’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa
Published: 9th, May 2025 GMT
Wasu daliban jami’a da ke shirin tafiyar aikin yi wa kasa hidima NYSC sun rasu a wani harin da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka kai musu a yankin Gbarabtoru-Ekpetiama, Karamar Hukumar Yenagoa.
Matasan biyu da suka kammala karatunsu a Jami’ar Niger Delta (NDU), Amassomma, sun rasu ne bayan da gungun wasu mutane da ke wake-waken kungiyar asiri a cikin wata mota suka kai musu hari da adduna.
Kwamandan Kungiyar ‘Yan Banga (VGN) na Jihar Bayelsa,Tolummbofa Akpoebibo Jonathan ya ce, daya daga cikin samarin ya yi kokarin tserewa, amma maharan suka bi shi suka kama shi suka sassare shi.
Ya bayyana cewa da misalin karfe 11:00 na daren ranar Alhamis ne, abin ya faru kuma matasan biyu biyu sun mutu ne sakamakon raunukan da suka samu.
Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare An kama mutum 78 da makamai da kwayoyi a Kano JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Musa Mohammed, ya bayyana cewa an kama wasu da ake zargi kuma Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) na gudanar da bincike.
An kuma tsare direban motar da ake zargin maharan sun yi amfani da ita.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kugiyar asiri
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.