Fafaroma Leon na 14 : Ina matukar bakin cikin abinda ke faruwa a Gaza
Published: 11th, May 2025 GMT
Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta nan da nan, a ba da agajin jin kai ga fararen hula da suka gaji, kuma a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su.”
Fafaroman ya kuma yi kira ga “manyan kasashen duniya” da su dakatar da yaki, ya kuma yi kira da a samar da zaman lafiya “adalci” mai “dorewa” a Ukraine a wani jawabi da ya gabatar yau Lahadi a sallarsa ta farko bayan zama fafaroma.
Shugaban ‘yan katolika na duniya ya kuma yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Indiya da Pakistan, amma ya yi kira da a samar da maslaha mai dorewa tsakanin kasashen biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shawarar Gudanar Da Harkokin AI Na Duniya Na Jagorantar Ci Gaban Wayewar Kan Dan Adam Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani
A yanzu haka, fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI na sauya zaman rayuwar dan Adam. Ga misalin, motoci mara matuki na saukaka tafiye-tafiye na dan Adam, samfurin binciken yanayi na iya hasashen hanyar guguwa a cikin dakika 10 kawai… Amma, fasaha ta zama kamar “takobi mai kaifi biyu”, wadda a lokaci daya take kuma kara haifar da matsaloli, kamar su fallasar sirri, yaudara ta hanyar amfani da AI, da hadarin rashin aikin yi. Bisa wannan yanayin da ake ciki na kasancewar alfanu da matsaloli tare, ’dan Adam na bukatar hadin gwiwa cikin gaggawa don daidaita ci gaban fasahar AI, da kafa tsarin gudanar da harkokin fasahar AI na duniya, da nemo daidaito tsakanin kirkire-kirkire da tsaro, da nufin tabbatar da ganin an inganta ci gaban wayewar kai ta hanyar amfani da fasaha. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka kaddamar da “shawarar gudanar da harkokin AI ta duniya”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp