Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow
Published: 9th, May 2025 GMT
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet.
An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow.
Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Babban Taro Kan Shawarar Samar Da Ci Gaban Duniya
Jiya Talata 23 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci babban taro kan shawarar samar da ci gaba ga duniya baki daya, tare da gabatar da jawabi a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka.
A gun taron da kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa, firaminista Li ya ce, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya duniya baki daya a wajen babban taron MDD a shekara ta 2021, shawarar da ta mayar da hankali kan muradun daukacin bil’adama. Li ya kuma jaddada cewa, Sin za ta kara zama kasar dake nuna goyon-baya, da taimakawa samar da ci gaba na bai daya, da ci gaba da daukar matakan zahiri, da kara daukar nauyin dake wuyanta. Kazalika, kasar Sin za ta ci gaba da zuba kudi wajen raya duniya baki daya, da inganta hadin-gwiwa a fannin kimiyya da fasaha don daukaka ci gaban duniya, da ingiza ci gaban duniya ba tare da gurbata muhalli ba.
Mahalarta taron daban-daban, sun goyi bayan manyan shawarwarin duniya guda hudu da shugaba Xi ya gabatar, gami da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, tare da nuna babban yabo ga dimbin nasarorin da aka samu don inganta hadin-gwiwa a fannin aiwatar da shawarar samar da ci gaban duniya, da maraba da sabbin matakan hadin-gwiwar sassan kasa da kasa da suka shafi fasahar kirkirarriyar basira ta AI da kasar Sin ta gabatar. Har wa yau, bangarori daban-daban sun nuna cewa, ra’ayi da matakan kasar Sin sun dace da manufofin kundin tsarin mulkin MDD, kuma ya kamata a aiwatar da ra’ayin cudanyar sassa daban-daban, da kyautata tsarin shugabancin duniya, da taimakawa samar da ci gaba dake nuna juriya ga bangarori daban-daban, da kiyaye muradun kasashe daban daban, musamman kasashe masu tasowa. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp