An Dakatar Da Ayyukan Jam’iyyun Siyasa A Kasar Mali
Published: 9th, May 2025 GMT
Majalisar koli ta sojojin kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa da duk wasu kungiyoyi masu alaka da su.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai majalisar sojan kasar ta Mali ta fitar da dokar wacce shugabanta janar Assimi Goita ya rattaba wa hannu, wanda kuma aka sanar ta kafafen watsa labarun kasar.
Sanarwar ta ce, an dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasar har illa masha Allahu.
Dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasar bai shammaci ‘yan siyasar kasar ta Mali ba, bayan da a baya a taron kasa da aka yi, aka gabatarwa da gwamnatin sojan shawarar dakatar da jam’iyyun siyasar da kuma nada shugaban majalisar koli ta sojan kasar a matsayin shugaban rikon kwarya na tsawon shekaru biyu, da kuma za a iya sabuntawa.
A karon farko, daruruwan mutanen kasar sun fito wani gangami a makon da ya shude domin yin kiran a mayar da kasar kan turbar demokradiyya.
Wani daga cikin wadanda su ka tsara gangamin Sheikh Umar Dombiya ya fada wa kamfanin dillancin labarun AP cewa; “Ban yi mamakin wannan matakin ba, na tsammaci farwuarsa, domin wannan shi ne tunaninsu,amma za mu ci gaba da aiki tukuru domin kare tsarinmu na demokradiyya a Mali.
Masu Zanga-zangar dai sun rika bayar da taken nuni kin jinin mulkin soja.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Na Fatan Kwamitin Sulhun MDD Zai Goyi Bayan Kuduri Game Da Halin Da Iran Ke Ciki
Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Rasha, da Sin da Pakistan, sun gabatar da wani daftarin kudurin kwamitin sulhun MDD, kan halin da ake ciki a Iran. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya shaidawa nuni taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, harin da Amurka ta kai kan wuraren da kasar Iran ta girke na’urorin nukiliya ya saba wa manufar tsarin dokokin MDD, tare da kara ta’azzara tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya, don haka, dole ne kwamitin sulhun ya dauki mataki kan batun.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin na sa ran mambobin kwamitin za su goyi bayan daftarin kudurin, tare da sa kaimin kwamitin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, da tsaron kasa da kasa.
‘Yan Bindiga Sun Sace Dukkan Fasinjojin Motar Bas A Jihar Benuwe Yanzu-yanzu: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jami’ar Neja Bayan Kashe ƊalibiDangane da goyon bayan da majalisar dokokin Iran ta nuna game da rufe mashigin tekun Hormuz, mashigin tekun Farisa, da yankin ruwan da ke kewaye da shi muhimmiyar hanyar cinikayyar kayayyaki da makamashi ce ta kasa da kasa. Kuma kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara kokarin sa kaimi ga kwantar da kurar rikici, don magance karin tasiri da tashin hankalin da ake fuskanta a shiyyar ka iya haifarwa ga gaban tattalin arzikin duniya.
Baya ga haka kuma, kakakin ya bayyana cewa, ‘yan kasar Sin 3,125 sun riga sun fice daga kasar Iran lami lafiya, kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake Isra’ila, ya taimaka wa ‘yan kasar Sin sama da 500 barin Isra’ila yadda ya kamata, kana ya taimaka wa wasu ‘yan kasar Birtaniya, da Indiya, da Poland wajen barin kasar lami lafiya. (Mai fassara Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp