Ce: Sanarwar Trump Kan Batun Yemen Gazawa Ce Ga Netanyahu