Ficewar ’yan majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren majalisar Wakilai
Published: 8th, May 2025 GMT
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC
Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon.
Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama’iyyar APC, wanda dawowar su jam’iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam’iyyar take da shi a Jihar Katsina.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana.
Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a matsayin tubalin cigaba.
Ya kuma sanar da cewa Jihar Jigawa ce za ta karbi bakuncin taron gidauniyar na shekarar 2026, wanda zai ƙunshi laccoci, shirye-shiryen wayar da kan jama’a da bada lambar yabo.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya gode wa Gidauniyar bisa wannan yabo da kuma zaɓar Jigawa don karɓar taron na 2026.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bin sawun Sardauna ta hanyar shugabanci na gaskiya, tsare-tsaren jin daɗin jama’a da kuma zuba jari a fannin ilimi.
Ya tabbatar da cikakken goyon baya wajen shirya taron 2026 cikin nasara.
Tawagar ta haɗa da Madakin Zazzau, Malam Muhammad Munir Ja’afaru, da wasu jami’an Gidauniyar.