2025-05-12@10:15:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4398
«karfafa hadin»:
Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu. Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar. Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar. Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi. Gwamnan ya yi addu’ar...
Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar Borno ya gabatar a zauren Majalisar, kan gobarar da ta tashi a ma’ajiyar makamai ta rundunar soji da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe a baya-bayan nan. Ɗan malisar ya ce yawan yadda ’yan ta’adda ke lalata kayan yaƙin sojoji a yanzu, ba a taɓa ganin irinsa ba a baya. Ya ƙara...
Lamido a ranar Lahadi ya ce, “Ina da yakinin cewa duk wadanda suka bar PDP za su dawo ciki har da Ganduje, domin nan ba da dadewa ba APC za ta balle ta rabu gida biyu, saboda tana rungumar mutane masu tunani daban-daban. “Na fadi haka, kuma ina sake maimaitawa: nan da watanni shida, duk wadanda suka koma APC za su dawo, kuma PDP za ta farfado da karfi don kwace mulki a 2027.” A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin ta hannun sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yi watsi da ikirarin da cewa, hakan ba zai yi wu ba. Ganduje ya ce maimakon ya koma PDP, Lamido...
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara. Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar. Wani jami’in gudanarwa na makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun shiga harabar makarantar ne ta wata ƙofa da ke bayan katangar makarantar. “Sun mamaye harabar makarantar sanye da cikakkun kayan ’yan sanda, da hula da takalman roba. Sun yi amfani da kofar da ke bayan katangar wajen shiga da kuma guduwa bayan harin,” in ji shi. Rahotanni sun nuna...
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
Kwamitin ya kuma haɗa da Honarabul Sulaiman Adamu Gummi, Kwamishinan Al’amuran Addinai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba, sai kuma Alhaji Habibu Balarabe, Babban Sakataren Hukumar Zakka, a matsayin sakatare. Yayin ƙaddamar da kwamatin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana sa ran tawagar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da walwala, aminci da jin daɗin alhazan Jihar Zamfara. “Gwamnatin Jihar Zamfara, a madadin al’ummarmu, ta ba ku kwarin gwiwa sosai wajen ganin an aiwatar da kowane fanni na aikin Hajjin 2025 cikin inganci, mutunci, da gaskiya. “Ina kira gare ku da ku ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙa da Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, da hukumomin Tarayyar da abin ya shafa, da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya gabatar bayan kammala zagaye na 4 na tattaunawar a jiya. Ministan y ace bangarorin biyu sun tattauna babututuwan da suke da zurfi a cikin matsalolin da kasashen biyu suke son su warware, na farko gamsar da Amurka kan cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran ban a tsaro bane. Da kuma maganar daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. Yace tattaunawar jiya yafi...
Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga ma zauna garin Tullaram mata da maza da yara da tsoffi duk su fice daga gidajensu. Kwanaki 105 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta fara wannan shirin na korar falasdinwa da kuma rusa gidajensu da nufin korarsu kwatakwata daga yankin. MDD ta bayyana a baya ya zuwa yanzu sun kori falasdinawa kimani 40,000 daga gidajensu, inda suka rusa su suka kuma . A wani...
Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar tsagaita budewa juna wuta. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa wannan wata dama ce kawo karshen zubar da jinni tsakanin kasashen biyu na fiye da shekaru uku da suka gabata. Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, haduwar shuwagabannin biyu zai fayyace matsayin yakin, da kuma yiyuwar dakatar da shi nan kusa. Banda haka haduwarsu zai bawa kasar Amurka damar gane matakin da zata dauka nan gaba,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɓallewar ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) bayan kwashe fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakaninta da su, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga ci gaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas. A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da ECOWAS a hukumance dangane da buƙatar ficewar tasu. Muna bayan Tinubu a Zaɓen 2027 — Patience Jonathan Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670 To sai dai bisa dokokin kungiyar, kasashen na buƙatar sanar da ita shekara guda kafin amincewa da ficewar. Bayan wa’adin da kungiyar ta deba musu...
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta sanar da cafke wata mata da ta ɓoye hodar iblis tana shirin tafiya ƙasar Iran. Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama matar ce a filin jirgin sama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas. Muna bayan Tinubu a Zaɓen 2027 — Patience Jonathan Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670 Babafemi ya ce matar ta ɓoye hodar iblis ɗin a cikin al’aurarta da cikinta da kuma a wata jaka. A cewarsa, matar mai suna Ihensekhien Miracle Obehi, wadda ta saka hijabi domin ƙoƙarin tsallake binciken jami’an tsaro, an cafke ta ne a Lahadin da...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron ministoci na dandalin Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya ko CELAC karo na 4, kuma zai gabatar da jawabi. An shirya gudanar da dandalin ne a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a ranar Talata 13 ga watan Mayun nan, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a Lahadin nan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin. Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata...
Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta nan da nan, a ba da agajin jin kai ga fararen hula da suka gaji, kuma a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su.” Fafaroman ya kuma yi kira ga “manyan kasashen duniya” da su dakatar da yaki, ya kuma yi kira da a samar da zaman lafiya “adalci” mai “dorewa” a Ukraine a wani jawabi da ya gabatar yau Lahadi a sallarsa ta farko bayan zama fafaroma. Shugaban ‘yan katolika na duniya ya kuma yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Indiya da...
Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar. Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika. A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangaré, da ministan harkokin cikin gida Janar Mohammed Tomba, da shugaban ‘yan sandan Nijar Janar Omar Chiyani. A yayin ganawar, M. Zein ya jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda a tsakanin kasashen biyu inda ya ce: “A shirye muke mu yi amfani da gogewar da ‘yan sandan Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke da ita a dukkan...
“Babu shakka cewa INEC na fuskantar matsin lamba mai tsanani, daga mambobin APC da sauran abokan huldarsu wadanda ke tsoron TNN, domin sun shirya yin magudi a zaben 2027 wajen samun nasararsu. “Amma muna kira ga INEC da ka da ta bayar da kai bori ya hau a matsayinta na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tare da kare mutuncnta ta hanyar kin yin abin da ya saba wa doka. “Muna tunatar da hukumar INEC cewa ‘yan Nijeriya suna sa ido sosai kan yadda za ta magance wannan batun na TNN, kuma duk abin da za ta yi zai tantance ko ‘yan Nijeriya za su iya dogaro da ita don shirya sahihin zabbe mai cike da adalci a 2027,”...
Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. “Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo ya amfanar.” Ya ce kafin ya zama minista, ya mallaki tashar rediyo da talbijin har ma da gidan jarida. Ministan ya buƙaci matasa da kada su yi watsi da burin su ko da ba sa ganin damar cimma buƙatar su. Ya ce shauƙin sa ne yake motsa shi wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya ta hanyar ƙarfafa fahimtar kafofin sadarwa. Idris ya kuma bayyana cewa...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa...
Wata muhawara ta kunno kai a Jihar Kano da ma wajenta bayan gwamnatin jihar ta ba da umarni a cire naira miliyan 670 daga asusun ƙananan hukumomin jihar domin saye da kuma gyaran motocin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhanmmadu Sanusi II. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kashe naira miliyan 50 daga cikin kudin wajen gyaran wasu motoci biyu na sarkin, ragowar kuma za a sayo wasu sababbin motoci huɗu. Shekara 10: Me ya sa Kofin Zakarun Turai ya gagari Barcelona? Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Ɓullar takardar da ke ɗauke da umarnin ta haifar da ce-ceku-ce, amma gwamnatin jihar ta hannun Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Waiya, ta kare matakin da cewa...
Kazalika, sanarwar ta sanar da cewa, ana bukatar kwamtin ya sanya ido wajen ganin an gabatar da kasidu da alkalan da za su yi hunci kan bayanan da za a tattauna a wajen taron da baje kolin kanana da matsakaitan sana’oi da za a yi a wajen taron tare da kuma mika kyaututtuka ga ‘yan kasuwar kasar da suka dace, a wajen taron. Acewar sanarwar, Mataimakin Shugaban Ma’aikata da ke a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne, zai shugabaci kwamtin. Sauran ‘ya’yan kwamtin sun hada da, Ministar Ma’aikatar Kasuwanci da zuba hannun jari Dakta Jumoke Oduwole; Ministan sadarwa da kere-kere da kuma tattalin arziki na fasahar zamani Dakta Bosun Tijani; Ministar yawon bude ido da kirkiren tattalin...
“Bisa ga al’adarta hukumar, INEC za ta sanar da ranar da za ta fara sabunta katunan masu zabe a lokacin da ya dace, wanda kuma za a raba cikakkun bayanai ta shafukan sada zumunta na hukuma,” in ji Oyekanmi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasa na uku da kungiyoyin suka hadu a bana shi ne wasan karshe na kofin Copa Del Rey inda nan na Barcelona ta sake samun nasarar doke Madrid da ci 3-2, a wannan karon kocin Madrid Carlo Ancelotti na fatan ganin kungiyarsa ta samu nasara akan Barcelona duba da cewar wannan ka iya zama wasan karshe da ita a matsayinsa na kocin Real Madrid. Manyan yan wasan da bazasu buga wannan wasa sakamakon raunin da suka samu sun hada da Joules Kounde da Pablo Torre a bangaren Barcelona, sai kuma Antonio Rudiger, Eduordo Camavinga da Ferlnad Mendy a bangaren Real Madrid. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe. An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona. Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara zura wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona. Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin Davide Frattesi ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Inter nasara a cikin ƙarin lokaci, bayan ƙwallon ne kuma aka kaure da ruwan sama. Barça,...
Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI. Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu. A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da su ka yi shahada sun kai 12,000 da 400. Bugu da kari wasu matan da sun kai 14 sun bace ba a gano su ba, sai kuma wasu matan masu ciki da sun kai 60,000 da suke fuskantar hatsari mai tsanani saboda rashin kula da su, da kuma rusa asibitoti da sojojin HKI su ka yi. A cikin wani tanti a Khan-Yunus da akwai wata...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta jadada cewa ko kadan sojojin kasar ba su keta tsagaita wutar yaki da Indiya ba. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta fitar ta ce; kasar tana ci gaba da aiki da tsagaita wutar yaki wacce aka sanar da ita, kuma sojojin kasar sun kai zuciya nesa, duk da cewa Indiya ce ta keta wutar yakin. Saanrwar da Pakistan ta biyo bayan zargin da Indiya ta yi wa kasar ne cewa tana keta yarjejeniyar wutar yaki bayan an cimma yarjejeniya a kan hakan. Jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Indiya Bigram Maisari ne ya bayyana hakan a wani taron manema labaru da ya gabatar a yau, sannan ya kara da cea;...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka da su ka hada na Zimbabwe da na Burkina Fasa, inda su ka tattaunawa hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashen nasu. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Burkina Faso Ibrahim Taraore sun isa birnin Moscow domin halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasara akan ‘yan Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na 2. Bugu da kari shugaban kasar ta Rasha ya kuma gana da shugaban gwamnatin kwarya-karyar Falasdinawa Mahmmud Abbas Abu Mazin,inda su ka yi musayar ra’ayi akan yadda za a kawo karshen kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya. Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa. A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
Gwamnatin Nijeriya ta ce tattaunawa ta yi nisa domin kwaso ’yan ƙasar guda 15,000 da suke gudun hijira a ƙasashen Kamaru da Nijar da Chadi da wasu ƙasashen cikin mutunci. Kwamishinan hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Nijeriya, Alhaji Tijjani Ahmed ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Abuja. Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Ya ce akwai aƙalla ’yan Nijeriya miliyan shida da ke zaman gudun hijira a cikin ƙasar, sannan akwai wasu dubbai da suke zaune a wasu ƙasashen na duniya. “Akwai ’yan Nijeriya 15,000 da suke so su dawo da kansu; haka kuma muna da ’yan ƙasashen waje aƙalla...
Sai dai a cikin takardar murabus din, Edema ya bayyana rashin tsarin jam’iyyar a matsayin dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai kaga mutum daga ya samu wata yar dama to do yake ace ya samu wata hanyar wulakanta wannan wanda yayi masa rana kokuma ya wuce shi a matsayi ko wani abin Duniya ba tareda la’akari da cewar wannna wanda ya koya maka to ya fika sanin komai a wannan harkar musamman ma a nan masana’antar Kannywood. Don haka kamata ya yi ce mutane sun fahimci cewar babu ta yadda za a yi ka ci gaba matukar ka na da wata niyyar cin amanar wanda ya taimake ka ka kai wani matsayi na rayuwa, ni yanzu a matsayina na Ayatullahi Tage na yi biyayya ga maigidana Alhaji Tage wanda ya nuna mani hanya, ya rike ni kamar dan da ya...
Miliyoyin mutane, mafi yawansu mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) sun taru a hubbaren limami na 8 daga limamai masu tsarki wasiyan manzon All..(s)..12. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, miliyoyin mutanen kasar Iran da kuma wasu bakin da suka zo daga kasashen waje sun yi cincirindo a hubbaren Imam Aliyu dan Musa Al-rida(a) limamai na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Alll..(s) da ke birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran don tunawa da ranar haihuwarsa. An kawata hubbaren na sa da fulawowi wasu na lantarki sannan malamai suna bayyana matsayinsa a wajen raya addinin kakakinsa manzon All..(s), musamman a lokacinda sarki Mamun daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya tilasta masa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana fuska biyu na kasashen yamma, dangane da shirin magakamashin nukliya na kasarsa, da kuma yadda basa magana kan makaman nukliya wanda HKI take da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar, a birnin Doha na kasar Qatar a inda yake halattan taron JMI da kasashen larabawa a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa, wannan rashin adalci ne a fili sannan nuna fuska biyu, Iran wacce babu tabbas kan shirinta na makamashin nukliya na soje ne, an cika duniya da cewa tana son ta mallaki makaman nukliya amma ga HKI wacce aka tabbatar da cewa tana da makaman na nukliya, babu...
Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin JMI dake birnin NewYork ya kara da cewa, abin mamaki da kamfanin dilancin laraban reuters, shi ne ba wannan ne karo na farko yake yada labaran karya a duniya wanda wai yake samu daga wasu wadanda basa son a bayyana sunansu. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa bata bayan wani bangare daga cikin bangarori biyu da suke fafatawa a kasar Ukraine. Don haka bata...
Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi. A wani bangare Aragchi ya fadawa...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco. Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu tana bunkasa inda a shekarar da ta gabata ya kai dalar Amurka biliyon $9. Har’ila yau kowa ya san yadda kasar Masar ta zama sansanin sojojin kasar Rasha a lokacin yakin duniya na biyu. Da kuma yadda kasar ta taimakawa kasar Rasha a yakin da ta fafata da sojojin Nazi na kasar Jamus. Har’ila yau shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya godewa shugaban kasar...
Amma sha’awar taka leda a Real tare da babban abokinsa kuma abokin wasansa na Ingila Jude Bellingham ya sa shi canza ra’ayi, yunkurin da Alexander-Arnold ya yi zuwa Real Madrid ya raba kan magoya bayan Liverpool, inda wasu ke ganin ya kamata ya zauna ya zama gwarzon kulob daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin. Taron wanda ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda suka tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin. An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da Filato da Yobe da Jigawa da Kogi da Adamawa da kuma Zamfara na cikin waɗanda suka halarci taron. A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed...
A jawabinsa a wajen tarbar Jirgin Ruwan na na yankin Asia Jim Stewart, ya bayyana jin dadinsa ga Hukumar ta NPA, bisa goyon bayan da ta bayar wajen samar da kyakyawan yanayi a babban wajen da Jiragen Runwan na Tashar Onne suke tsayawa. “Muna da kyakaywar dangantakar gudanar da ayyuka da Manajan Tashar ta Onne Mista Abdulrahmon Hussain da kuma sauran ‘yan tawagar Hukumar ta NPA, “Inji Stewart. Ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancin shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho, wanda kuma kashin bayan duk wata nasara da muka zamu. “Sake farfado da babban wajen tsayawar Jiragen Ruwan a Tashar Onne, hakan ya kara mana kwarin Guiwa”. A cewar Stewart. Kazalika, Stewart ya yi kira ga Gwamnatin...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
Sarkin Katsina Muhammadu Dikko Allah ya yi ma shi rasuwa,a shekarar 1944 da ba’a dade da shigarta ba,bayan ya sanu damuwa daga rashin lafiya, wannan shi yasa aka fara fafutukar neman wanda zai gaje shi.Ta bnagare daya akwai gidan Sarautar Dallazawa a karkashin jagorancin Yarima, wanda shi dan Sarkin Katsina Abubakar ne wanda yake ganin Sarautar Katsina wata dama ce ta shi,sai ta daya bangaren kuma akwai ‘ya’yan marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko,wadanda su ma suna da matukar karfi,wadanda daga cikinsu ma da akwai wata ‘yar jayayya kan wanda zai gaji mahaifin nasu. Watan Maris 1944,sai masu zaben Sarki suka zabi karami daga cikin ‘ya’yan Dikko da ake kira da suna Usman Nagogo,wanda shi ne Turawan mulkin mallaka na Ingila...
Ya kara da cewa bukatar kasa da kasa game da karfin ma’adinai na Kaduna yana karuwa, tare da masu saka hannun jari da yawa wadanda suke bincike kan yadda za su yi amfani da wadannan albarkatun da ba a taba amfani da su ba. “Baya ga wannan, muna da ma’adanan karfe. Kamfanin ‘African Mines’ ya riga ya zo Kaduna don hakar wannan albarkatun, wanda ya nuna a fili cewa Kaduna tana da ma’adanan karfe da za a iya gudanar da kasuwancinsu,” in ji shi. Bello ya jaddada cewa tsarin kamfanin yana nuna jajircewa don kokarin killace iyakokin ma’adinai da kuma habaka su. Ya ce tun lokacin da aka kafa kamfanin, hukumar gudanarwaar kamfanin ta ba da fifiko ga ayyukan da...
Kasashen Indiya da Pakistan sun tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan shafe kwanaki suna yi wa juna luguden wuta da makaman atilare. Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da cewa ƙasashen biyu maƙwabta sun amince su cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta nan take bayan shafe dare guda ana tattaunawa. Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina “Bayan doguwar tattaunawa da Amurka ta yi na a cikin dare, ina farin cikin sanar da cewa Indiya da Pakistan sun amince da tsagaita wuta cikin gaggawa. “Ina taya ƙasashen biyu murna a kan amfani da hankalinsu da kuma basira,” kamar yadda Trump ɗin ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Asabar ne kasashen Sin da Amurka suka fara wani babban taron tattalin arziki da cinikayya na matakin koli a birnin Geneva na kasar Switzerland. A matsayin shugaban tawagar kasar Sin kan harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin, He Lifeng, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar, ya halarci taron tare da jagoran tawagar Amurka, babban sakataren baitul-malin kasar, Scott Bessent. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata” ya bayyana cewa: A yau duniya ta shaida yadda ake daukar manufofin son zuciya kan wasu kasashe. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa daga cikin wadannan manufofi na son zuciya da ake aiwatarwa a yau akwai kokarin mantar da al’umma batun da suka shafi Falasdinawa, yana mai cewa: Kada al’ummar musulmi su kuskura wannan kyale hakan ya faru, domin ko dan...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna. A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Kai Hari Kan Ofishin Jakadancin Kasarsa A Kasar Sweden
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka kai harin. A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da ministar harkokin wajen Sweden Maria Malmer Stenergård, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma na ofishin jakadancin. A yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin...
Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, wanda Amurka ta shiga tsakani wajen kulla ta. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, da aka samu, inda ya yaba da amfani da hankali da basirar da kasashen biyu suka nuna wajen daukar wannan mataki. Ya kuma jaddada cewa, dogon tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu ya haifar da wannan yarjejeniya, wanda ke nuna muradin bangarorin biyu na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan sanarwar...
Wani babban hafsan sojin Yemen ya bayyana dabarun Yemen da suka tilastawa Amurka dakatar da kai hare-hare kan kasar Yemen Kwararren kan harkar sojin kasar Yemen kuma kwararre kan harkar yaki Birgediya Janar Aziz Rashid ya jaddada bunkasar karfin sojan kasar Yemen, yana mai nuni da dalilan da suka sanya aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Yemen. A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, kwararren sojan kasar Yemen kuma kwararre kan harkar dabarun yaki birgediya Janar Aziz Rashid ya tabbatar da cewa: Kasar Yemen ta samu wani matsayi mai inganci a arangamar da take yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta yi nasarar sauya ma’aunin karfin iko da kuma karuwar matakan soji...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki. Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke yi na daƙile ayyukan ’yan ta-da ƙayar baya. “Na bayar da umarnin haramta sayar da da man...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jiya Juma’a, a birnin Moscow na kasar Rasha, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasashe daban daban, wadanda suka hada da shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, da mai jagorantar gwamnatin kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Cuba, kana shugaban kasar Cuba, Miguel Diaz-Canel Bermudez, da shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro Moros, gami da firaministan kasar Slovak, Robert Fico. Bayan haka, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi, shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, zai ziyarci kasar Sin, tsakanin ranar 10 zuwa 14, ga watan Mayun da muke ciki. (Bello Wang) Daga kanmu, magana...
Gidauniyar attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ta yi wa masu fama da cutar gwaiwa da taruwar ruwa a wasu sassan jiki fiye da 12,300 tiyata kyauta. Da yake yi wa wakilin bayani, Malam Husaaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar ne ya tabbatar da hakan a Katsina, a lokacin ƙaddamar da aikin kashi na biyu. Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso Kabir ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da aikin tiyatar da bayar da magani kyauta a duk bayan watanni uku tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2013. Ya ƙara da cewa, “majinyata masu rauni...
Hukumar Ƙwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce za ta faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata daga tawagogi 32 zuwa 48. FIFA ta ce sabon tsarin zai fara aiki ne daga gasar 2031, wadda Amurka ce kawai ke neman ɗaukar nauyinta. Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya Tuni dai FIFA ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta Maza da za a yi nan gaba, zuwa wannan adadi. FIFA ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yadda gasar ke ci gaba da samun karɓuwa da farin jini tsakanin masoya ƙwallon ƙafa a duniya. Masu suka sun zargi hukumar da fifita kuɗin da za ta samau...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad Fu’ad dulaibh, da matarsa Hindu, da ‘ya’yansu Ahmad, Hamzah, da Abdulazizi. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren ta jirgin sama maras matuki a unguwar “Tuffah” dake birnin Gaza, da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Su ma jiragen ruwan HKI sun kai wasu hare-haren munanan a garin Rafah da ya yi sanadiyyar shahadar Muhammad Sa’id al-Burudawil. A tsakiyar birnin Gaza, ma dai...
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fada a yau Asabar cewa: Ma’aikata ne jari mafi muhimmanci na samun zaman lafiya a cikin al’umma da kuma cimma manufar sunan da aka bai wa wannan shekarar na : “Zuba Hannun Jari Domin Yin Kere-Kere.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da ma’aikata da su ka fito daga sassan Iran, ya yi ishara da sake bude kamfanoni da dama a zamanin shugabancin Shahid Ra’isi, alhali gabaninsa an rufe su,tare da bayyana hakan da cewa daya ne daga cikin ayyukan da Shahidin ya aiwatar. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana ma’aikatar da cewa, su nekashin bayan kowace al’umma, yana kuma mai yin addu’ar Allah ya ba su...
Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar da su yi taro. Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya. Ita dai Majalisar kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.An kafa wannan majalisar ne dai a 2000. Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da...
Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS. Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake. Sa Wa Shanu 110 guba Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren...

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda
Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya. Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50 da kafuwa. Kasan an kafa kungiyar ne ranar 28 ga watan Mayu,1975 bana kungiyar za ta cika shekaru 50. To kasancewa shekaru 50 sun wuce wasa na ga cewa, kungiyar ta cancanci a yaba mata, kuma a kara matakaimi da azama. Kuma za ka yarda da ni idan na ce ma cikin wadannan shekaru 50, Kungiyar ta taka muhimmiyyar rawa ta a zo a gani...
A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin. Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu. Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa. Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna...
Duba da yadda yanayin muhalli yake, zai ba da dama wajen rage fuskantar sauyin yanayi tare da inganta kiwon lafiyarsu, abincinsu da kuma ingancin ruwan shansu. 2- Fashin Baki Kan Abin Da Zai Iya Afkuwa A Wajen Kiwon Su: Ga wanda zai fara wannan kiwo, ana so ya zabi wajen da ya dace da kuma tsarin da zai yi, don guje wa abin da zai iya afkuwa a bangaren sauyin yanayi mai tsanani. 3- Raba Kafa A Yayin Kiwon: Masu iya magana na cewa, ‘Ba a zuba kwai a cikin kwando daya’, wato ma’ana, ana so ka raba kafa ta hanyar yin wata dabara a kan kayanka, don kaucewa yin asara. Kazalika, raba kafa na taimakawa wajen kara bunkasa kiwo...
Bugu da kari, wasu kwararru a fannin aikin noma, su ma tuni suka gargadi manoman kan kaucewa yin shuka da wuri, inda suka shawarce su da su tabbatar da sun kiyaye da hasashen na hukumar ta NiMet, domin kaucewa tabka asara da kuma yin da-na-sani. Lokacin Da Ya Fi Dacewa Manona Su Yi Shuka: Wata kungiya mai bayar da agajin gaggawa, (Christian Aids) tare da hadaka da wasu abokan hudda, sun samar da wata taswira da ke kunshe da lokacin da ya fi dacewa manoman da ke jihohin kasar 36 ciki har da babban birnin tarayayyar Abuja, su yi shuka. Taswirar wadda ta kasance mai saukin amfanai, sun tsara matakan da suka kamata manoman su bi, na kiyaye lokacin yin...

Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba. Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba...
Gwamnatin kasar Pakisatan ta basa sanarwan kai hare-haren maida martani kan kasar Indiya, inda tayi amfani da makamai masu linzami wadanda suka fada kan rumbun ajiyar makaman kasar ta Indiya da wani filin tashin jiragen. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar Nacewa daga wadannan wurare biyu ne makaman kasar Indiya suka tashi suka kuma yi sanadiyyar kashe mutane fararen hula a cikin kasar Pakisatan a makon da ya gabata. Labarin ya kara da cewa sojojin Pakisatan sun bawa wannan farmakin maida martani suna [Bunyanun Marsus) inda suka dauki aron Kalmar daga wata ayar al-kur’ani mai girma. Hare-haren maida martanin sun auku ne a safiyar yau Asabar, don haka har yanzun bamu ta bakin kasar...
Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen da sunan tilastawa kasar dakatar da kaiwa jiragen ruwan Amurka da kuma na HKI wucewa da tekun Red sea don tallafawa mutanen Gaza, wadanda HKI take masu kissan kare dangi da kuma hana shigar abinda zuwa cikin gaza don kashesu da yunwa. A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fito ya fadawa duniya kan cewa, ya cimma yarjeniya da...
Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata. Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran ta nakalto kakakin Jami’ar a jiya Jumma’a na cewa a ranar Laraba yansandan NewYork sun kama talibai kimani 80 inda suke tsare da su, a halin yanzu suke kuma ci gaba da gudanar da bincike a kansu. Amma duk da haka an dakatar da karatun wasu daga cikinsu zuwa wani lokaci nan gaba. Labarin ya kara da cewa akwai wasu karin mutane 33 wadanda Jami’ar...
Kamfanin man fetur da gas na kasar Iran zai fara aikin nema da hakar man fetur a tekun Caspian da ke arewacin kasar, wanda mataki ne na ci gaba ga kamfanin musamman a halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an kamfanin na cewa tuni sun kai kayakin aiki zuwa wuraren da suke zata akwai danyen man fetur a cikin tekun, sannan a shirye suke su fara aiki don hakar man daga yanzun. Ba wannan ne karon farko wanda gwamnatin kasar Iran take hakar danyen man fetur a cikin tekun Caspian ba, saboda a shekara ta 1997 ne ta dakatar da hakar mai daga gabar tekun, sannan ta dakatar da hakar man a tsakiyar...
Janar Hussain Salami babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kaddamar da sabon sansanin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na karkashin kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Salami yana cewa, wadannan jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, suna iya daukar hotunan jiragen yakin Amurka wadanda suka kasance sansanin jiragen saman yaki na kasar wadanda suke cikin tekuna, don amfani da hotunan saboda kai wa sansanin hare hare. Salami yace gabatar da wannan sansanin gargadi ne ga mjakiya, sannan duk wata kasa a yankin wacce ta bar Amurka ta yi amfani da dandanin sojojinta da ke kasar don kaiwa kasar Iran hare0hare kasar ma ta zama filin daga....
Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni. A gun gudanar da ayyukan jinyar kyauta, kwararrun likitocin kasar Sin daga bangaren aikin tiyata na gama-gari, da aikin kasusuwa, da aikin kula da mata da na sauran sassa sun gudanar da gwaje-gwajen lafiya da gano cututtuka da kuma ba da jinya cikin tsari a wurin bayar da jinya na wucin gadi da rarraba magunguna kyauta, tare da ba da cikakken jagora kan yadda...
Babban bankin kasar Sin zai aiwatar da jerin matakai da za su inganta hidimomin hada hadar kudi da nufin habaka yin amfani da kudi ga masu sayayya, a cewar wani rahoto da babban bankin kasar (PBOC) ya fitar a yau Juma’a. Bisa ga rahoton manufofin hada hadar kudi na rubu’in farko na shekarar 2025 na PBOC, bankin zai fi mai da hankali wajen aiwatar da manufar hada hadar kudi mai sassauci. A lokaci guda kuma, zai yi amfani da tsarin bayar da lamuni da sarrafa takardun lamuni, wanda za a yi amfani da shi wajen jagorantar cibiyoyin hada hadar kudi don kyautata ba da goyon baya ga masu amfani da kudi a manyan sassa, kamar yawon shakatawa, abinci, nishadi...

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani
Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin kulla takardar hada kai da aka shirya a fadar Kremlin a jiya Alhamis. A shaidar shugabannin kasashen biyu, shugaban CMG Shen Haixiong ya wakilci hukumar fina-finai ta kasar Sin da ministar hukumar al’adu ta Rasha Olga Borisovna Lyubimova sun kulla hannu da yi musanyar takardar “Shirin samar da fina-finai bisa hadin gwiwar hukumar fina-finai ta kasar Sin da hukumar al’adu ta Rasha kafin shekarar 2030”. Shirin ya taka rawar gani wajen gaggauta hadin gwiwar kasashen biyu ta fuksar samar da fina-finai tare, da shigowar fina-finan junansu da gabatar da bukukuwan fina-finai tsakaninsu, ta yadda za a kara tuntubar al’adu da koyi da juna a bangaren...
An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin 2025. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da tashin maniyattan a filin jirgin Sam Mbakwe da ke birnin Owerri na Jihar Imo. ’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025 Sahun farko na maniyyata 315 waɗanda suka kama hanyar ƙasa mai tsarki sun fito ne daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa inda jirgin Air Peace ne ya kwashe su. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya, Farfesa Abdullahi Usman da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III da sauran manyan jami’an gwamnatin Nijeriya ne suka tarbi Kashim Shettima...
Dakarun Yeman sun sanar da sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila na Ben Gurion da ke kusa da birnin Tel Aviv da makami mai linzami mai linzami. Bayanai sun ce ko wannan karo tsarin garkuwa daga hare haren sama na Amurka samfarin THAAD ya gaza kakkabo harin. Sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ta bayyana cewa, an kai harin ne yau Juma’a. Kakakin rundunar ‘yan Houthi Yahya Saree ya ce, sun yi amfani da makami mai linzami mai gudun tsiya,” Isra’ila dai ta sha alwashin mayar da martani mai karfi kan harin. Kasar Yemen dai na mai kai hari kan kaddarorin Isra’ila domin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza...
A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta. “Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.” Bayanin hakan ya...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, ta yi kakkausar suka kan rufe makarantu guda 6 na MDD da Isra’ila ta yi a yammacin gabar kogin Jordan, tare da bayyana hakan a matsayin keta dokokin kasa da kasa ranar Alhamis 8 ga watan Mayu, Hamas ta bayyana cewa harin da aka kai kan makarantun hukumar agaji ta MDD UNRWA da ke birnin Quds da aka mamaye, da kuma rufe su da aka yi bayan korar dalibai da malamai da aka yi, ya zama harin kai tsaye ga daukacin tsarin MDD da cibiyoyinta. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, irin wadannan matakai na aikata laifuka wani bangare ne na yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi da wanzuwar Falasdinu da kuma asalinsu. Don...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar. Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu kasar Oman ta tattauna da bangaren waccen bangaren. Babban mai shiga tsakani na Iran ya jaddada cewa tattaunawar Tehran da Washington tana ci gaba. Iran da AMurka dai sun yi jerin tattaunawa har guda uku a Oman, sannan a Italiya sai kuma a Oman. Dukkan bangarorin dai sun bayyana tattaunar da mai kyakyawan fata.
Kasashen NIjar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu a bangarori da dama. Bangarorin sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a yayin ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin cikin gida da tsaron jama’a da wata tawagar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar tsaron kasa Birgediya Janar Ahmad Rezaei RADAN. A yayin wannan zama Nijar da Iran sun amince da kafa kwamitin kwararru domin yin musayar ra’ayi lokaci-lokaci da karfafa hadin gwiwa. Nijar da Iran, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a fagen yaki da ta’addanci, da manyan laifuffukan kasa da kasa, tsaron iyakoki, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba.
Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan...
An kama mutane 78 tare da kwace tulin miyagun kwayoyi da makamai da kayan sata a wani samame da ’yan sanda suka kai kwanan nan domin ayyukan laifi a Jihar Kano. A yayin samamen, an kama gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022. Daga cikin sauran wadanda aka kama har da wani da ake zargin dan fashi da makami ne da bindigogi biyu da harsasai. Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya sanar a taron ’yan jarida da ya gudana a hedikwatar rudunar da ke Bompai a ranar Juma’a cewa aikin kamen ya yi daidai da umarnin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa kan a aiwatar da ingantattun matakai domin...
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa. Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar da aka yi watsi da ita Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitoci Mista Alausa ya bayyana cewa wannan matakai ya samu ne sakamako nazari da aka yi wajen sanya ƙaƙƙarfan jari a manyan makarantun ƙasar. Ministan ya ce daga yanzu babu batun bai wa ’yan ƙasar kuɗaɗen ƙaro ilimi daga ƙetare, saboda yanayi da ake ciki da ma kyawun tsari da...
Wasu kananan yara biyar sun mutu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a harabar wani gida a yankin Agyaragu da ke Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa. Yaran sun rasu ne a sakamakon daukewar nunfashinsu a cikin motar, lamarin da ya jefa mazauna yakin yankin, wadanda yawancinsu manoman ne, daga kabilu daban-daban, cikin alhini. An gano gawarwakinsu ne da misalin karfe 1 na rana a cikin motar bayan mutanen yankin sun shafe tsawon lokaci ana neman su. Misis Ifeoma Nnaji, wacce ta rasa ’ya’yanta biyu, Nmesoma da Chidima, ta bayyana yadda aka gano gawarwakin ta ce, “Mun duba ko’ina… Daga karshe, wani ya ba da shawarar mu duba motar da aka yi watsi da ita,...
Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57 Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya...
Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.27, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 314, yayin da adadin hajojin da kasar ta shigo da su daga waje ya karu da kaso 0.8 bisa dari a shekara zuwa kimanin yuan tiriliyan 1.57. Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. Wani kwararre a kan sha’anin tsaro, Jackson Lekan, ya ce bayanan Manjo-Janar Kanye ya nuna laifi da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin...
Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa. Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa, wata kuma ta mutu sakamakon dauke wuta a yayin da ake tsada da yi wa mata tiyata, a Asibitin Jummai Babangida Aliyu, da ke jihar Neja. ’Yan uwa sun shaida wa wakilinmu cewa an shafe sama da kwana uku a jere babu wutar lantarki a asibitin gwamnatin, a yayin da rashin wuta da yanayi na tsananin zafi ya tilasta wa ’yan uwan majinyata amfani da...
Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa. Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa, wata kuma ta mutu sakamakon dauke wuta a yayin da ake tsada da yi wa mata tiyata, a Asibitin Jummai Babangida Aliyu, da ke jihar Neja. ’Yan uwa sun shaida wa wakilinmu cewa an shafe sama da kwana uku a jere babu wutar lantarki a asibitin gwamnatin, a yayin da rashin wuta da yanayi na tsananin zafi ya tilasta wa ’yan uwan majinyata amfani da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. An kashe mutane da yawa tare da raba wasu dubbai da gidajensu a jihohin Filato da Benue a sakamakon hare-hare da makiyaya ɗauke da...