2025-05-01@13:50:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3325
«Asiwaju Bola Tinubu»:
Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai...
An tashi 3-3 tsakanin Barcelona da Inter Milan a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Sifaniya ranar Laraba. Inter Milan ce ta fara cin ƙwallo a daƙiƙa 30 da take leda ta hannun Marcus Thuram, ya zama na farko da ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a daf...
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya. Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma...
An ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har tsawon makonni biyu. Bayan haka, za a zaɓi waɗanda suka cancanta domin ganawa da su da kuma tantance su Hukumar ta shawarci duk masu sha’awar aikin da su gaggauta cike fom ɗin domin guje wa cunkoson mutane a ranar ƙarshe. Gwamna Fintiri ne, ya bayar.da...
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai...
Gwamnatin jihar Kwara ta sake jaddada kudirinta na kara bude kofa ga al’umma domin ci gaba da kuma sanya jihar ta yadda za ta yi tasiri a duniya ta hanyar sanya hannun jari mai inganci. Kwamishinan Ayyuka na Jiha Injiniya. Abdulquawiy Olododo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da ayukkan ma’aikatar...
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar...
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu tare da hadin guiwar Kyakyawar Gate Handicapped Centre Jos, sun bayar da tallafin keken guragu guda dari da talatin ga masu bukata ta musamman a Birnin Kebbi na jihar Kebbi. Kakakin Ministan, Sadiq Nura Maiyaka, ya ce Ministan ya kuduri aniyar taimakawa masu bukata...

An Bukaci Masu Yiwa Kasa Hidima Su Yi Amfani Da Kafofin Sadarwa Na Zamani Don Inganta Hadin Kan Kasa.
Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Birgediya-Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya yi kira ga mambobin kungiyar a fadin kasar nan da su yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani cikin gaskiya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa. Ya bayyana hakan ne a lokacin da...
Rear Admiral Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC ya bayyana haka ne a jiya a bikin ranar “Tekun farisa’ ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen mai sauran kilomita Knots 116 na ruwa wanda yayi dai-dai da kilomita 215 / a ko wace sa’a yana da...
Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cututtuka da dama suna ƙamari a Najeriya wanda a mafi yawan lokuta mutanen da da7uke da irin cututtukan ba su da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan da ke tabbatar...
Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar. Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya...
Kwanaki kadan bayan wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da...
Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman...
Masana Alkur’ani daga ƙasashe 20 ne za su shiga Gasar Karatun Alƙur’ani ta Duniya da za gudanar a karon farko a Najeriya. Gasar wadda za ta gudana a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos na Jihar Filato, sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja Tsohon Ɗan Majalissar Wakilai...
Ƙarar wani abin fashewa mai ƙarfi ya girgiza Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan. Tashin abin fashewan ya jefa mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA da Jami’ar Maiduguri cikin tashin hankali. Ƙarin bayani na nan tafe.
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin. Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha;...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin...
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar ta Tsakiyar Afirka saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023. Wani taro da aka yi na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro kan sauyin siyasa a Gabon “ya yi nazari kan ayyukan tare da gano cewa sun...

Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau...
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar. Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci. Aref ya bayyana hakan ne a...
To, bayanai a sama sun nuna ra’ayi iri daya na gwamnatocin dimbin kasashe masu tasowa. Ban da haka, wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar a kasashe 38, ya nuna cewa, matakan ramuwar gayya da kasar Sin ta dauka kan kasar...
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon...
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun...
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro...
Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke...
Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu. Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba...
’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar...
Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. . Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar...
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar...
A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki...
A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon...
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce...
Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu. Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa,...
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim...
Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin...
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24. Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44...
Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar,...
Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro. “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.” Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin...
Ƙungiyar ISWAP mai yaƙi da tayar da ƙayar baya a yammacin Afirka, ta ɗauki alhakin harin da ya yi ajalin mutum 26 a Jihar Borno. Ƙungiyar ta iƙirarin ɗaukar alhakin harin ne a wani saƙo da ta wallafa a shafin Telegram kamar yadda BBC ya ruwaito. Aminiya ta ruwaito yadda wani abin fashewa da ake...
Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin...