Tawagar Hafsoshin Sojojin Afirka Ta Ziyarci Kasar Sin
Published: 7th, May 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Halarci Babban Taro Kan Kasuwancin Halal A Malaysia
Tawagar gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahun sauran kasashe da suka halarci taron kasa da kasa na Halal da ke gudana a Malaysia (MIHAS), domin neman jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki.
Tawagar karkashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Kiwo, Farfesa Abdurrahman Salim Lawal, ta hada da Dr. Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Hukumar Zamanantar da Harkar Noma ta Jihar Jigawa, da kuma Hajiya Aisha Sheik Mujaddadi, Darakta-Janar ta Hukumar Inganta Zuba Jari ta Jihar.
Tuni dai tawagar ta halarci taruka daban-daban yayin isar su kasar ta Malaysia, ciki har da taron Halal Certification Convention, taron kasuwancin Halal na duniya, da MIHAS Power Talk kan zuba jari ta hanyar Halal, da kuma zaman tattaunawa kan kasuwar Halal da bada shaida.
Farfesa Lawal ya ce Jihar Jigawa na son ta zama cibiyar samar da kayayyakin Halal a yammacin Afirka, ta hanyar nuna ƙarfin ta a bangaren noma, musamman kiwo da kuma amfanin gona.
Ya kara da cewa manufar ita ce samar da haɗin gwiwa da kamfanonin Malaysia, hukumomin gwamnati, da shugabannin masana’antun da ke samar da kayayyakin Halal a fannonin sarrafa nama da noman da aka tabbatar da Halal.
“Shigar mu cikin MIHAS wani bangare ne na jajircewar wannan gwamnati wajen bambance hanyoyin samun kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi. Mun yi imani cewa haɗin gwiwa da bayanan da muka samu daga wannan taro za su taimaka wajen jawo jari da kuma samar da damar arziki ga al’ummarmu.” In ji shi.
Tawagar ta kuma gudanar da tarurruka da dama tare da manyan masu ruwa da tsaki na Malaysia domin tattauna batutuwan zuba jari, musayar fasaha, da kuma shirye-shiryen ƙarfafa ƙwarewa.
Usman Muhammad Zaria