Leadership News Hausa:
2025-10-13@20:18:52 GMT

Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

Published: 11th, May 2025 GMT

Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

Sarkin Katsina Muhammadu Dikko Allah ya yi ma shi rasuwa,a shekarar 1944 da ba’a dade da shigarta ba,bayan ya sanu damuwa daga rashin lafiya, wannan shi yasa aka fara fafutukar neman wanda zai gaje shi.Ta bnagare daya akwai gidan Sarautar Dallazawa  a karkashin jagorancin Yarima, wanda shi dan Sarkin Katsina Abubakar ne wanda yake ganin Sarautar Katsina wata dama ce ta shi,sai ta daya bangaren kuma akwai ‘ya’yan marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko,wadanda su ma suna da matukar karfi,wadanda daga cikinsu ma da akwai wata ‘yar jayayya kan wanda zai gaji mahaifin nasu.

Watan Maris 1944,sai masu zaben Sarki suka zabi  karami daga cikin ‘ya’yan Dikko da ake kira da suna Usman Nagogo,wanda shi ne Turawan mulkin mallaka na Ingila suke so saboda yana da ilimin Boko,da kuma yadda ya kasance kusa da mahaifinsa.An nadawa Usman Nagogo rawanin Sarautar ranar  19 Mayu 1944 Yayin da shi kuma marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko aka rufe shi,a Lambun da ke fadar Sarkin Katsina Dikko

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Sarki Sarkin Katsina Muhammadu Dikko

এছাড়াও পড়ুন:

Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

 

Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru.

 

Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.”

 

Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro.

 

Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani. Wannan mataki ya rage hare-hare a wasu yankuna, inda al’umma ke sake komawa gonakinsu da kasuwancinsu cikin natsuwa.

 

Tattalin Arziki da Ci gaban Sana’o’i

A bangaren tattalin arziki, gwamnatin Dauda Lawal ta mayar da hankali kan farfaɗo da ƙananan sana’o’i da bunƙasa harkar kasuwanci.

 

Ta ƙaddamar da Zamfara Economic Empowerment Programme (ZEEP), wanda ke bai wa matasa da mata tallafin jari da horo kan sana’o’i kamar ɗinki, noma, kiwo, sana’ar waya da ƙera kayayyakin gida.

 

Haka kuma, gwamnatin ta buɗe Industrial Cluster a Gusau domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ƙananan masana’antu, tare da samar da tallafi daga Bankin Noma da na Masana’antu.

 

A cewar kwamishinan tattalin arziki, “Gwamna Lawal na son ganin Zamfara ta daina dogaro da kuɗin rabon asusun tarayya, ta koma jiha mai samar da abin more rayuwa.”

 

Ilimi: Sabon salo na sake gina makarantun gwamnati

Fannin ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. A ƙarƙashin wannan gwamnati, an mayar da hankali wajen gyaran makarantu sama da 200, tare da samar da kujeru, littattafai, kayan koyarwa da gyaran gine-gine.

 

Gwamnati ta kuma dawo da malamai dubu ɗaya (1,000) da aka bar su ba tare da albashi ba a baya, sannan aka ƙaddamar da shirin “Back to School” domin dawo da yara daga kan titi zuwa aji.

 

Haka kuma, gwamnatin ta sake gyara Zamfara State University Talata-Mafara, inda aka ƙara sabbin sassa na kimiyya da fasaha tare da inganta wuraren kwana da ɗakin karatu.

 

Lafiya: Asibitoci suna sake farfaɗowa

A bangaren lafiya, gwamnatin ta ƙaddamar da Free Maternal and Child Healthcare Programme, wanda ke bai wa mata da yara ƙarƙashin shekaru biyar kulawa kyauta a asibitoci.

 

An gyara asibitoci 14 a faɗin jihar, ciki har da babban asibitin Gusau, da aka sake gina dakin haihuwa da dakin tiyata da kayan aiki na zamani.

 

Gwamnati ta kuma samar da motocin ɗaukar marasa lafiya (ambulance) a kowace ƙaramar hukuma, tare da tura sabbin ma’aikatan jinya, likitoci da masu jinya zuwa yankunan karkara.

 

Ayyukan Gina Hanyoyi da Tsarin Gine-gine

Gwamnatin Dauda Lawal ta ƙaddamar da aikin gine-ginen manyan hanyoyi kamar Gusau–Damba–Mayana, Zurmi–Bukkuyum, da Kaura Namoda–Birnin Magaji.

 

Har ila yau, an gyara titunan cikin garin Gusau, inda aka saka fitilun zamani da tsarin ban ruwa don rage ƙura da datti.

 

A cewar Gwamna Lawal, “titi ba kawai hanyar mota ba ce, ita ce hanyar ci gaban al’umma.”

 

Gudanar da Gwamnati da Gaskiya

Wani abu da ya bambanta wannan gwamnati da waɗanda suka shuɗe shi ne gaskiya. A karon farko, Zamfara ta kafa tsarin Open Budget Portal, inda kowa zai iya ganin yadda kuɗin gwamnati ke tafiya.

 

Gwamnatin ta kuma kafa Anti-Corruption and Due Process Bureau, domin tabbatar da cewa kowace kwangila yana bin ƙa’idar gaskiya da nagarta.

 

Matsayin Jama’a da Hangen Nesa

Yawancin mazauna jihar sun bayyana cewa wannan gwamnatin “ta shigo da sabuwar rayuwa.” A cewar wani ɗan kasuwa a Gusau, “A baya, an manta da mu gaba ɗaya. Amma yanzu muna ganin canji a zahiri.”

 

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa burinsa shi ne “Zamfara ta zama misalin tsabta, ci gaba da daidaito a Arewa.”

 

A tsarin da yake ginawa, ya ƙunshi Zamfara 2050 Vision Plan, shiri mai dogon lokaci da ke nufin canja jihar daga karkacewar tsaro da talauci zuwa jihar da ke iya dogaro da kanta.

 

Kammalawa

A ƙarshe, shekaru biyu bayan hawansa mulki, Dauda Lawal ya kafa tubalin sabon sahu a Zamfara – sahun da ya haɗa da tsaro, ilimi, lafiya, da tattalin arziki.

 

Ko da yake har yanzu akwai ɗan burbushin ƙalubale na tsaro da tattalin arziki, yawancin ‘yan Zamfara na ganin cewa wannan gwamnatin ta fara canji daga tushe, kuma abin da ke buƙata shi ne ci gaba da ɗorewar gaskiya, aiki tuƙuru da haɗin kai.

 

Zamfara tana fuskantar sabon zamani. Kuma idan aka kiyaye wannan tafiya, akwai yiwuwar a ce a cikin ɗan lokaci, Dauda Lawal ya kafa sabon tarihin shugabanci a Arewa.

 

Rahoto na musamman daga Mahdi Musa Muhammad

Ƙaramin Edita, Blueprint Manhaja

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nazari Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci September 11, 2025 Nazari Shettima: Shekaru Biyu Na Mataimaki, Jagora Mai Hangen Nesa Da Kawo Sauyi Nagari June 2, 2025 Nazari Masana Sun Bayyana Yadda Yakin Neman Zaben 2027 Ke Barazana Ga Harkokin Tafiyar Da Gwamnati May 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
  • Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
  • Tarihin Hassan Usman Katsina (1)
  • Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar .
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina