Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha
Published: 10th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin kulla takardar hada kai da aka shirya a fadar Kremlin a jiya Alhamis. A shaidar shugabannin kasashen biyu, shugaban CMG Shen Haixiong ya wakilci hukumar fina-finai ta kasar Sin da ministar hukumar al’adu ta Rasha Olga Borisovna Lyubimova sun kulla hannu da yi musanyar takardar “Shirin samar da fina-finai bisa hadin gwiwar hukumar fina-finai ta kasar Sin da hukumar al’adu ta Rasha kafin shekarar 2030”.
Shirin ya taka rawar gani wajen gaggauta hadin gwiwar kasashen biyu ta fuksar samar da fina-finai tare, da shigowar fina-finan junansu da gabatar da bukukuwan fina-finai tsakaninsu, ta yadda za a kara tuntubar al’adu da koyi da juna a bangaren fina-finai don ciyar da huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakaninsu a sabon zamani gaba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA