2025-05-03@21:14:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2845
«sauya sheƙa»:
Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta miƙawa Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON kuɗi sama da Naira biliyan 6 a matsayin kuɗin jigilar maniyyatan jihar na 2025 na zuwa Saudiyya. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Labbo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, ya ce hukumar ta raba tare da sayar da kason kujerun aikin Hajji sama da 1,000 na jihar ga ƙananan hukumomi 27 ga mahajjata. Sojoji sun kama jami’an tsaro da ke haɗa baki da ’yan ta’adda ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe Umar Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kammala shirye-shiryenta da suka haɗa da biza ga maniyyatan jihar, inda a yanzu...
Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas. Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jami’ai biyu na rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojoji domin yaƙar ’yan ta’addar. ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu A cewar Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, an kame sojojin ne a wani samame da aka yi tsakanin ranakun 26 zuwa 29 ga watan Afrilu a cikin ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali. Ya ce, suna daga cikin waɗanda suke taimakawa ’yan ta’adda huɗu da sojojin suka kama. Kangye ya...
A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai. Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji. Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.” Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya...
Ƙungiyar mayaƙan ISWAP sun mamaye garin Buni Gari a daren Juma’a da ƙarfe 12:00 na dare, mahaifar Gwamna Buni da ke ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe inda suka kai wani harin ba zata a garin da kuma barikin soja ta 27 da ke garin. Wata majiya mai tushe daga garin ta tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na daren Juma’a, inda maharan suka ƙona wani ɓangare na hedkwatar rundunar ta 27 da ke Buni Gari a Jihar ta Yobe. An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu An gano shanu 25 da suka ɓace a dajin Sakkwato Wannan gari na Buni Gari wadda bai wuce kilomita bakwai ba daga Buni Yadi hedkwatar ƙaramar hukumar ta...
Wata kotu a kasar Tunisiya ta daure tsohin fira minsitan kasar Ali al-Aridh zaman kurkuku na tsawon shekaru 34 Shi dai al-Aridhi wanda dan jami’iyyar masu kishin musulunci ta ‘al-Nahdha’ ya zama fira minista ne daga shekarar 2013 zuwa 2014. Kotun ta zargi tsohon Fira ministan da hannu a ayyukan ta’addanci, lamarin da shi da jam’iyyar tasa su ka kore. A cikin makwannin bayan nan dai ana yanke wa ‘yan adawa hukuncin dauri, lamarin da masu fafutuka suke dauka a matsayin bita da kulli na siyasa da shugaba Kais Sa’id yake yi.
Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450. Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin. Gwajin makamin na sojojin Pakistan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakaninta da kasar Indiya, bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Kashmir. A ranar 22 ga watan Afrilu ne dai aka kai wani hari akan masu yawon bude ido a yankin na Kashmir wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 26. Da akwai fargabar cewar kasashen biyu za su tsunduma cikin...
A yanzu kuma, Amurka na son kawar da dimbin gibin kudaden asusunta, ta hanyar amfani da kare-karen haraji. A baya Amurka ta yi kokarin hakan ba tare da cimma nasara ba, kuma a yanzu ma hakan ne zai sake faruwa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga HKI da ta kawo karshen hare-haren da take kai wa kasar Syria,jim kadan bayan da sojojin HKI su ka sanar da cewa; a karon farko jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniya ya sauka a Suwaidah. A daren jiya Juma’a ne dai HKI ta kwana tana luguden wuta akan yankuna mabanbanta na kasar ta Syria da su ka hada da birnin Damascuss har da daura fa fadar shugaban kasa. HKI tana kai wannan hare-haren ne dai da sunan bayar da kariya ga ‘yan Duruz domin hana sojojin Syria ci gaba da kai musu hare-hare. Jami’in diplomasiyyar MDD mai kula da kasar Syria Geir Otto Pedersen ya rubuta a shafinsa na X sakon yin...
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sashen tawagarta masu tattara bayanan sirri (IRT), ta kuɓutar da wasu ’yan ƙasar Ghana biyu da aka yi garkuwa da su tare da damƙe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a kan iyakokin ƙasashen duniya. Rundunar ’yan sandan a ranar Juma’ar ta ce hakan ya biyo bayan rahoton da aka shigar gaban babban ofishin hukumar a Abuja a ranar 27 ga Afrilu, 2025, game da yin garkuwa da wani Anastasia Arthur da aka fi sani da Baidoo, ɗan ƙasar Ghana mai shekara 48. An gano shanu 25 da suka ɓace a dajin Sakkwato ’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo A wata sanarwa da jami’in hulɗa...
“Ka san idan za ka yi la’akari da sauran jihohin da suke barin jam’iyyarsu su shiga wata jam’iyya ni a tunanina tsoro ne karawa da babban jam’iyyar adawar da ke jihar ba, yanzu misali a Jihar Delta shi gwamnan jihar ya san daker ya ci zabe a 2023 sannan kuma yana da yakinin idan bai fita daga PDP ya shiga APC ba ba zai iya samun nasara a 2027 ba; to mu in ka yi la’akari da hakan a jam’iyyar mu ta PDP a Jihar Bauchi tun da ake mulki sau daya APC ta samu galba a 2015 sakamakon maja wanda ya ci ko’ina. “Duk gwamnonin PDP da aka yi a Jihar Bauchi ba wanda bai kafa tarihin yin kyawawan...
A daya bangaren kuma, sashen sufurin jiragen kasa na Sin, ya gudanar da zirga-zirga kusan miliyan 23.12, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari, kamar dai yadda alkaluman kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin suka nuna. Har ila yau, idan an kwatanta da tafiye-tafiye masu cin gajeren zango da Sinawa suka fi gudanarwa cikin kwanaki 3 na bikin sharar kaburbura na Qingming, an gudanar da zirga-zirga zuwa wurare masu nisa, tare da lekawa wuraren dake kusa da kan iyakokin kasar a ranakun hutun murnar ranar ‘yan kwadago ta duniya a bana. Wasu alkaluma na daban, daga shafin hidimar tafiye-tafiye na Qunar.com, sun nuna cewa, a ranar Alhamis, adadin wuraren da masu yawon bude ido suka ziyarta...
Hedikwatar ’yan sandan Gada da ke Jihar Sakkwato ta gano wasu shanu 25 da ake zargin an sace ko kuma sun ɓace daga hannun masu su. An gano dabbobin ne a wani dajin da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar Alhamis, bayan da hukumomin yankin suka samu labarin. ’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo Shettima zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Gabon Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an gano dabbobin ne bayan da Alhaji Muhammad Kyari ya bayar da rahoton cewa akwai shanun da suka ɓace. Sanarwar...
Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau. Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da kuma samar wa daliban fannin kimiyyar Jami’ar kayan aikin zamani da za su rika gudanar da ilimin yin gwaje-gwaje da kuma bayar da gudunmawa wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar. Kazalika, wannan nasara ta kuma nuna a zahiri irin kyakkyawan shugabancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, duba da irin kokarinta na dora Jami’ar a kan turba mai dorewa, musamman a bangaren samar...
Wasu daga cikin manoman a wadanan yankuna sun bayyana cewa, sun koma neman wasu gonakin da za su yi shuka ko dai a cikin jihar ko kuma a wasu guraren daban, musamman duba da cewa; sun dogara ne a kan wadannan sana’o’i na noma da kamun Kifi. Koda-yake dai, gwamnatin tarayya ta yi wani gini mai tsawon zurfin kimanin mita bakwai da nufin dakile ambaliyar ruwan daga Kogi, amma tuni ginin ya rushe tun daga farkon aikin. An dai gaza sake yin aikin ginin, yau kusan shekara uku zuwa hudu. Bugu da kari, tuni wasu gonaki, musamman a yankin na Muye da ake da kadada 2.6, aikin yin noma ya tsaya cak, inda kuma mazauna yankin a halin yanzu ke...
Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri. An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata. Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an gurfanar da 64 daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin Maphites, Eiye, da Aye kuma ake zarginsu da kisan gilla da aka yi kwanan nan a rikicin kungiyoyin asiri. Kayan da aka ƙwato sun hada da bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga guda mai tashi daya, da harsashi 24. ’Yan sandan sun shawarci iyaye da su kula da ayyukan ’ya’yansu kuma sun gargadi...
Wadanda ake tuhumar dai sun tabbatar wa kansu aikata laifin ba tare da kara yin wata shaida ba. Duk da haka, a kokarin janye ikirari nasu, sun yarda cewa abokai ne kuma suna zaune tare a wurin da suka aikata laifin, kuma aka kama su tare. Tawagar masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Zainab M. Jabbo, DDPP daga ma’aikatar shari’a ta Jihar Kebbi, ta gabatar da karar a gaban kotun. A halin da ake ciki, wadanda ake kara sun samu wakilcin Barista Alhassan wanda ya fara kare su, Barista Rilwan M. Mayalo wanda ya kammala da kuma Barista Faruk Dauran, Kodinetan Agaji na shari’a, wanda ya wakilce su a yayin yanke hukunci. Lauyan wanda ake kara ya kalubalanci nauyin...
Bankin Raya kasashen Afirka (AfDB) ya ware dala miliyan 650 a duk shekara tun daga 2025 zuwa 2030 domin wani shiri na musamman na habaka ci gaban tattalin arziki a Nijeriya. Bankin ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce za a samar da dala biliyan 2.95 tsawon shekara hudu a wannan shirin, inda zai samu ƙarin kimanin dala biliyan 3.21 daga sauran ƙawayen kawo ci gaba. Sanarwar ta ce shirin zai mayar da hankali kan abubuwa biyu muhimmai wadanda suka hada da kawo ci gaba ma dorewa da samar da ababen more rayuwa wadanda suka zo daidai da tsarin da ake da shi na sauyin yanayi da samar da gasa da ci gaban...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya. “Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.” Ministan...
Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan yankuna daban-daban na kasar Siriya a yammacin Juma’a. Rahotanni cikin gida sun ruwaito cewa jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare akalla 20 a wajen garuruwan Damascus, Daraa da Hama, inda suka auna wuraren sojoji da ma’ajiyar kaya. Hare-haren sun hada da wani sansanin sojojin Syria da ke kusa da kauyen Shatha da ke Hama, hedkwatar tsohuwar bataliyar sojojin Syria da ke arewacin Damascus, da kuma sansanonin soji a Dera. Fashe-fashe sun afku a Damascus da kewaye, ciki har da Harasta, inda wani farar hula ya mutu. Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa an kai hari a wasu yankuna a babban birnin kasar a karon farko. Tun bayan faduwar...
“Manchester United ce fa kowane dan wasa na hankoron taka wasa a cikinta kuma idan kuka duba kungiyar a yanzu, kamar akwai matsaloli, ciki har da sauya koci da aka yi amma duk da haka muna da masaniyar abin da ya kamata, kuma abu ne mai sauki a ganar da dan wasa” in ji Amorim, wanda ya koma United daga Sporting Lisbon. Ya kara da cewa magana ce ta karshen kaka kuma komai zai iya sauyawa. Amma dai suna so su fara komai da wuri kuma sun san yadda za su yi hakan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon hakurin da ya bayar aka rage hukuncin zuwa wasanni hudu. Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki hudu tsakani da Barcelona mai jan ragama, za ta karbi bakuncin Celta Bigo ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai bar Abuja yau zuwa Libreville, babban birnin ƙasa Gabon, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Brice Clotaire Oligui Nguema. A halin yanzu Shugaba Tinubu yana ziyara ta kwanaki biyu a Jihar Katsina. A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa, Najeriya na goyon bayan sauyin mulki na dimokuraɗiyya cikin lumana a ƙasar Gabon kuma ta sake tabbatar da ƙudirinta na inganta dimokuraɗiyya a Afirka. Oligui Nguema, wanda ya kasance shugaban riƙon ƙwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu, inda ya samu kashi 94.85% na ƙuri’un da aka kaɗa. Rashin...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai bar Abuja yau zuwa Libreville, babban birnin ƙasa Gabon, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Brice Clotaire Oligui Nguema. A halin yanzu Shugaba Tinubu yana ziyara ta kwanaki biyu a Jihar Katsina. A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa, Najeriya na goyon bayan sauyin mulki na dimokuraɗiyya cikin lumana a ƙasar Gabon kuma ta sake tabbatar da ƙudirinta na inganta dimokuraɗiyya a Afirka. Oligui Nguema, wanda ya kasance shugaban riƙon ƙwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu, inda ya samu kashi 94.85% na ƙuri’un da aka kaɗa. Rashin...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya. Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar. Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya. Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar. Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula...
A yayin da jam’iyyun hamayya ke ci gaba da shirye-shirye tunkarar babban zaɓen shekara ta 2027, a bayabayan nan an ga yadda suke haɗuwa da juna, inda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa duniya cewa, suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen mai zuwa. Ko da yake yaƙi ɗan zamba ne, abi da har yanzu bai fito fili ba zuwa yanzu shi ne dabarar da ’yan adawar ke son yin amfani da ita wajen tunkarar APC a 2027, ganin yadda Jam’iyyar ke ta ƙara karɓar masu sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu. Guguwar APC ta girgiza ’yan adawa Wasu na ganin sauyin sheƙar na iya kawo babban...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce wata jam’iyyar siyasa ta fara yakin neman zaben 2027.” Sai dai wasu lauyoyin da suka zanta da LEADERSHIP sun ce amincewa da ‘yan takara ba magana ce da za a ayyana a matsayin kamfe ba. A cewarsu, cin zarafin dokar zabe ne kowa ya fara yakinn neman zabe a yanzu. A nasa jawabin, Dr Wahab Shittu (SAN) ya danganta lamarin da rashin bin doka da...
Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara. Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis. Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma. Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kan Zaman Tattaunawan Amurka Da Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, inda suka yi musayar ra’ayi da musayar mahanga da kuma tattaunawa kan ci gaban yankin da kuma kasa da kasa. Araqchi ya kuma yi wa Guterres bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa a shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, da kuma shirye-shiryen da masarautar Oman ta yi na tsara zagaye na...
Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin Siriya da kuma yankin yammacin kasar Majiyoyin cikin gida na kasar Siriya sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojin Siriya bayan da suka yi shawagi a kan garuruwan Hama, Dar’a, Damascus, yankin kan iyakar Siriya da Lebanon da kuma gabar tekun Siriya. Wadannan su ne fitattun abubuwan da suka faru a lokacin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wa kasar Siriya hare—haren wuce gona da iri a yammacin ranar Juma’a. Rahotonni sun kara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare guda biyu kan birnin Al-Tall da ke cikin...

Falasdinawa 40 Ne suka Yi Shahada A Zirin Gaza Sakamakon Ta’addancin Sojojin Mamayar Isra’ila A Jiya Juma’a
Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin Jabaliya da al-Balad da ke arewacin zirin Gaza. Haka zalika hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 6 sannan wasu 8 suka jikkata a wani harin da jiragen saman yakin mamayar Isra’ila suka kai kan taron fararen hula da ke kusa da mahadar Abd al-Aal da ke kan titin al-Jala’a da ke arewacin birnin Gaza. A cewar majiyoyin cikin gida,...
Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa an gudanar da babban zaben 2023 ba tare da jinkirta ba, a karon farko tun 2010. Ya ce wani ci gaba kuma ya hada da samar da kayan aiki na cikin gida, yana mai cewa a karon farko tun 1999, an buga dukkan kayan zabe masu muhimmanci a Nijeriya, Farfesa Yakubu ya bayyana kalubalen da ke bukatar kulawar majalisa, da suka hada da...
Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar. Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa da kayayyakin yawon shakatawa yayin da kuma ake kara daidaita tsarin rajistar jiragen ruwa da kuma shigar da su cikin hada-hada. Wasu manazarta dai sun bayyana cewa, a sa’ilin da lokacin goshin damina ke gabatowa, ana sa ran yawon shakatawa na bakin teku da tsibirai a yankin kudu maso gabashin kasar Sin ya bunkasa, tare da kara samun balaguro ta ruwa da nufin cin...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Jihar Katsina domin ziyarar aiki ta kwana biyu, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi. Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna jihar Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgin Umaru Musa. Tinubu zai yi shekara takwas yana mulki – Afenifere Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya Bayan isarsa ne kuma ya yi wa rundunar sojin ƙasar jawabi.
Ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta shaida wa masu sukar Shugaba Bola Tinubu cewa zai yi wa’adi biyu ne a kan karagar mulki. Kungiyar ta kuma ce rashin adalci ne a hana Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ganin cewa jigo a Arewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a baya ya yi cikakken wa’adi biyu a ofishi shugaban ƙasa. Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya An kama mutane 1,611 da ƙwato motoci 21, babura 51 da aka sace a Abuja Afenifere ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren ƙungiyar ta ƙasa Kole Omololu ya sanarwa manema labarai a ranar Juma’a, wadda Daily Trust ta samu. “An bar Buhari ya cika...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa dokokin kasa da kasa ne. Har\ila yau take hakkin mutanen kasar Iran ne da kuma shigar da shakku a cikin tattaunawar da Amurka take yi da kasar. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa mutanen da kamfanoni 7 wadanda suke mu’amala da kasar Iran a kasashen UAE da Turkiya saboda sayan danyen man kasar Iran da kuma sinadaran manfetur na kasar. Har’ila...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar Jumm’a. Ya kuma kara da cewa, lalle tawagar kasar Iran a tattaunawar suna ci gaba da tattaunawa, sannan suna matukar iyawarsu don kare hakkin Iran na mallakar Fasahar Nukliya wacce take da matukar muhimmanci. Hujjatul Islam Sadiki ya kara da cewa tawagar Iran a wannan tattaunawar, suna amfani da tajruban da suke da shi a tattaunawar baya, sannan sauran...
Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya sun kama wani jami’in sojan kasar Burtania mai suna Manjor Micah Polo tare da zarginsa da shigo da makamai kasar sannan da kokarin fasa korinsu zuwa wajen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an lama manjo polo ne da makamai wadanda suka hada da MK-47 50, bindiga mai jigida 6 da kuma manya-manyan albarusai har 3000. Labarin ya kara da cewa, Nigeria’s Department of State Services (DSS), ta bada labarin cewa ta kai sumame a wani wuri a birnin Asaba na Jihar Delta inda ake fama da yanbinga masu fasa bututan mai da kuma sace mutane don karban kudaden fansa inda suka kama makaman sannan sun kama Manjo Polo a...
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo. Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna. Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci. A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34. Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika...
“Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice. “Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da...
Kalli ya da Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajao Saka Adewale, ya yi hole ababen hawa da sauran kayan laifi da rundunarsa ta kama a gaban ’yan jarida a ranar Juma’a. Hotuna: Abubakar Sadiq Isah.
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama mutane 1,611 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato motocin sata guda 21, babura 51 da kuma miyagun ƙwayoyi. Kwamishinan ’Yan sanda CP Ajoa Saka Adewale, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da motocin da aka ƙwato, baburan da sauran kayayyaki a gaban manema labarai a ranar Juma’a a Abuja. Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano da wasu 4 Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Ya ce an kama mutane 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban na satar mota. Ya kuma ce shida daga cikin motoci 21 da aka ƙwato an mayar wa...

Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana. A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
Ministan harkokin jin kai da rage radadin talauci na UNOCHA, Farfesa Nentawe Goshwe, ya sanar da yunkurin hukumar na ficewa daga Nijeriya. Ya shaida hakan ne a yayin taron kara wa juna sani kan tsarin da za a dauka a Nijeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja. A cikin wata wasika da aka yada a shafin intanet na hukumar a ranar 11 ga Afrilu, shugaban hukumar ta UNOCHA, Tom Fletcher ya ba da sanarwar yanke ayyuka sakamakon karancin kudade na kusan dala miliyan 60 a shekarar 2025. Hukumar ta ce za ta rage ayyukanta a Nijeriya, Kamaru, Kolombiya, Eritriya, Iraki, Libya, Pakistan, Turkiyya da Zimbabwe,...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu. Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin Turakin Kano; Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano; da Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano. Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru Da yake jawabi yayin bikin naɗin sarautar, Sarki Sanusi ya buƙaci sabbin masu riƙe da muƙaman da su kasance masu koyi da shugabanni da kuma ci gaba da...
Hukumar ta FIRS ta yi gargadin cewa duk bankunan da ke shiga cikin tsarin tattarawa, kudaden da ake aikawa da su, da kuma tsarin sasantawa dole ne su bi wannan umarnin ba tare da bata lokaci ba, su daina amfani da asusun da ba su izini, sannan su tabbatar da cewa ana sarrafa hada-hadar kudaden ne kawai ta tsarin da aka samar daga dandalin manhajar ‘TaxProMax’. “Muna fatan samun cikakken hadin kan ku don tabbatar da samun sauyi cikin sauki zuwa wannan tsari, ta yadda za a ba da gudummawa ga tsarin tattara haraji mai inganci,” in ji hukumar. An samar da tsarin na dandalin ‘TadPro Mad’ da nufin saukake ayyukan haraji masu muhimmanci kamar rajistan masu biyan...
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan. Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin su ba sabon kwamandan goyon baya. Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba...
Haka zalika, mutuwar mutane 33 da jikkata 54 sun faru ne sakamakon munanan ayyuka na ganganci da rashin yanayi mai kyau, yayin da yin aiki ba bisa ka’ida ba ya kai ga mutuwar 23 da jikkata shida. Masu barnatawa da lalata kayan wuta sun janyo mutuwar mutane 18 da jikkata wasu 7, sai kuma hatsarin fadowa daga sama ya janyo mutuwar mutum daya da jikkata wasu 18. A Nijeriya dai sama da shekaru ana fama da matsalar rasa rayukansu da jikkata mutane da dama daga hadurran da suka shafi na wutar lantarki kuma wannan mafi akasari na faruwa ne sakamakon amfani da kayan wuta marasa inganci ko marasa kyau, karancin amfani da kayayyakin kariya, ayyukan masu lalata kayan wuta da...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace, lura da abin da ke iya biyo bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman...
A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, Babban Sufuritendan dansanda, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa, cikin gaggawa aka yi tura jami’an ‘yansanda wanda hakan ya kai ga kamo Amusu. Wakil ya ce an kai yarinyar zuwa babban asibitin Bayara domin likita ya dubata kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi. A wani labarin kuma, rundunar ‘yansandan ta cika hannunta da wani matashi mai shekara 26 a duniya, Johnson John, mazaunin unguwar Gwallameji, bisa zarginsa da yin safarar wata budurwa ‘yar shekara 19 a duniya, Cecelia Cosmos, zuwa kasar Burkina Faso domin karuwanci. A cewar ‘yansanda, Johnson ya yaudari Cecelia ne a ranar 12 ga watan...
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16. Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bukaci ma’aikatan Nijeriya da su jajirce wajen tabbatar da adalci da walwala. Kwamared Inuwa ya bayyana cewa duk da nasarorin da gwamnatin ta samu wajen horas da ma’aikata, har yanzu akwai bukatar karin ma’aikata masu tallafawa a ma’aikatun gwamnati da na kananan hukumomi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa...

Zamfara Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 13 A Matsayin Bashin Garatuti Da Aka Gada – Mataimakin Gwamna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala biyan sama da naira biliyan 13 na garatuti, wanda ke nuna wani gagarumin mataki na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2025 da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar Mummuni, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce wajen ganin ta magance kalubalen da ma’aikata da masu ritaya ke fuskanta a jihar. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tana sane da korafin ma’aikatan da aka yi kuskuren cire su daga lissafin albashin sakamakon aikin tantance ma’aikatan da aka kammala. “Gwamnati ta riga ta kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin shugaban...
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi. Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na 11 da ya gudana a Jalingo. Shugaban SSANU ya dage cewa ya kamata a yi wa ’ya’yan kungiyar adalci, domin wadanda ba aikin koyarwa ba na daga cikin bangarori hudu da suka kafa jami’a. Sai dai ya yi gargadin cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani memba da ya sabawa ka’idojin jami’a ba. Tun da farko, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka,...
“Murkushe ‘yan adawa tare da musguna musu, musamman jam’iyyar PDP, wata alama ce karara da ke nuna cewa; zangon karshen mulki na karatowa; domin kuwa tarihi ya sha nuna hakan”, in ji Lamido a tattaunawarsa da BBC Hausa. “Ya kamata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kasance mai adalci, domin shi ne shugaban dukkanin ‘yan Nijeriya. Dole ne ya bar ‘yan adawa su yi takara a siyasance da jam’iyyar APC, idan kuma bai yi taka-tsan-tsan ba, abin zai iya komawa kansa”, in ji shi. A ranar Litinin ne, Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oborebwori da da wanda ya gaji kujerar daga wajensa, Dakta Ifeanyi Okowa da daukacin tsarin ‘yan siyasar da ke jam’iyyar PDP a jihar, suka sauya sheka...

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi. Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi. Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna. Sun bayar da misali bisa yadda samarin Yarabawa daga wasu unguwanni suka mayar da unguwar tasu filin ƙwallon ƙafa, inda suke tilasta musu rufe rumfunansu na kasuwa, har sai an gama buga ƙwalon kafin su ci gaba da sana’arsu. A kan haka ne suka yi wani zama da Shugaban Karamar Hukumar Ikoyi Obalande (LCDA) Fu’ad Lawal Atanda da shugabannin siyasa ’yan Arewa a jihar, da nufin cire...
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...

Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Matsayin Amurka Na Goyon Bayan Haramta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa Ta UN
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu. Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Damaturu yayin jawabinsa na maraba yadda ya bayyana fatansa cewa, taron zai samar da sabbin dabarun yaƙi da rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki. Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Buni ya bayyana wannan ƙungiyar a matsayin wani muhimmin dandali na haɗin gwiwa da daidaita manufofi, musamman yadda yankin ke fama da...
Cibiyar cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin, mai shirya bikin, ta ba da sanarwar cewa, baya ga wuraren baje kolin da suka shafi farfado da yankunan karkara da za a ba su rumfuna kyauta, sauran masu baje kolin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje su ma za a rage musu kudaden rumfunansu da kashi 50 cikin dari a wajen bikin Canton Fair karo na 137. Ana gudanar da bikin Canton Fair karo na 137 ne a matakai uku, daga ranar 15 ga Afrilu zuwa 5 ga Mayu. Kashi na farko da na biyu sun jawo hankulan masu sayayya fiye da 220,000 daga kasashe da yankuna 219 na duniya, inda suka kafa sabon tarihi a lokaci guda. Wannan...
Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Sun Xiaobo, ya shaida wa babban taron muhawara na 3 na kwamitin shirya taron koli na yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) na shekarar 2026 cewa, kasar Sin tana nan a kan bakanta game da kin raba ‘yancin kiyaye tsaro da na sauke nauyin da ya rataya a wuyan kasashe na tsaro, da kafa shugabanci na adalci a kan hana yaduwar makaman...
Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho. A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar. Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu. Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000...
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da rashin tabaka komai na taimaka wa jama’a a zirin Gaza. “Muna wargaza tunani da jikin yaran Gaza, ga yunwa ga yaran Gaza, idan ba mu dauki mataki ba, za mu shiga cikin abin da ke faruwa a idanunmu,” in ji shi. A gobe Juma’a ne za a cika watanni biyu na hana shigar da kayan agaji da sojojin Isra’ila suka yi a zirin Gaza baki...
Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis. Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun yammacin Yeman, lamarin da ya janyo hasarar kayayyaki na fararen hula. Dama a cewar kafar yada labaran kasar Yemen Al-Masirah, jiragen yakin Amurka sun kai hari a gundumar al-Sayl da ke lardin al-Jawf a arewacin kasar Yemen ranar Laraba. Tun a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata ne, kawencen Amurka da Birtaniya ke kai hare-hare ta sama kan kasar Yamen, domin nuna goyon...
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.” “Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya wargaza nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro a yankin. Ina mai bayar da shawarar cewa, sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.” Gwamna Zulum ya ce, “kangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki...
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kaptin Reuben Kovangiya, a hedkwatar rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso gabas ta Operation HAƊIN KAI. ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta Bayelsa NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Ya fayyace cewa fashewar ta faru ne ba sakamakon wani harin maƙiya ba, illa dai lamarin ya faru...
Ƴan ta’addan Boko Haram sun kashe masunta 18, a wani harin da suka kai a yankin Mobbar, wanda ke arewacin Jihar Borno, kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar. Harin ya faru ne a kogin Fadana-Garuwa a yankin Duji, lokacin da mayakan suka kai hari cikin ruwan, inda suka zargi masu kamun kifin da haɗin kai da ‘yan ta’addan ISWAP. A cewar wani mai kamun kifi da ya yi magana da wakilinmu, Boko Haram sun zo da yawan gaske suka yi ta kai hari kan masu kamun kifin, suna zargin su da kai rahoton maɓoyarsu ga ‘yan ta’addan ISWAP. Sun tattara su duka, suka kashe su, sannan suka yi barazanar cewa wannan hukunci ne ga wanda ke aiki tare da ISWAP. Mayaƙan...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya. Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da rayuwar ’yan Najeriya da ke dogaro a kullum kan hanyoyin ruwa na cikin kasa wajen sufuri da kasuwanci. Ya amince da dimbin karfin tattalin arzikin magudanan ruwa a kasar nan da ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon yawaitar hadurra na kwale-kwalen da ke bukatar hada kai, da kuma daukar matakai bisa dabaru don haka aka fara raba riguna 3,500 a matakin farko ga...
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa karo na 27 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano. A cewar sanarwar, majalisar ta ba da haske ga manyan ayyuka da yawa, da suka hada da manyan gyare-gyaren hanyoyi, shigar da tsarin zirga-zirga, fadada gine-ginen jama’a, da inganta wutar lantarki. Wani abin lura a cikin amincewar akwai fitar...
Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa yawan kudaden da Amurka ta tallafawa Ukraine a yakin dai ya kai dalar Amurka biliyon $175, kuma wannan ita ce hanya tilo wacce Ukraine zata iya biyan wadannan basussuka. Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjeniyar. Wannan na faruwa ne al-hali ana ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine. Wannan yarjeniyar dai ta tabbatarwa...

An Bukaci Masu Yiwa Kasa Hidima Su Yi Amfani Da Kafofin Sadarwa Na Zamani Don Inganta Hadin Kan Kasa.
Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Birgediya-Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya yi kira ga mambobin kungiyar a fadin kasar nan da su yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani cikin gaskiya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yiwa kasa rukunin A na 2025 Batch a sansanin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara. Birgediya Janar Nafiu ya kuma shawarci matasan su guji bibiyar shaharar shafukan sada zumunta na zamani, maimakon haka su mayar da hankali wajen samar da bayanai masu ma’ana da tasiri. “Bari in yi magana da ku...
Babu tabbacin ko ya rasu sakamakon rashin lafiya ko kuwa an kashe shi. An ce ‘yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, amma iyalansa sun iya haɗa Naira miliyan 11 ne kacal. Sun kuma buƙaci sabon babur da kayan abinci, duk a matsayin kuɗin fansa. Bayan da matar da ta tsere ta shaida wa jama’a abin da ya faru a ranar Litinin, sai aka yi masa sallar jana’iza a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta bakin kakakinta DSP Yazid Abubakar, ta ce har yanzu ba ta samu labarin tabbacin mutuwar limamin da iyalansa daga hukumomi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Rear Admiral Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC ya bayyana haka ne a jiya a bikin ranar “Tekun farisa’ ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen mai sauran kilomita Knots 116 na ruwa wanda yayi dai-dai da kilomita 215 / a ko wace sa’a yana da kayan aikin cilla makamai masu linzami. Kwamandan ya kara da cewa, wannan yana daga cikin shirin JMI na karfafa tsoron kasar, kuma sako ne ga makiya su san da haka, sannan sakon zaman lafiya ga makobta da abokai. An sanya ranar da turawan Portigal suka fice daga tekun farisa da mashigar ruwa ta Hurmus shekaru 1622 da suka gabata, a matsayin ranar tekunfarisa ta kasa....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cututtuka da dama suna ƙamari a Najeriya wanda a mafi yawan lokuta mutanen da da7uke da irin cututtukan ba su da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar bil’adama. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan da ke sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliyan biyu a duk shekara a Najeriya. Domin sauke shirin, latsa nan
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar. Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya da Ashrafiyyah a yankin Suwaida. Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 70.
Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman lafiya ba. Da yake Magana akan Falasdinu kuwa, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce: “Amfani da karfi domin kai wa ga sulhu” da “Diflomasiyya ta dole” akidun siyasa ne masu hatsarin gaske, yana mai kara da cewa; ta hanyar shimfida adalci ne ake kai wa ga sulhu,haka nan kuma yin furuci da hakokin da suke halartattu. Akan barazanar da wasu kasashe suke...
Masana Alkur’ani daga ƙasashe 20 ne za su shiga Gasar Karatun Alƙur’ani ta Duniya da za gudanar a karon farko a Najeriya. Gasar wadda za ta gudana a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos na Jihar Filato, sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja Tsohon Ɗan Majalissar Wakilai Mai wakiltar Mazaɓar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Filato, Honorabul Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shiryawa. A lokacin gagarumin taron kaddamar da kwamitocin shirye-shiryen gasar ta duniya, wanda Gwanayen Alƙur’ani daga faɗin kasar nan suka halarta, Honourable Alkali ya ce tuni an sanar da cibiyar bunƙasa karatun addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo ta Sakkwato kuma ta goyi bayan ƙudirin. Ya...
Ƙarar wani abin fashewa mai ƙarfi ya girgiza Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan. Tashin abin fashewan ya jefa mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA da Jami’ar Maiduguri cikin tashin hankali. Ƙarin bayani na nan tafe.
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin. Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa. “Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu. Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba. Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.

Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Najeriya Wajen Yin Watsi Da Kariyar Cinikayya Da Yin Adawa Da Danniya Da Cin Zarafi
Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban. Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane...

Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba su da rajista, musamman magungunan inganta jima’i, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan abubuwa na da matukar barazana ga kiwon lafiyar jama’a. Ya yi gargadin cewa, yin amfani da wadannan magungunan ba tare da kulawar likitoci ba zai iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, ciki har da haɗarin cututtukan zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar. Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci. Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku. Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace....
To, bayanai a sama sun nuna ra’ayi iri daya na gwamnatocin dimbin kasashe masu tasowa. Ban da haka, wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar a kasashe 38, ya nuna cewa, matakan ramuwar gayya da kasar Sin ta dauka kan kasar Amurka suna samun goyon baya tsakanin al’ummun kasashe daban daban, inda a dimbin kasashe masu tasowa da suka hada da Najeriya, da Kenya, da Masar, da Ghana, da Afirka ta Kudu, da Turkiya, matakan kasar Sin suka samu goyon baya daga mutane fiye da kaso 70% da aka gudanar da bincike kansu. Kana a kasashen yamma da suka hada da Faransa, da Jamus, da Canada,...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta. AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa. Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023. Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take. ‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar. Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar...
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400. Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023. Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza. Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke...
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi. Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Shugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu. “Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin. “Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina...
A ko da yaushe Sin tana himmatuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kira da a warware rikici ta hanyar tattaunawa. A sa’i daya kuma, aniyarta ta kiyaye ikon mulkin kasa, da hakki da moriyarta a tekun kudancin Sin ba za ta sauya ba. Ita kasar Philippines kuma za ta dandana kudarta bisa ga yadda ta aiwatar da mummunan mataki kan batun zirin tekun Taiwan, da nufin biyan bukatun Amurka game da dabarunta a yankunan tekun Indiya da na fasifik. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali. Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah. Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba. A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a Jihar Osun. “Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar. Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.