Almundahana: Jamiyar LP Ta Nada Sanata Ireti Kingibe Domin Binciken Tsohon Shugaban Jam’iyyar
Published: 8th, May 2025 GMT
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar.
Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar tare da batanci da haddasa rikici.
Sanata Usman ta Kara da cewa, Abure yana aikata laifufuka wanda suke kalubalantar mutunci Jam’iyar da kuma yin karo da manufofin dimokuradiyya. Don haka, majalisar zartaswa ta Jam’iyar ta dauki matakin kaddamar da bincike kan wannan munanan halayya.
Bugu da Kari Sanata Nenadi Usman tace majalisar zantaswa na Jamiyar Labour bayan dogon nazari akan hukuncin da kotun koli ta Kasa ta yi na ranar 4 ga watan Afrilun 2025, Jam’iyar ta nuna matukar damuwarta akan Yadda Julius Abure yake amfani da sunan shi a matsayin Shugaban Jam’iyar bayan dakatar da shi.
Ta ce, abubuwan da Julius Abure yake yi ya sabawa dokar Kasa kuma ya ci mutuncin Jamiyar. A sabo da haka ne tace kundin tsarin mulkin Jamiyar na shekarar 2019 (Wanda aka yi wa Kwaskwarima) ya Basu damar daukan kwararan matakai da hukunci akan Julius Abure.
Daga bisani, Sanata Nenadi Usman ta nuna rashin amincewarta akan Yadda Julius Abure yake cin mutunci jagoran jam’iyar Labour na Kasa, Peter Obi da Gwamna Alex Otti. Tace Abure da mukarabansa wadanda wa’adinsu ya kare, basu da hurumin magana da yawun Jam’iyar kuma baza su iya dakatar da Gwamnan ba ko wani mamban Jamiyar.
Ta kuma shaidawa ‘Yan Nijeriya cewa, Jam’iyar ta sanar da Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) akan shirye-shiryenta na gudanar da zabuka a matakai daban-daban tare da gudanar da babban taron Jam’iyar na kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Tsokaci Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa: Shugaban Kasar Iran Zai Gana Da Shugaban Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe.
Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa duk wadanda batutuwa da suke fitowa daga majiyoyi marassa tushe da asali kuma mafi yawansu labarai ne na karya na bogi da ba su da wata madogara mai tushe. Baqa’i ya jaddada cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar ita ce ke da alhakin ba da bayanai dangane da ayyukan jami’an diflomasiyya, ciki har da batun tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, cikin gaskiya, kwarewa, da kuma lokacin da ya dace.