2025-05-03@21:26:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 24
«ɗaya daga cikin»:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...
Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu, 2025, Sarki Sanusi II ya sanar da ɗaga likafar baffansa kuma Wamban Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, zuwa matsayin sabon Galadiman Kano. Kasa da makonni biyu bayan haka, a ranar 21 ga Afrilu, 2025, Sarki Aminu Ado Bayero ya mayar da martani ta hanyar naɗa babban yayansa kuma ɗan fari ga marigayi Sarki Ado Bayero, Sanusi Ado Bayero, a matsayin nasa Galadiman Kano. Wannan sabon...
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027. Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya. Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Bankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito. Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba...
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya. Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi. Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Hakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal. A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a...
Gwamnatin Jihar Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya. Wani mai magana da yawun gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya gaya wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an gano wannan badaƙalar ce a yayin da ake tantance tsarin biyan albashin gwamnati. Dr. Sani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan ma’aikata daidai kuma akan lokaci, kuma gano waɗannan matsalolin wani ɓangare ne na gyara al’amura. Ya ce sun duba bayanan ma’aikata ta hanyar amfani da hotunan yatsa a matakin jiha da ƙananan hukumomi. “Tsohuwar hanyar biyan mutane tana da matsaloli. Mun gano ma’aikata 240 suna...
Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa, sun yaba wa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, bisa bai wa Nasir Bala Ja’o’ji muƙami a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi da Fasaha ta Tarayya, Potiskum, da ke Jihar Yobe. A wata wasiƙar taya murna da shugaban shiyyar ƙungiyar, Makama Dan Kaduna, ya sanya wa hannu bayan wani taro da suka gudanar a Kaduna, sun ce Ja’o’ji mutum ne mai kishin matasa da ƙoƙarin inganta rayuwarsu. Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji Sun bayyana cewa, “Wannan muƙami da Sarkin Daura zai ba shi, ya ƙara tabbatar da binciken da muka gudanar wanda ya nuna cewa Ja’o’ji yana cikin shugabannin matasa 10...
Duk da kasancewarta matar aure kuma uwa daga Arewacin Nijeriya, sannan kuma ga karatu tana yi, a lokaci guda, amma hakan bai hana ta samun nasarar zama gwarzuwar ɗalibar da ta kafa sabon tarihin da sai da aka shekara 35 rabon da a samu wani mahaluki da ya kafa irinsa a fannin ilimin shari’a. A yayin da take karatu, A’isha Widad, mai shekara 24 a duniya, ta fuskanci ƙalubalen da suka danganci haɗa karatu mai zurfi da kuma rayuwar aure — kama daga ɗawainiyar kula da gida zuwa na juna biyu da na jego da kuma shayarwa — amma duk da haka, ta kafa tarihin zama mutum ɗaya tilo da ta kammala digirinta na farko da Daraja na ɗaya (First...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya. Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya. An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karɓar lambar karramawa da aka yi masa shi da wasu shugabnnin da Ƙungiyar Inganta zaman lafiya ta “Peace Building Development Consult” (PBDC) ta yi musu. Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar...
Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna. An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa. Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu...
Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23. Fulham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa. Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta...
Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 177 dubu dari 615 da 840 daga wani babban kantin da ke Millenia a birnin Orlando da ke Jihar Florida a Amurka a ranar 26 ga Fabrairu. A cewar sashen ’yan sanda na Orlando, Glider ya dauki matakin da ba a saba gani ba na haɗiye ’yan kunnayen da ya sace. A cewar rahoton ’yan sanda da kafar yada labarai ta...
Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Rikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba. Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar. Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano. Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci Ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin gargajiya. Ya ce gudunmawar da ya bayar za a ci...
A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali. Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.” Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah. Yadda ake fitarwa Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda...
Allah Ya yi wa Alhaji Nasiru Ahali, Shugaban Kamfanin Mainasara & Sons, rasuwa. Marigayin wanda yake shahararren masanin masana’antu ne ya rasu yana da shekara 108. Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP A cewar majiyoyin na kusa da iyalan marigayin ɗan kasuwar ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano a daren ranar Alhamis. Ana girmama Ahali a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan masanin asalin masana’antu a Kano. Ya yi ƙoƙari ya kafa tsarin kasuwanci na yau da kullun. A tattaunawarsa da Daily Trust a shekarar 2018, marigayi Ahli ya bayyana cewa sana’arsa ta haɗa da buga littattafai, bugu takardu, masana’antar bulo, sana’ar...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗora wa alhakin haddasa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya. Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu na siyasa ya samo asali ne daga yanayi da ya fi ƙarfinsu gaba ɗaya. “Gaskiya ni na yi imanin cewa ni da Kwankwaso ba mu da wata matsala ta zama tare a ƙarƙashin inuwar jam’iyya ɗaya. A duk abubuwan da suka faru, da ni da shi duk babu mai laifi,” inji shi. Da yake tsokaci kan lokacin da suka...
Aƙalla matasa 150 masu kirkire-kirkire daga yankin Arewa sun hallara a Kano don halartar “Innovate North” Business Development and Innovation Hackathon, wani shiri da ke da nufin ƙarfafa harkokin kasuwanci da sauya fasalin dijital. Yayin da take jawabi a taron, Maryam Lawan Gwadabe, wacce ta shirya gasar kuma ita ce wanda ta kafa Blue Sapphire Hub, ta jaddada mahimmancin shiryawa da ba da jagora ga matasa domin bunkasa basirarsu. APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara “Yawancin matasa masu kirkire-kirkire ba su da jagora ko kuma wanda zai taimaka musu su sauya tunaninsu zuwa kasuwanci mai ɗorewa,” in ji ta. Gwadabe ta bayyana gasar a matsayin babbar...
A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron. Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya? Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester. Mece Ce Matsalar Manchester United? AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin...
Ƙungiyar Shugabannin Kiristoci na Kudancin Kaduna (SKCLA) ta yi kira ga al’ummar yankin da su rungumi haɗin kai da ƙaunar juna a matsayin tubalin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba. Shugaban ƙungiyar SKCLA, Fasto Emmanuel Nuhu Kure ne ya yi wannan kiran ga mazauna yankin a wajen taron addu’ar shekara-shekara da ake gudanarwa a garin Kafanchan don kyautata alaƙarsu da Ubangiji tare neman ɗauki daga gare Shi don samun zaman lafiya da wadata. DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata An kama gungun masu yi wa Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura “Lokaci ya yi da za mu haɗa kai da tunanin mu waje ɗaya da manufa ɗaya don sake gina al’ummomin Kudancin...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci. Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina. Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba. “Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba. “Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko. “A yanzu na ƙara...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...