2025-05-01@17:13:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3999

«Barcelona ta»:

    Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho.   A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar.   Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu.   Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000...
    Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki. An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin. Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad Ali Dehghan Dehnavi, shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta Iran; da Sahabi Oumarou, ministan mai na Nijar, ne suka halarci taron. Da yake jawabi a wajen taron, Atabak ya ce, bayan shafe shekaru 13 da aka shafe ana aikin kwamitin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar,  “Muna fatan inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashenmu biyu ta hanyar wannan takardar hadin gwiwa.” Dehghan Dehnavi ya jaddada cewa,...
    Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da rashin tabaka komai na taimaka wa jama’a a zirin Gaza. “Muna wargaza tunani da jikin yaran Gaza, ga yunwa ga yaran Gaza, idan ba mu dauki mataki ba, za mu shiga cikin abin da ke faruwa a idanunmu,” in ji shi. A gobe Juma’a ne za a cika watanni biyu na hana shigar da kayan agaji da sojojin Isra’ila suka yi a zirin Gaza baki...
    Iran ta sanar da cewa an dage tattauanwa ta karo na hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington a ranar Asabar mai zuwa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba tsakanin Iran da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Rome na kasar Italiya. Esmail Baghai ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne bisa bukatar ministan harkokin wajen kasar Oman, kuma Za a sanar da sabon lokaci nan gaba. Baghaei ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da hanyar diflomasiyya wajen kare muradun al’ummar...
    Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis. Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun yammacin Yeman, lamarin da ya janyo hasarar kayayyaki na fararen hula. Dama a cewar kafar yada labaran kasar Yemen Al-Masirah, jiragen yakin Amurka sun kai hari a gundumar al-Sayl da ke lardin al-Jawf a arewacin kasar Yemen ranar Laraba. Tun a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata ne, kawencen Amurka da Birtaniya ke kai hare-hare ta sama kan kasar Yamen, domin nuna goyon...
    Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.”   “Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya wargaza nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro a yankin. Ina mai bayar da shawarar cewa, sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.”   Gwamna Zulum ya ce, “kangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki...
    Iran ta yi tir da Allah-wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta lafta mata. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce matakin wata babbar alama ce da ke nuna cewa Washington ba ta da kyakyawar niyya, hasali ba abar yarda ce ba. Sanarwar ta bayyana karara cewa Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen matsin lamba na Amurka kuma ta dage kan yin shawarwari a karkashin sharudda guda. Iran na cewa takunkuman da Amurka ke bayyanawa da matsin lamba mafi girma, tun zuwa gwamnatin Trump, ba zasu tankwaso Tehran ba game da hakokkinta. Kalaman na zuwa ne jim kadan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya sanar da kakaba...
    Elevator shoes, often whispered about or discreetly employed, are footwear designed to provide the wearer with increased height. They achieve this through cleverly concealed built-up insoles and thicker outsoles, seamlessly integrating an extra lift into the shoe’s construction. While the concept might seem simple, the impact of elevator shoes can be multifaceted, affecting not only physical stature but also confidence and overall presence. This article delves into the mechanics and effects of elevator shoes, addresses the common question of detectability, explores the range of height increase they offer, and definitively confirms their suitability for men. The Mechanics of the Lift: What Elevator Shoes Do At their core, elevator shoes are engineered to elevate the wearer’s heel and often the ball...
    A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kaptin Reuben Kovangiya, a hedkwatar rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso gabas ta Operation HAƊIN KAI. ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta Bayelsa NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Ya fayyace cewa fashewar ta faru ne ba sakamakon wani harin maƙiya ba, illa dai lamarin ya faru...
    Ƴan ta’addan Boko Haram sun kashe masunta 18, a wani harin da suka kai a yankin Mobbar, wanda ke arewacin Jihar Borno, kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar. Harin ya faru ne a kogin Fadana-Garuwa a yankin Duji, lokacin da mayakan suka kai hari cikin ruwan, inda suka zargi masu kamun kifin da haɗin kai da ‘yan ta’addan ISWAP. A cewar wani mai kamun kifi da ya yi magana da wakilinmu, Boko Haram sun zo da yawan gaske suka yi ta kai hari kan masu kamun kifin, suna zargin su da kai rahoton maɓoyarsu ga ‘yan ta’addan ISWAP. Sun tattara su duka, suka kashe su, sannan suka yi barazanar cewa wannan hukunci ne ga wanda ke aiki tare da ISWAP. Mayaƙan...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko  Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai taɓa kin halartar bikin Ranar Ma’aikata ba tun bayan da ya zama mataimakin gwamna. Sabanin shekarar da ta gabata, Kwamred Garba bai bayyana a wannan shekarar ba duk da cewa Gwamna Bago da Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas, Sani Musa, sun halarta, lamarin da ya ƙara zafafa zargin rikici tsakaninsa da gwamnan. Wasu majiyoyi sun ce yana wajen gari, yayin da wasu ke...
    An tashi 3-3 tsakanin Barcelona da Inter Milan a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Sifaniya ranar Laraba. Inter Milan ce ta fara cin ƙwallo a daƙiƙa 30 da take leda ta hannun Marcus Thuram, ya zama na farko da ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a daf da karshe a Champions League. Daga nan Inter ta kara na biyu ta hannun Denzel Dumfries, wanda ya zama na farko daga Netherlands da ya ci ƙwallo ya kuma bayar aka zura a raga a daf da karshe a Champions League, tun bayan Wesley Sneijder a Inter a karawa da Barcelona. Dumfries shi ne ya bai wa Thuram ƙwallon farko da Inter Milan ta zura...
    ‘Yar takarar shugaban ƙasar Amurka da ta sha kaye a zaɓen da aka yi, ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, Kamala Harris ta zargi shugaba Donald Trump da tunzura abin da ta kira taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar. Ms Harris ta kuma zargi Mr Trump da jefa ƙasar cikin ruɗani da salon mulkin da ke jefa tsoro a zukatan jama’a. Ta ce abin da suka kasa ganewa shi ne, tsoratarwa ba ita ce kaɗai hanyar magance matsala ba, ƙwarin gwiwa ake buƙata. Tattalin arziƙin Amurka ya samu koma baya a rububin farko na wannan shekarar, idan aka kwatanta da bunƙasar shi a shekaru hudu na mulkin shugaba Joe Biden.
    Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya.   Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da rayuwar ’yan Najeriya da ke dogaro a kullum kan hanyoyin ruwa na cikin kasa wajen sufuri da kasuwanci.   Ya amince da dimbin karfin tattalin arzikin magudanan ruwa a kasar nan da ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon yawaitar hadurra na kwale-kwalen da ke bukatar hada kai, da kuma daukar matakai bisa dabaru don haka aka fara raba riguna 3,500 a matakin farko ga...
    Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa karo na 27 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.   A cewar sanarwar, majalisar ta ba da haske ga manyan ayyuka da yawa, da suka hada da manyan gyare-gyaren hanyoyi, shigar da tsarin zirga-zirga, fadada gine-ginen jama’a, da inganta wutar lantarki.   Wani abin lura a cikin amincewar akwai fitar...
    Gwamnatin jihar Kwara ta sake jaddada kudirinta na kara bude kofa ga al’umma domin ci gaba da kuma sanya jihar ta yadda za ta yi tasiri a duniya ta hanyar sanya hannun jari mai inganci.   Kwamishinan Ayyuka na Jiha Injiniya. Abdulquawiy Olododo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da ayukkan ma’aikatar a taron manema labarai na wata 3 na farkon shekara ta 2025, wanda aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar kudi, Ilorin.   A cewarsa jimillar ayyuka 46 da ake ci gaba da gudanarwa a cikin kwata na farko na shekarar 2025, daga cikin su 33 an kammala su baki daya, inda a yanzu haka ayyuka 11 ke ci gaba da gudana.   Ya kara...
    A dai-dai lokacin da kasashen Amurka da JMI suke ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliya ta Iran gwamnatin Amurka a jiya Laraba ta dorawa kamfanoni da mutanen da suke mu’amala da JMI a bangaren man Fetur takunkuman tattalin arziki. Da dama daga cikin wadannan kamfanoni na kasar China ne. Jaridar ‘the Nation’ ta Amurka ta ce tun farkon wannan shekarar ne shugaban Trump ta farfado da takurawar tattalin arziki  mafi muni a ka kasar Iran da nufin tilasta mata dawowa teburin tattaunawa ko kuma ta wagaza cibiyoyin Nukliyar kasar. A halin yanzu dai kasashen biyu zasu ci gaba da tattaunawar ba kai tsaye ba,  karo na hudu a birnin Roma na kasar Italiya a ranar Asabr mai zuwa....
    Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar haka, a jiya laraba, a lokacinda yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na majalisar. Jakadan ya bukaci kungiyoyin Falasdinawa su hada kansu don duk wani sabani a tsakaninsu nasarace ga HKI. Iranvani ya ce HKI tana ci gaba da aikata laifukan yaki a yankin Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, tare da tallafin Amurka da wasu kasashen yamma. Kuma tallafin da...
    Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa yawan kudaden da Amurka ta tallafawa Ukraine a yakin dai ya kai dalar Amurka biliyon $175, kuma wannan ita ce hanya tilo wacce Ukraine zata iya biyan wadannan basussuka. Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjeniyar. Wannan na faruwa ne al-hali ana ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine. Wannan yarjeniyar dai ta tabbatarwa...
    Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu tare da hadin guiwar Kyakyawar Gate Handicapped Centre Jos, sun bayar da tallafin keken guragu guda dari da talatin ga masu bukata ta musamman a Birnin Kebbi na jihar Kebbi.   Kakakin Ministan, Sadiq Nura Maiyaka, ya ce Ministan ya kuduri aniyar taimakawa masu bukata ta musamman don gudanar da ayyukansu na yau da kullun da sauran jama’a.   Ya shawarci wadanda suka amfana da su yi amfani da keken guragu kada su sayar da su domin su rika zagayawa da ayyukansu ba tare da wata damuwa ba.   Daraktan yada labarai na Kyawawan Gate Handicapped Centre Jos, Sandra Riliwan, ta ce wannan ba shi ne karon farko da cibiyar...
    Babu tabbacin ko ya rasu sakamakon rashin lafiya ko kuwa an kashe shi. An ce ‘yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, amma iyalansa sun iya haɗa Naira miliyan 11 ne kacal. Sun kuma buƙaci sabon babur da kayan abinci, duk a matsayin kuɗin fansa. Bayan da matar da ta tsere ta shaida wa jama’a abin da ya faru a ranar Litinin, sai aka yi masa sallar jana’iza a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta bakin kakakinta DSP Yazid Abubakar, ta ce har yanzu ba ta samu labarin tabbacin mutuwar limamin da iyalansa daga hukumomi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Rear Admiral Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC ya bayyana haka ne a jiya a bikin ranar “Tekun farisa’ ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen mai sauran kilomita Knots 116 na ruwa wanda yayi dai-dai da kilomita 215 / a ko wace sa’a yana da kayan aikin cilla makamai masu linzami. Kwamandan ya kara da cewa, wannan yana daga cikin shirin JMI na karfafa tsoron kasar, kuma sako ne ga makiya su san da haka, sannan sakon zaman lafiya ga makobta da abokai. An sanya ranar da turawan Portigal suka fice daga tekun farisa da mashigar ruwa ta Hurmus shekaru 1622 da suka gabata, a matsayin ranar tekunfarisa ta kasa....
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cututtuka da dama suna ƙamari a Najeriya wanda a mafi yawan lokuta mutanen da da7uke da irin cututtukan ba su da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar bil’adama. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace  Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan da ke sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliyan biyu a duk shekara a Najeriya. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar. Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya da Ashrafiyyah a yankin Suwaida. Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 70.
    Kwanaki kadan bayan  wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun  yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya zargi sojojin dake Mulki da amfani da ma’adanan kasar saboda kashin kansu maimakon yi wa mutane aiki. Mahalarta gangamin sun daga kwalaye dake dauke da rubutun yin tir da furucin jami’in sojan na Amurka da kuma nuna goyon baya ga shugaban kasar.  Daga cikin mahalarta gangamin da akwai fitaccen mawakin kasar, Ocibi Joan,wanda ya siffata jami’in sojan Amurkan da dabbar daji mai cin mutane yana...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da ya gana da ministar masana’antu ta Sudan Mahasin Ali Yakub da ta kawo Ziyara Iran. Muhammad Ridha Arif ya yi wa Sudan fatan alheri da son ganin zaman lafiya ya dawo, sannan kuma ya bayyana sake bude ofishin jakadancin Sudan a Tehran a shekarar da ta gabata a matsayin alamar kyautatuwar alaka a tsakanin kasashen biyu. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya zargi kasashen turai...
    Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman lafiya ba. Da yake Magana akan Falasdinu kuwa, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce: “Amfani da karfi domin kai wa ga sulhu” da “Diflomasiyya ta dole” akidun siyasa ne masu hatsarin gaske, yana mai kara da cewa; ta hanyar shimfida adalci ne ake kai wa ga sulhu,haka nan kuma yin furuci da hakokin da suke halartattu. Akan barazanar da wasu kasashe suke...
    Masana Alkur’ani daga ƙasashe 20 ne za su shiga Gasar Karatun Alƙur’ani ta Duniya da za gudanar a karon farko a Najeriya. Gasar wadda za ta gudana a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos na Jihar Filato, sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja Tsohon Ɗan Majalissar Wakilai Mai wakiltar Mazaɓar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Filato, Honorabul Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shiryawa. A lokacin gagarumin taron kaddamar da kwamitocin shirye-shiryen gasar ta duniya, wanda Gwanayen Alƙur’ani daga faɗin kasar nan suka halarta, Honourable Alkali ya ce tuni an sanar da cibiyar bunƙasa karatun addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo ta Sakkwato kuma ta goyi bayan ƙudirin. Ya...
    Bayan gobarar, jami’an kashe gobara sun kai ɗauki, kuma sun samu nasarar kashe wutar. A shekarar 2014, ƙungiyar Boko Haram ta kai wa wannan bariki na Giwa hari, inda ta kashe mutane da dama tare da jikkata wasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙarar wani abin fashewa mai ƙarfi ya girgiza Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan. Tashin abin fashewan ya jefa mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA da Jami’ar Maiduguri cikin tashin hankali. Ƙarin bayani na nan tafe.
    Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin.   Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa.   “Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga...
    Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu. Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba. Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.
    Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar ta Tsakiyar Afirka saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023. Wani taro da aka yi na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro kan sauyin siyasa a Gabon “ya yi nazari kan ayyukan tare da gano cewa sun yi nasara,” in ji shashen Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU a shafin X a ranar Laraba. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Sanarwar ta ce za a yi maraba da Gabon “ta dawo nan da nan, ta ci gaba da shiga ayyuka” a sakatariyar Tarayyar Afirka. An dakatar...
    Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.   Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban.   Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane...
    Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar.   Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba su da rajista, musamman magungunan inganta jima’i, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan abubuwa na da matukar barazana ga kiwon lafiyar jama’a.   Ya yi gargadin cewa, yin amfani da wadannan magungunan ba tare da kulawar likitoci ba zai iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, ciki har da haɗarin cututtukan zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
      Cikin adadin, masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Saudiyya da Serbia, suna cikin mafiya bayyana matukar baiken matakin na Amurka, da karin kaso 28.5 bisa dari. Yayin da a daya bangaren al’ummun Malaysia, da Isra’ila, da Australia, da Singapore, da Philippines, da Najeriya, da Portugal, da Pakistan, da Afirka ta kudu, kasonsu na nuna baiken matakan kara harajin na Amurka ya karu da sama da kaso 20 bisa dari. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015. Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade...
    Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar. Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci. Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku. Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace....
      To, bayanai a sama sun nuna ra’ayi iri daya na gwamnatocin dimbin kasashe masu tasowa. Ban da haka, wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar a kasashe 38, ya nuna cewa, matakan ramuwar gayya da kasar Sin ta dauka kan kasar Amurka suna samun goyon baya tsakanin al’ummun kasashe daban daban, inda a dimbin kasashe masu tasowa da suka hada da Najeriya, da Kenya, da Masar, da Ghana, da Afirka ta Kudu, da Turkiya, matakan kasar Sin suka samu goyon baya daga mutane fiye da kaso 70% da aka gudanar da bincike kansu. Kana a kasashen yamma da suka hada da Faransa, da Jamus, da Canada,...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta. AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa. Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023. Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take. ‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar. Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar...
    Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu. A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man...
    Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi. Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Shugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu. “Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin. “Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina...
    Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai ziyarci Jihar Katsina. Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Zango, ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba. Sanarwar ta ce shugaban zai kai ziyarar ce, domin ƙaddamarwa da kuma rangadin wasu ayyukan da Gwamna Umar Dikko Radda ya aiwatar a jihar. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja Karin bayani na tafe.
    A ko da yaushe Sin tana himmatuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kira da a warware rikici ta hanyar tattaunawa. A sa’i daya kuma, aniyarta ta kiyaye ikon mulkin kasa, da hakki da moriyarta a tekun kudancin Sin ba za ta sauya ba. Ita kasar Philippines kuma za ta dandana kudarta bisa ga yadda ta aiwatar da mummunan mataki kan batun zirin tekun Taiwan, da nufin biyan bukatun Amurka game da dabarunta a yankunan tekun Indiya da na fasifik. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.   Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
    Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah. Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba. A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a Jihar Osun. “Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar. Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.
    Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu. Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba da tafiyarsu cikin tsaro. Shugaban Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tsayin daka kan aiki. Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran. Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar. Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za su gudanar da cikakken binciken lafiyar maniyata kafin tafiyar su zuwa kasa mai tsarki da zai gudana a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna. Sannan kuma za su bayar da taimakon gaggawa a kasar Saudiyya tare da haɗin gwiwar Ayarin likitocin daga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON). Shugaban hukumar ya ce mambobin ayarin za su kasance cikin tsari na duba lafiyar mahajjata a tsawon lokacin...
    Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. . Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir  kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee. Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu...
    A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu. Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25. Rahmatollah Akrami,...
    Rahotannin da suke fitowa daga kasar Yemen na cewa katafaren jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki malakar klasarAmurka wato USS Harry Truman zai fice daga tekun red sea da nan kusa saboda makaman kasar Yemen da suka fada mata. Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta nakalto wani jami’in ma’aikatar tsaron kasar wanda baya son a bayyana sunansa yana cewa, saboda yawan hare haren da sojojin Yemen suka kaiwa jirgin, wadanda suka hada da amfani da makamai masu linzami samfurin Crusse da kuma Balistic, har ila yau da jiragen yaki masu kunan bakin waken da suka fada a kansa. A yanzun ya zama dole jirgin ya fice daga tekun. Tun cikin watan Maris da ya gabata ne gwamnatin...
    A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
    Wata tsohuwa mai shekara 80 a kasar Turkiyya za ta shafe sama da shekara 4 a gidan yari, saboda ta daki jikarta ’yar shekara 18 da silifa a lokacin da suke takaddama. Asiye Kaytan na zaune tare da jikarta Vural a unguwar Topraklık da ke Denizli a Kudu maso Yammacin Turkiyya. Tuntuni dai iyayen yarinyar suka rabu, inda tsohuwar mai shekara 80 take kulawa da ita fiye da kanta. A ranar 9 ga Agustan bara, bayan Vural ta dawo daga aiki, ta fada wa kakarta cewa, za ta fita waje tare da wasu abokanta. Tsohuwar ta ji tsoron fitar don kare lafiyarta, ta ce ba za ta yarda ba, har ma ta kulle kofa don tabbatar da cewa Vural ba...
    Haka kuma wasu hukumomin gwamnati sun taimaka, ciki har da Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Lafiya ta Tashar Jirgin Sama da Rundunar ‘Yansanda. Mutane biyu daga cikin waɗanda aka dawo da su na fama da matsananciyar rashin lafiya, kuma an garzaya da su asibitin New Ikeja don a duba lafiyarsu. Bayan an yi musu rijista da ɗaukar bayanan yatsunsu, an mayar da su cibiyar mazauna ‘yan gudun hijira da ke Igando, a Jihar Legas, inda za su samu taimako don ci gaba da rayuwa. NEMA ta ce wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na tallafa wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen waje da kuma taimaka musu...
    A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
    Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce a halin yanzu jam’iyyar APC ba ta buƙatar dawowar Kwankwaso cikinta saboda tasirinsa a siyasance na ci gaba da gushewa. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno Darekta Janar na KASASCO, Kwamared Yahaya Usman Kabo, ya ce jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abbas ta yi tsayuwar daka da kafa tubalin samun nasara...
    Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu. Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa, da akwai batutuwa da dama da su ka raba kawunan manyan malaman addinin na Roman Katolika da  su ka batun auren jinsi, da rawar da mata za su taka a karkashin inuwar cocin. Sai dai kuma wani mai sharhi akan abubuwan da su ka shafi cocin, Reese ya bayyana cewa, masu zaben za su mayar da hankali ne akan wanda zai kare ayyukan da mamacin...
    Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”...
    Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata. Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya. Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani. Wani dan sintiri da yake...
    Kamar yadda Sin da masana suka sha fada, mummunan matakin na Amurka, zai fi yi mata illa maimakon kasashen da take neman cin zalinsu.   Tabbas Sin ta yi gaskiya da ta ce bayar da kai ko ja da baya, dama ce ga mai cin zali. Don haka, Sin ta yi daidai da ta tsaya haikan wajen mayar da martani ba tare da bada kai ba, domin Amurka ta gane kuskurenta, kana ta fahimci cewa, lokaci ya wuce da za a rika biye mata tana yin abun da ta ga dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana. A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar. Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar. Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu. Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.   A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.   Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013...
    Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta. A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025. Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai. Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Darajar cinikayyar ba da hidima ta kasar Sin ta karu sosai, inda ta kai yuan triliyan 1.97 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 270 a rubu’in farko na bana, karuwar kashi 8.7 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Darajar jimillar hidimar fice ta kai yuan biliyan 835.15, karuwar kashi 12.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, yayin da darajar hidimar shige ta kai yuan triliyan 1.139, wanda ta nuna karuwar kashi 6.2 cikin dari. Hidimomin tafiye-tafiye sun nuna karuwa mafi sauri na kashi 21.8 cikin dari. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    “Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.   “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”   Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.   Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Ƙungiyar ISWAP mai yaƙi da tayar da ƙayar baya a yammacin Afirka, ta ɗauki alhakin harin da ya yi ajalin mutum 26 a Jihar Borno. Ƙungiyar ta iƙirarin ɗaukar alhakin harin ne a wani saƙo da ta wallafa a shafin Telegram kamar yadda BBC ya ruwaito. Aminiya ta ruwaito yadda wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida. Ta yi wa saurayinta...
    Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...
    Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya). AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba. Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.” Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya...
    Rahotonni sun tabbatar da cewa: Da tsakar daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila dauke da motocin soji guda hudu da wasu sojoji masu tafiyar kafa sun kutsa cikin yankunan kasar Siriya daga titin Al-Hurriya, inda suka wuce titin Al-Kassarat, zuwa Talat Jabata Al-Khashab. Majiyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta bayyana cewa: Sojojin mayar sun kafa shingen binciken ababen hawa inda suka tsaya suna binciken ababan hawa da ke wucewa, sannan suka haska wuta don gano hanyar kafin su fita ta hanyar da suka shiga. Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma suna shawagi a sararin samaniyar birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya. A jiya Litinin ma, sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai...
    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama. A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar...
    Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari. Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi. Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“ Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu  gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman...
    Shi ma dayan, bayan ya bayyana cewa, sun kasance barayin mota ne a jihar Katsina amma wani abokinsu ya gayyace su zuwa jihar Filato domin ci gaba da sana’ar.    Yayin da ya amince zai jagoranci Tawagar Soji zuwa maboyarsu, jami’an sun gano bindiga kirar fistul daya da mukullai da suke amfani da su wajen bude motoci da gidajen jama’a, inda daga bisani shi ma ya yi kokarin arcewa kamar yadda abokin shi ya yi. Hakan ta sa shi ma aka harbe shi har lahira. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    kauyuka a China, ana nufin yankunan da suka bunkasa, wadanda suka kasance, sun yi kamance-ceniya da sun anguwanin GRA a Nijeriya da kuma a nahiyar Afirka.   A yankin na Hero Bay, an tanadar da tituna inganciyyar wutar lantarki, tsaftatattacen ruwan sha da kuma kafar Inernet   Akwai manyan bene masu tsawo a yankin, wadanda tsawonsu ya dara na bene mai hawa biyar, inda kuma aka tanadar wa da yankin, ababen more rayuwa.   kananan hukumomi ne, suka gina wadannan matsugunnan, musamman donin a dakile barazanar kwararowa alumma daga kauye, zuwa cikin birane.   A gwajin da aka yi na yankunan da su habaka sosai a China, ana buga misali da Hero Bay kan yadda gwamnati ke bai wa alumma...
    Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida. Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal Majiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata. Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu...
    Wani saurayi ya wallafa wani labarinsa a kafar sada zumunta ta Reddit tare da yin nadama, inda ya ce matar da suke soyayya ta faɗa masa cewa, an haife ta ne a shekarar 1998, har sai da ya duba bayanan fasfo dinta. A wani lamari mai ban al’ajabi da ban tsoro, matashin ɗan shekara 26 ya girgiza bayan ya gano cewa, matar da yake soyayya da ita da nufin aure, bayan shafe shekaru huɗu suna tare tana da shekara 47, ba 27 ba, kamar yadda ta yi iƙirari. An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Saurayin ya tafi shafin Reddit don ya wallafa labarinsa na nadama, inda ya...
    Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN).   Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamatin, Ministan Sufuri, Sanata Said Alkali, ya jaddada muhimmancin shawo kan kalubalen hadurran da ke ci gaba da barazana da haddasa munanan asarar rayuka da dukiyoyi.   Alkali wanda ya jaddada bukatar a gaggauta kawo karshen wannan mumunan lamari, ya bai wa kwamitin mako guda ya gabatar da rahotonsa, inda ya jaddada cewa, tsaro da inganci su ne kan gaba a cikin manufofin gwamnatin Bola...
    An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai. A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita. Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu....
    Ba wannan ne karo na farko da shugaba Trump ya nuna girman kai da rashin sani game da Afirka ba. A watan da ya gabata, lokacin da yake bayani game da dalilin da ya sa gwamnatinsa ke rage gudummawar jin kai da take bayarwa a duniya, ya ce a baya, Amurka ta samar wa kasar Lesotho gudummawar dala miliyan 8, amma “ba wanda ya taba jin sunan wannan kasa”. Amma ita wannan kasar da ko sunanta shugaba Trump bai taba ji ba, ya sanya ta cikin jerin kasashen da ya sanar da zai kakaba musu haraji, har ma ya sanya mata haraji na kaso 50%. Idan ba mu manta ba kuma, a wa’adin shugabancinsa na farko, shugaba Trump ya taba...
    Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    A nasa ɓangaren, mai bai wa Gwamnan Shawara Kan Al’ammuran Tsaro, Janar Dahiru Abdusalam (Mai Ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana ɗaukar matakai tare da jami’an tsaro don samar da tsaro mai inganci. Ya kuma bayyana cewa duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a hanyar Damaturu zuwa Gujba, jami’an tsaro na ƙoƙarin yin sintiri domin tabbatar da tsaro. Janar Dahiru ya ce, “Koda yake muna fuskantar ƙalubale daga Boko Haram a yankunan wasu sansanin sojoji, jami’an tsaro na ci gaba da aikinsu domin kare yankin.” Ya ƙara da cewa, “Muna taka-tsan-tsan musamman wajen daƙile karɓar haraji daga Boko Haram a wasu yankuna. Wannan al’amari yana da matuƙar wahala, amma muna fatan za mu samu nasara.” Janar Dahiru ya...
    Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno. Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu. Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa. “Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke...
    Rikicin sarautar Kano da aka shafe kusan shekara guda ana yi, ya ɗauki sabon salo. Abin da ya fara a matsayin rikicin neman halacci tsakanin sarakuna biyu —Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero —yanzu ya kai su ga yin naɗin sarautu iri guda a fadodinsu daban-daban a masarauta ɗaya. A ranar 9 ga Afrilu, 2025, Sarki Sanusi II ya sanar da ɗaga likafar baffansa kuma Wamban Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, zuwa  matsayin sabon Galadiman Kano. Kasa da makonni biyu bayan haka, a ranar 21 ga Afrilu, 2025, Sarki Aminu Ado Bayero ya mayar da martani ta hanyar naɗa babban yayansa kuma ɗan fari ga marigayi Sarki Ado Bayero, Sanusi Ado Bayero, a matsayin nasa Galadiman Kano. Wannan sabon...
    Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da  kuma 1000. Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa. Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba. Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba. Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar. Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya...
    Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin  masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar. EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan...
    Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Muslunci a Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, rasuwa. Babban Mufti na ƙasar Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan, ne ya sanar da rasuwar Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a kai a daren Litinin. Sai dai bai bayar da cikakken bayani game da inda Sheikh Hadiyatullah ya rasu ko kuma lokacin da hakan ya faru ba. Sheikh Molaasan ya bayyana cewa rasuwar marigayi Sheikh Hadiyatullah ta bar giɓi mai wuyar cikewa a shugabancin Musulunci na ƙasar. Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya “An haife shi a garin Iwo a Jihar Osun kuma...
    Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
    Shugaban  kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye. Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take  ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar. Shugaban kungiyar...
    Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar. Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.” Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita...