Aminiya:
2025-08-07@16:35:51 GMT

’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato

Published: 8th, May 2025 GMT

’Yan sanda sun gano harsasai guda 500 a wata maɓoyar masu aikata laifuka da ke kusa da hanyar Bauchi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya ce an gano harsasan ne ta hanyar rahotannin sirri, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka a jihar.

Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa an gano harsasan ne bayan wani kisan kai da ya faru a yankin, inda aka kashe wani da ba a gane ko wanene ba.

“Bayan samun rahoton faruwar lamarin, nan take muka fara gudanar da bincike domin gano yanayin da ya kai ga mutuwar wanda aka kashe.

An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan sun sha ‘Kayan Mata’ ’Yan sanda sun bankaɗo masana’antar man gyaɗa na bogi a Kaduna

“A yayin gudanar da wannan binciken ne aka samu nasarar gano waɗannan harsasan. Ina so in ba ku tabbacin cewa muna ci gaba da ƙoƙarin ganowa tare da kama waɗanda suka aikata wannan laifin tare da ƙwato makamansu.”

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba su duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen kama su.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Harsasai

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Yusuf Ya Raba takardun daukar Aiki Ga Sabbin Ma’aikatan Gona Su 1 ,038

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki.

 

Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano.

 

Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su yi wa jihar hidima cikin himma da gaskiya.

 

 

Ya ce matakin ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da jihar ke yi na inganta samar da abinci da kuma habaka arzikin iyali.

 

 

Gwamna Yusuf ya bayyana daukar ma’aikata a matsayin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma wani muhimmin mataki na cimma wadannan manufofin.

 

“Yau rana ce ta sabuwar dama da cika alkawarin da muka dauka a yakin neman zabe, wadannan ayyuka ba wai kawai za su tallafa wajen samar da abinci ba, har ma da samar da kudaden shiga ga dubban iyalan Kano.”

 

Gwamnan ya bayyana cewa, duk da cewa Kano ta riga ta jagoranci kasar nan wajen yawan ma’aikata, amma duk da haka jihar na bukatar karin biyan bukatun noma na zamani.

 

 

“Muna bukatar karin kwararrun ma’aikatan da za su yi wa al’ummominsu hidima, da tallafa wa manomanmu, da kuma taimakawa wajen kawo sauyi a fannin noma.”

 

Gwamna Yusuf ya gargadi sabbin ma’aikatan da su guji cin hanci da rashawa, rashin zuwa aiki, da rashin tausayi, yana mai jaddada cewa daukar ma’aikata ba wata hanya ce ta wawure dukiyar al’umma ba.

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
  • ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti
  • ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
  • An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
  • Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore
  • Rundunar NSCDC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Hada-hadar Miyagun Kwayoyi A Kano
  • Jihar Zamfara: ‘Yan Sanda 390 Sun Sami Karin Girma
  • Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
  • Gwamna Yusuf Ya Raba takardun daukar Aiki Ga Sabbin Ma’aikatan Gona Su 1 ,038
  • Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta