Kungiyar Kurdawan Turkiya Za Ta Ajiye Makamanta Na Yaki
Published: 12th, May 2025 GMT
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta.
Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata.
Sanarwar ta PKK ta kuma kunshi cewa;Jam’iyyun siyasa na kurdawa za su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa domin bunkasa tsarin demokradiyya da sake gina al’ummar Kurdawa.
Haka nan kuma PKK ta ce, da akwai alakar a sake Shata salon alakar Kurdawa da Turkiya.
A martanin da jam’iyyar dake Mulki a Turkiya ta fitar, ta bayyana cewa; Zartar da matakin da kungiyar ta Kurdawa ta dauka na ajiye makamanta da kuma rusa kanta, da dukkanin rassanta, zai zama bude wani sabon shafi.
Kakakin jam’iyyar, Umar Jalik ya ce; Matakanin yana da matukar muhimmanci ga Turkiya, domin hakan yana nufin kawo karshen ta’addanci,kuma gwamnati za ta sa ido ta ga aiwatar da wannan matakin, kuma za a rika sanar da shugaba Rajab Tayyib Urdugan akan zartar da matakan.
Kungiyar dai ta PKK ta yi taronta ne a arewacin Iraki a ranakun 5 da 7 ga watan Mayu, bisa gayyatar jagoranta Abdullahi Ojlan da yake tsare tsawon shekaru 26 da su ka gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025
Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025