Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Kai Hari Kan Ofishin Jakadancin Kasarsa A Kasar Sweden
Published: 10th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka kai harin.
A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da ministar harkokin wajen Sweden Maria Malmer Stenergård, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma na ofishin jakadancin.
A yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin kasar Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka aikata wannan lamari tare da daukar matakan da suka dace don hana sake aukuwar lamarin.
Araghchi ya kuma bayyana dangantakar dake tsakanin Tehran da Stockholm tare da jaddada bukatar yin zurfafa tuntuba domin warware rashin fahimtar juna da inganta hadin gwiwar kasashen biyu.
A nata bangaren, ministar harkokin wajen kasar Sweden ta jaddada aniyar kasarta na kare cibiyoyin diflomasiyyar Iran, tana mai jaddada cewa Stockholm za ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen kasar Sweden
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Zaman Lafiya ta Duniya: Kungiyar Arewa Ta Nemi Ƙarfafa Sirrin Tsaro Don Kare ‘Yan Najeriya
A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa.
Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna.
Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan.
Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka wajen magance matsalalon tsaro da suka addabi Kasar nan.
Ya jadda da bukatar ganin Shugabanni da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro su daina nuna son zuciya da siyasantar da sha’anin tsaron Kasa domin amfanin al’umma.
Dakta Abdullahi Idris ya tunatar da Shugabanni cewa Allah zai tambaye su yadda suka Shugabanci al’umma, a ranar gobe kimyama.
Daga nan sai Shugaban Kungiyar ya bukaci Gwamnati a dukkan matakai da Hukumomin tsaro su rubunya kokarin da suke yi kana su yi amfani da rahitannin tsaro na sirri wajen maganin wannan matsala ta tsaro.
COV/LERE