2025-11-14@08:42:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9002
«Fatakwal»:
Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta...
Iran da China sun bayyana shirinsu na haɓaka alaƙar da ke tsakaninsu da kuma haɓaka haɗin gwiwa bisa ga yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu. Jakadan Iran a China Abdolreza Rahmani Fazli ya ce a ranar Alhamis cewa Tehran a shirye take ta ƙarfafa cikakken haɗin gwiwa da Beijing a sassa daban-daban a matsayin...
Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya soki Shugaban Amurka Donald Trump saboda kin halartar taron shugabannin G20 da ke tafe, yana mai gargadin cewa yunkurin ware kasar da ke karbar bakuncin taron ba zai yi wani tasiri ba ga taron ko sakamakonsa. Trump ya sanar da cewa shi ko wani jami’in Amurka ba za...
Majalisar Wakilai ta umarci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Shirya Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) da su dakatar da shirin fara amfani da tsarin jarabawa ta kwamfuta a jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2026. Umarnin ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa da Kelechi Wogu ya gabatar a zaman majalisar na ranar...
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “damuwarsa mai zurfi” game da rahotannin “mummunan kisan gillar da kuma take hakkin bil’adama masu tsanani a El Fasher,” Sudan, yana mai cewa “tashin hankali ma yana karuwa a Kordofan.” A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X a ranar Alhamis, Guterres ya jaddada bukatar...
Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis. WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin...
A bisa wannan dalilin, ya kuma zama waji, manyan hafsohin tsaron su mayar da hankali, wajen ingnata jin dadi da walwalar dakarun sojin, musamman duba da cewa, manyan hafsoshin tsaron, su ba baki ne, kan wadannan kalubalen ba, domin kuwa kafin nada su, a baya an nada su kan makamai da ban da ban. Kwarewar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi kira ga kasar Japan da ta janye kalaman baya-bayan nan da firaministar kasar ta furta, dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, ta shirya girbar sakamakon danyen aikinta. Lin Jian, ya yi kiran ne yayin taron ganawa da manema labarai na...
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kaduna, ta ƙone fiye da tan 52,000 na miyagun ƙwayoyi a bainar jama’a a ƙauyen Karofi da ke Kufena, a kan tsohuwar hanyar Birnin Gwari da ke Zariya. An gudanar da bikin ƙone kayan ne a wannan Alhamis ɗin, inda Birgediya Janar...
Shugabar kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya (IOC), Kirsty Coventry, ta halarci bikin bude gasar wasannin kasa ta Sin karo na 15 a lardin Guangdong da yammacin ranar 9 ga Nuwamba. A ranar 12 ga wata kuma, Coventry ta yi wata hira ta musamman da ‘yar jarida daga babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na...
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta zargin cewa yana da wani saɓani da rundunar sojin Najeriya, yana mai cewa batun rikicin fili ne ya haɗa jami’ansa da wasu sojoji sa-in-sa da a yanzu ake faman cece-kuce a kai. Wike ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, inda...
Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles ta doke tawagar ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka fafata a yammacin wannan Alhamis. Wasan wanda aka soma da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat a Morocco, ya bai wa Super Eagles damar...
Rahotanni sun bayanna cewa kakakin fadar kremlin Dimitry peskov yayi gargadi game da barazanar baya yana nan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubios yayi da cewa akwai yiyuwa Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya. Ci gaba da gwajin nukiliya ga Amurka zai kara fadada zaman dardar a duniya, kuma zai kawo cikasa ga...
NDLEA ta bayyana cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar wannan matsala, tare da wayar da kan jama’a da kula da masu fama da shan ƙwayoyi, domin kare tsaron rayuka da zaman lafiya a ƙasar nan. Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilin shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammadu Buba Marwa (mai ritaya),...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa November 12, 2025 Daga Birnin Sin Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing November 12, 2025 Daga Birnin Sin Madalla Da...
A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026. Wasan da za a buga da karfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa...
Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa...
Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25
1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari...
Daga karshe Tanimu Akawu ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim da su kasance masu hakuri kada suyi hassada kuma su dage da addu’oi, Harkar fim sana’ace da ake samun rufin asiri da daukaka, kuma fim sana’ace wadda sai dai kai ka barta ba dai ta barka ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nishadi...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa...
Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya ( IEA) Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka...
Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da wani Hakimi da Dagaci a ƙaramar hukumar Funakaye bayan barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin. Rahotanni sun ce rikicin dai ya yi sanadin mutuwar ɗan sanda ɗaya tare da jikkatar wasu jami’an tsaro da dama. Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur...
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal na kashi 15, wanda a baya aka amince da shi domin daidaita farashin shigo da kayayyaki da yanayin kasuwa. Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA) ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a, George...
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar. Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa...
A ci gaba da aikace-aikacen yaki da ta’addanci da laifuffuka a fadin Jihar Taraba karkashin Operation Lafiya Nakowa, sojojin Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya / Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu nasarar kama wani wanda ake zargin dillalin makamai, tare da kwato makamai da harsasai daga hannunsa. Wannan na kunshe ne...
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa hangen nesansa na ƙarfafa masana’antu a jihar shi ne domin ƙirƙirar ayyukan yi da kuma inganta rayuwar jama’ar jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnati ta Lafia, yayin da yake karɓar bakuncin sabbin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu aiko rahotann dake Jihar (Correspondents’ Chapel)....
A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na...
Gidauniyar fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar. Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin...
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ministan FCT ya je filin mai lamba 1946 a ranar Litinin inda ya zargi sojoji da hana jami’ai daga Ma’aikatar Kula da Ci Gaban FCT aiwatar da umarnin dakatar da aiki a filin. Ana zargin cewa, filin yana da alaka da tsohon Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu...
Wani babban ɗan Kasuwar Singa da ke Jihar Kano, Alhaji Salisu Abdullahi, ya ce ya yi asarar kaya da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 120 a gobarar da ta auku da safiyar ranar Alhamis, wadda ƙone shaguna da yawa. “An kira ni da misalin ƙarfe 6 na safe, na garzaya zuwa kasuwa, sai kawai na...
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar. Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na...
Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba. Babban...
A yammacin jiya ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki. A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa...
Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu...
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da...
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu...
Kungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta bukaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Najeriya. Aminiya ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne...
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a...
Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar...
Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina yi wa masu fafutukar neman “‘Yancin kan Taiwan”, ingiza mai kantu ruwa, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun ya bayyana a yau Laraba. An ruwaito cewa, gwamnatin Japan a ranar Talata ta ba da wata lambar girmamawa ga tsohon “wakilin Taiwan...
Aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar ɗaukar aikin soja a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da ɗaruruwan matasa masu neman aikin suka kutsa cikin filin wasan ba...
Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe. Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma...
Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi...
Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata. An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi...
Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi. Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani...
’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati. Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu...
A shekaru fiye da 20 da suka gabata, birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin ya yi suna domin samar da takalma, kuma kayayyakin da ya samar sun samu karbuwa a duniya domin suna da araha. Amma ma’aikatan kamfanonin samar da takalma sun yi aiki har na tsawon awoyi 14 a kowace rana, inda...
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko...