2025-05-09@23:45:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3604
«da aka yi watsi da ita»:

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani
Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin 2025. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da tashin maniyattan a filin jirgin Sam Mbakwe da ke birnin Owerri na Jihar Imo. ’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025 Sahun farko na maniyyata 315 waɗanda suka kama hanyar ƙasa mai tsarki sun fito ne daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa inda jirgin Air Peace ne ya kwashe su. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya, Farfesa Abdullahi Usman da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III da sauran manyan jami’an gwamnatin Nijeriya ne suka tarbi Kashim Shettima...
A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta. “Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.” Bayanin hakan ya...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar. Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu kasar Oman ta tattauna da bangaren waccen bangaren. Babban mai shiga tsakani na Iran ya jaddada cewa tattaunawar Tehran da Washington tana ci gaba. Iran da AMurka dai sun yi jerin tattaunawa har guda uku a Oman, sannan a Italiya sai kuma a Oman. Dukkan bangarorin dai sun bayyana tattaunar da mai kyakyawan fata.
Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirerren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da dala biliyan...
Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da ɗalibai suka zana a bana. Wata sanarwa da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Juma’a, ta ce an riƙe sakamakon ɗalibai 39,834 wanda a cikin wannan adadi tana bincike kan sakamakon ɗalibai 1,426. An kama mutum 78 da makamai da kwayoyi a Kano Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da alƙaluman sakamakon bana tana mai cewa yawancin ɗaliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400. JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar daga cikin 2,030,862 da suka yi rajista,...
An kama mutane 78 tare da kwace tulin miyagun kwayoyi da makamai da kayan sata a wani samame da ’yan sanda suka kai kwanan nan domin ayyukan laifi a Jihar Kano. A yayin samamen, an kama gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022. Daga cikin sauran wadanda aka kama har da wani da ake zargin dan fashi da makami ne da bindigogi biyu da harsasai. Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya sanar a taron ’yan jarida da ya gudana a hedikwatar rudunar da ke Bompai a ranar Juma’a cewa aikin kamen ya yi daidai da umarnin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa kan a aiwatar da ingantattun matakai domin...
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa. Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar da aka yi watsi da ita Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitoci Mista Alausa ya bayyana cewa wannan matakai ya samu ne sakamako nazari da aka yi wajen sanya ƙaƙƙarfan jari a manyan makarantun ƙasar. Ministan ya ce daga yanzu babu batun bai wa ’yan ƙasar kuɗaɗen ƙaro ilimi daga ƙetare, saboda yanayi da ake ciki da ma kyawun tsari da...
Wasu kananan yara biyar sun mutu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a harabar wani gida a yankin Agyaragu da ke Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa. Yaran sun rasu ne a sakamakon daukewar nunfashinsu a cikin motar, lamarin da ya jefa mazauna yakin yankin, wadanda yawancinsu manoman ne, daga kabilu daban-daban, cikin alhini. An gano gawarwakinsu ne da misalin karfe 1 na rana a cikin motar bayan mutanen yankin sun shafe tsawon lokaci ana neman su. Misis Ifeoma Nnaji, wacce ta rasa ’ya’yanta biyu, Nmesoma da Chidima, ta bayyana yadda aka gano gawarwakin ta ce, “Mun duba ko’ina… Daga karshe, wani ya ba da shawarar mu duba motar da aka yi watsi da ita,...
Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57 Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya...
Farfesa Bamaiyi ya bayyana ainihin aikin IAR a matsayin habaka nau’ikan dimbin amfanin gona da kuma jure fari wadanda suka dace da bukatun noma a Nijeriya. Ya bayyana masarar TELA a matsayin wata sabon salo da kirkira ta zamani a kimiyyance domin magance matsalolin da ake ci gaba da addabar amfanin gona, kamar kwari da canjin yanayi. Aikin “Masarar TELA bai takaita kan inganci da wadatar abinci ba, har ma tana ba da kariya ga rayuwar manoma, da inganta noman da kuma magance ainihin illar da tsutsotsi ke haifarwa, gami da juriya a yayin fari,” in ji shi. Shi ma da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Muyideen Oyekunle, wani masani a fannin tsirrai kuma daya daga cikin jagorori masu...
Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.27, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 314, yayin da adadin hajojin da kasar ta shigo da su daga waje ya karu da kaso 0.8 bisa dari a shekara zuwa kimanin yuan tiriliyan 1.57. Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. Wani kwararre a kan sha’anin tsaro, Jackson Lekan, ya ce bayanan Manjo-Janar Kanye ya nuna laifi da kuma gazawar hukumomin da ke da alhakin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa. Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman. An kashe mutane da yawa tare da raba wasu dubbai da gidajensu a jihohin Filato da Benue a sakamakon hare-hare da makiyaya ɗauke da...
Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama mai dadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya. Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu dabbar da zai yi ba, sai ya yi azumi na kwana uku a Makka kafin a fita zuwa Arfa idan zai yiwu. Idan bai samu dama ba sai ya yi bayan Arfa kafin ya bar Makka. Bayan ya dawo garinsu, sai ya yi sauran azumin kwana bakwai. Jimillar azumin kwana 10 ne yake madadin hadayar da bai yi ba. Amma kuma kar ya zama Alhaji...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana. An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan...
Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s. “Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia, Afrika ta Kudu da Zimbabwe” in ji shi, ya kara da cewa, wannan sabon yarjejeniyar za ta karfafa hadin kai a bangarorin kimiyya da fasaha, bincike da kuma samar da ci gaba mai dorewa. A nasa tsokacin, Ministan harkokin waje na Cuba, ya ce, dangantakar da ke tsakanin Cuba da Afrika mai karfi ne, ya kuma gode wa Nijeriya a kan goyon bayan da ta...
Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma a lokaci daya muna cikin Shirin fuskantar kowane irin yaki duk yadda ya zo. Janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin karrama shahidan yi wa kasa hidima, a hubbaren Imam Ridha ( a.s) ya kuma kara da cewa; Ya kamata Amurkawa su kwana da sanin cewa, idan su ka yi mana barazana, to a shirye muke domin fuskantar kowane irin yaki, a duk yadda ya zo. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma zargi Amrukawa da cewa su, ba masu cika alkawali ba ne, saboda yadda su ka yi...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa. Shugaban na kungiyar Ansarullah ya kuma ce, a baya, ba a Kallon laifuka irin wadannan kai tsaye ta talbijin amma a yanzu ana Kallon ta akwatin talabijin. Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi,...
Shugabannin kasashen Rasha da China Sun yi alkawalin fuskantar siyasar Amurka akansu,a yayin wani taro da su ka yi a birnin Moscow a daidai lokacin bikin tunawa da zagayowar cikar shekaru 80 da samun galaba akan ‘yan Nazi na kasar Jamus. Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaransa na China Xi Jing Ping sun yi tattaunawa ta fiye da sa’oi 3, sun rattaba hannu akan yarjeniyoyi a tsakaninsu da su ka kunshi kara yawan hannunu jarin da su ka zuba a cikin kasashen junansu, haka nan kuma yin aiki a tsakaninsu domin tabbatar da zaman lafiya a duniya sannan kuma da zurfafa girman alaka a tsakaninsu. Bayanin bayan taron kasashen biyu ya kunshi nuna damuwa akan yadda Amurka take kara...
Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38. A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa. Wannan Jaridar na da ra’ayin cewa, ‘yayan Kotun uku da Mai Shari’a Alkalan Kotun Thomas Okosun da ya yanke wannan hukunci, sun canci yabo kan tsaywar da suka yi kai da Fata na yanke wannan hukuncin, duk da matsin lambar da suka fuskanta, inda suka tabbatar da ikon da Hukumomin FCCPC da NDPC suke da shi. Kazalika, abinda ya kara nuna mahimmancin hukuncin Kotun,...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, da sanya kwanciyar hankali da kyakkyawan kuzari a duniyar mai fuskantar sauyi da tashe-tashen hankula. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin ziyarar da ya kai kasar ta Rasha. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba mai dorewa, cikin koshin lafiya kuma a babban mataki, sakamakon...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai. A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro. ’Yan sanda sun ƙaddamar da ƙwararrun Jami’an tsaro saboda makarantu a Bauchi An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna ƙoƙarin kare ƙasarsu sosai”. Ya bayar da tallafin Naira miliyan 2m ga kowane iyalan...
A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa game da kara zurfafa hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal. Ya ce, ta hanyar haɗa kai da masu ruwa da tsaki ne jami’an tsaro za su iya kaiwa ga samar da ingantaccen tsaro a makarantu ga yaran Najeriya. An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Egbetokun wanda ya samu wakilcin AIG Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya shawarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi amfani da ƙwarewarsa...
Wata kotun majistare da ke titin Ibrahim Taiwo a Kaduna ta gurfanar da wasu mutane 10 da suka haɗa da kaka, bisa laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 16 fyaɗe a ƙauyen Likoro da ke ƙaramar hukumar Kudan ta jihar. An ruwaito cewa wanda ake zargi mutum na 11 na hannu a lokacin da shari’ar ta taso, ranar Alhamis. An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai Waɗanda ake zargin, a cewar rahoton farko da aka samu, sun ce wacce aka yi wa fyaɗen an yi ta aikat fyaɗen a lokuta daban-daban ta hanyar yaudara da kuma lallashinta ta zuwa wurarensu daban-daban inda suke da masaniya game da ita....

Aragchi: Muna Bukatar Rage Zaman Daradar Da Kuma Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Pakisatan Da Indiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A jiya larabace sojojin kasar Indiya suka cilla makamai masu linzami kan kasar Pakisatan da kuma yankin Kashamir da ke karkashinn ikon Pakisatn. Inda mutane 31n sauka rasa rayukansu a yayinda wasu 46 suka suka ji Rauni. Shehbaz Sharif firai ministan kasarPakisatan ya bayyana cewa kasar Pakisatan zata rama, kuma ya sha alwashin maida martani kan duk wani jinin mutanen Pakisatan da sojojin Indiya suka zubar....
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo a taron da aka fara gudanarwa a yau a makarantar Darushafia dake birnin Qom. Taron na Qom yana Magana dangane da “Makarantun Hauza a Qum, Juyin juya halin musulunci a Iran da kuma Gwagwarmaya’. Sheik Kasim ya kara da cewa mutanen kasar Lebanon sun fara gwagwarmaya ne bayan gwamnatin HKI ta mamaye kasarsu, sannan bayan sun sami jagoranci da tunanin Imam Khumaini (q)...
Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka shirya film na tattara bayanai yadda aka kashe Shirin Abu Akela wato ‘ Zeteo’ dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka na cewa sunan sojan HKI ta ya kashe Shirin shi ne Alon Skajio, wanda shima daga baya an kashe shi a birnin na Jenin daga bayan a wani farmakin da sojojin yahudawan suka...
Tsohon ministan kudin kasar Amurka John Connally ya ce, dala kudi ne na Amurka, amma matsala ce ga sauran kasashen duniya. Yanzu haka tsarin kudin na haifar da karin radadi ga kasashe daban daban, sakamakon matakan kasar Amurka na kashin kai, lamarin da ya sanya dimbin kasashe neman kauracewa tsarin dalar Amurka. Misali, a rubu’in farkon bana, darajar cinikin da kasar Sin ta yi tare da kasashen Malaysia da Cambodia da kudin RMB, ta karu da kaso 27%, da 24%, bisa makamancin lokacin bara. Kana a nata bangare, kasar Najeriya za ta kulla yarjejeniyar musayar kudin Naira zuwa kudin Sin RMB kai tsaye, tare da kasar Sin, bisa wani labarin da jaridar Vanguard ta kasar Najeriya ta gabatar. Kudi wani...
A yau ne aka bude kasuwar baje koli na kayakin da suka shafi man fetur da gasa wadanda aka kera a JMI karo na 29 a yau a nan birnin Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasuwar zata ci ne daga yau 8-11 ga wannan watan na mayu da muke ciki. Labarinn ya kara da cewa kamfanoni fiye da 2000 daga ciki da kuma wasu kasashen duniya 14 ne suka halarta ta. Baje kolin yana nuna matsayin JMI a fagen makamashi a duniya.
Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis. Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya. Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane Robert Prevost zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV). Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.

Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki
Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka. A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu. Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye...
Eze na cikin jerin da rundunar tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu da yake da shi wajen kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Gabas. Manjo Janar Kangye, ya ƙara da cewa, a watan Afrilu, sojojin sun ceto mutane 173 da aka yi garkuwa da su, sannan sama da ‘yan ta’adda 204 da iyalansu sun miƙa wuya. Haka kuma, sun kama mutane 430 da ake zargi da satar mai da wasu laifuka daban-daban. A ƙarƙashin Operation DELTA SAFE, an daƙile satar mai da darajarsa ta haura Naira biliyan 1.9 a cikin mako guda. Sun ƙwato sama da lita miliyan ɗaya ta ɗanyen mai da kuma dubban litoci na man fetur da wasu nau’inkan haramtattun mai....
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai, sai na (Batsari/Safana/Ɗanmusa) Hon. Iliyasu Abubakar. An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama’iyyar APC, wanda dawowar su jam’iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam’iyyar take da shi a Jihar Katsina.
Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana. A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar aiki yayi nisa na fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki. Yana mai cewar, hukumar ta kammala duk wani shiri ga maniyyata domin fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a lokacin taron da suka gudanar da jami’an sun rabawa shugabanin shiyya-shiyya da jami’an su dukkanin kayayyakin maniyyata da dukkan sauran muhimman abubuwa daya dace. Game da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da yin garkuwa da wasu mutane a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Timfon John ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Uyo, inda ya ce an kama su ne biyo bayan sahihan bayanai game da shirin yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Eket. A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje Sojoji sun kama mutum 4 kan zargin ta’addanci a Taraba John wanda ya bayyana cewa mace ɗaya tilo a cikin waɗanda ake zargin ba ’yar Najeriya ba ce, ya bayyana cewa an...
Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA. Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami’ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi. “Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara,...
Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne. Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar. Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Jalingo. Ya bayyana cewa rundunar ta sami kiran gaggawa dangane da shigowar wasu mutane ɗauke da makamai a yankin. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Kyaftin Oni ya ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar...
Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton sakonnin waya na Ma’aikatar Harkokin Waje. Sakonnin sun nuna yadda ofishin Jakadancin Amurka da ma’aikatar suka matsa wa ƙasashe don su kawar da duk wata cikas ga kamfanonin tauraron dan Adam, yana mai ambaton kamfanin Starlink da sunanta, kamar yadda jaridar Post ta ruwaito. Takardun ba su nuna cewa gwamnatin Trump ta buƙaci a ba da fifiko ga Starlink a musayar rage haraji ba, kamar...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
’Yan sanda sun gano harsasai guda 500 a wata maɓoyar masu aikata laifuka da ke kusa da hanyar Bauchi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya ce an gano harsasan ne ta hanyar rahotannin sirri, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka a jihar. Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa an gano harsasan ne bayan wani kisan kai da ya faru a yankin, inda aka kashe wani da ba a gane ko wanene ba. “Bayan samun rahoton faruwar lamarin, nan take muka fara gudanar da bincike domin gano yanayin da ya kai ga mutuwar wanda aka kashe. An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan...
An kwantar da wasu matan aure kishiyoyin juna a asibiti bayan da suka sha maganin kara sha’awa domin burge mijinsu bayan ya auro mata ta uku. Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da mijinsu ya auro ta tare. Da take tabbatar da faruwar lamarin, mijin nasu ya ce bayan kai su asibiti ne aka yi musu gwaji aka gano cewa wasu gaɓoɓinsu sun samu matsala, wanda ake zargin maganin da suka sha ne ya haddasa. Ya ce, “ina gidan amarya aka kira ni cewa matana ba su da lafiya, inda na je na samu suna birgima cewa cikinsu na ciwo. Sai na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai masu aminci don taimakawa wajen inganta tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Iran Ta Yi Tsokaci Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa: Shugaban Kasar Iran Zai Gana Da Shugaban Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe. Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran...
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha. Ta jaddada cewa “wadanda ke neman canza sunan Tekun Fasha ba su fahimci tarihin dubban shekaru na Iran ba.” Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran. Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na...

Yemen Ta Jaddada Cewa: Idan Amurka Ta Kai Mata Hari, Tabbas Yarjejeniyar Kawo Karshen Bude Wuta Tsakaninsu Zata Ruguje
Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...

Falasdinawa Sun Yi Shahada A Hare-Haren Da Sojojin Isra’il Suka Kai Gidan Cin Abinci Da Kasuwa A Gaza
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gidan abinci da wata shahararriyar kasuwa a Gaza Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gidan cin abinci na kasar Thailand da wata shahararriyar kasuwa a yammacin birnin Gaza. Sannan suka ci gaba da kai wasu hare-haren wuce gona da iri kan yankunan zirin Gaza a rana ta 213 a jere. Majiyoyi watsa labarai a Gaza sun rawaito cewa: Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai wani hari kai tsaye kan gidan cin abinci...
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa. Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa...
“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.” Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro. A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a. Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri...
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na tsayawa tsayin daka kan bin ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaici. A nasa bangare, minista Tuggar, ya yi kyakkyawan nazari kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke gudana, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari, da hada-hadar kudi da dai sauransu, da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa a harkokin...
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere. Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da...
A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi. Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.” Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu. Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin...
Sumaila, tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar dokokin kasar, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin “jam’iyyar da ke da rabe-rabe da tabarbarewar al’amura, inda ya ce, rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar a fili yake babu mai musantawa, wadanda suka hada da shari’o’i a kotuna da dama da kuma gwagwarmayar shugabancin jam’iyyar.” A karshe, Sumaila ya kafa uzuri a karkashin doka ta 42, inda ya bayyana godiyarsa ga takwarorinsa da jama’ar mazabarsa, inda ya yi alkawarin kara zage damtse wajen gudanar da ayyukansa na ‘yan majalisu domin yi wa kasa hidima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa, ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga...
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka akan doron jirgin ruwan dakon jiragen saman na ” USS Harry Trauman”. Sanarwar ta kuma kara da cewa; Matuka jirgin sun fice daga cikinsa ta hanar lema, kuma an tserato da su daga cikin ruwa ta hanyar jirgi mai saukar angulu. Matukan, kamar yadda sanarwar ta sojojin na Amurka, sun ji rauni. Wani jami’in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya fada wata kafar...
Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon. Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman...
119-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi, ko cikin cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a cikin shirimmu na yau. ///…Madalla, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujataba (a) da muke kawo maku, mun ji yadda aka yiwa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) bai’a bayana kashe khalifa na uku Uthman bin Affan, munji...

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta don yada tsoro, yada labaran karya, domin samun sabbin mabiya. A saboda haka, ya bukaci ‘yan jarida da editoci da su rungumi dabi’ar kishin kasa wajen bayar da rahoto ta hanyar guje wa kanun labarai masu daukar hankali ga farfagandar ta’addanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya. Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye. Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen ƙaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan ɗabi’u. Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo...
Ya ce, “Na koma jam’iyyar APC ne domin in ci gaba da samun ribar kujerar kakakin majalisar domin ci gaban mazaba ta. “A gare ni, sauya sheka ba batun jam’iyya ba ne, illa don ci gaban mazaba ta, a matsayina na mai wakiltar mutane na, idan na jefar da wannan matsayi saboda jam’iyya, matsayin da zai bunkasa ci gaban yankina, hakan na nufin ban shirya yi wa jama’a aiki ba. “’Yan uwana na majalisa, ina so in sanar da wannan majalisa a hukumance cewa, kakakin majalisar, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya koma APC,” inji shi. Agbebaku ya bayyana cewa ‘yan mazabar sa na goyon bayan matakin da ya dauka, inda ya ce “akwai ayyukan ci gaba...
Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin. “An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,” in ji shi cikin hawaye. Hauwa’u Isa, matar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, ta ce tana wahala da ’ya’yanta uku. “Sun ce za su taimaka mana da adalci, amma har yau babu wani taimako. Ba zan daina fatan samun adalci ba, amma har yaushe za mu jira?” in ji ta. Idan ba a manta ba gwamnonin Kano da Edo, Abba Kabir Yusuf da Monday...
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da ke martani a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure a Nijeriya kan wani allon saƙo da aka kakkafa a Katsina lokacin da Shugaba Tinubu ya halarci auren ‘yar gwamnan. DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan Gwamna Raɗɗa ya ce yana da kyau a riƙa bincike kafin yanke hukunci kan abubuwa. “Na saurari muryar da...
Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam. A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan...
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalar samun tsaftataccen ruwan sha, musamman a karkara, inda mutane da dama ke fuskantar wahala wajen samun ruwan da zai ishe su sha da amfani. Sai dai gwamnatin ta ce ta ƙudiri aniyar magance wannan matsala domin inganta rayuwar al’umma da kare lafiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje. Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da wani kudirin doka da ya soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kaduna ta shekarar 1989, tare da maye gurbin ta da dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli. Kudirin, mai taken “Kudirin Soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna na Shekarar 1989 (Dokokin Jihar Kaduna na Shekarar 1991) da kuma Kafa Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, 2025,” an amince da shi ne yayin zaman majalisar wanda Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya jagoranta. Yusuf Liman ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta bai wa kwalejin damar yin gogayya da sauran manyan cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan, tare da dacewa da tsarin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar sun samu ƙasa da maki 200. Ko waɗanne dalilai ne suke kawo faɗuwa jarabawa a Najeriya? NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan shi ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi...
A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba. Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka. Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na hana satar amsa zai taimaka wajen samar da ƙaimi na ɗalibai masu ƙwazo da amana, tare da ƙarfafa ingancin ilimi a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Iran Ta Ce Ana Yin Nazari Kan Lokacin Gudanar Da Zagaye Na Hudu Na Shawarwari Tsakanin Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai...
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa. Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari...
Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara. Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Ya ce sakamakon bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata. Ya bayyana cewa hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi. Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki sakamakon na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon...
Shugaban tawagar kasar Yemen, Mohammed Abdul Salam, ya sanar da cewa ayyukan Yemen na tallafawa Gaza ba zai tsayawa ba Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba. Ya kara da cewa ikirari da Amurka ta yi na mika wuya, yana nuni ne ga gazawa, saboda Amurka ba zata iya kare jiragen ruwan haramtaciyar kasar Isra’ila daga hare-haren Yemen ba. Abdul-Salam ya kara da cewa: Fahimtar farko da aka samu tsakanin Amurka da Yemen ba ta da wata alaka da matsayar Yemen kan goyon bayan Gaza, yana mai nuni da cewa za a samu ci...
Gwamnatin kasar Indiya ta yi luguden makamai masu linzami kan kasar Pakistan, yayin da Pakistan ta sha alwashin mayar da martani Gwamnatin Indiya ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Pakistan da yammacin jiya Talata, kuma sojojin Pakistan sun sha alwashin mayar da martini, yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin kasashen biyu masu karfin nukiliya. Gwamnatin Indiya ta kai hare-hare da makamai masu linzami guda uku kan wasu wurare a yankin Kashmir da Punjab na kasar Pakistan, yayin da daya daga cikin makaman ya afkawa tsohon filin jirgin sama na Muzaffarabad a yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi. A nata bangaren, gwamnatin Indiya ta sanar da cewa ta kaddamar da...
Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi. Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin...
Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana. A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya. A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna...
Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana. A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya. A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna...
Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ya Kamata Amurka Ta Daina Yin Barazana Da Matsin Lamba Idan Tana Son A Tattauna Batun Harajin Kwastam
Bugu da kari, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nuna godiya da taya kasar Togo murna nasarar kammala mika mulki a siyasance da kuma zaben sabon shugaban kasar da shugaban majalisar ministocinta na farko.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta ARD-FCTA, Dokta George Ebong, da babban sakataren kungiyar, Dr. Agbor Affiong, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnati ta dauka na cire ma’aikatan da abin ya shafa daga cikin tsarin albashi ba tare da sanarwa ko tuntuba ba, inda kungiyar ta ya bayyana matakin a matsayin “rashin gaskiya da adalci”. A cewar kungiyar, ma’aikatan da aka kora da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, masu kula da bangaren magunguna, da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, an yi kuskure ne aka bayyana su a matsayin ma’aikatan bogi ko kuma wadanda basu zuwa aiki, duk kuwa da gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibiti. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya. Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar. Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, yayin da mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita...
Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace. A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa ƙasar Honduras. Tun bayan da Trump ya sake komawa kan kujerar mulki a watan Janairu, ya gindaya sabbin matakai masu tsauri don hana baƙin haure shiga ƙasar. Wasu daga cikin waɗannan matakan na haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda ake amfani da tsofaffin dokokin wanda suke da alaka da zamanin yaƙi wajen aiwatar da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas. Labarin ya kara da cewa ministan yana ganin matsalolin shirin Nucliya da kuma tsaron kasar ba za’a iya warwaresu ba sai ta wannan hanyar. JMI ta dauki wannan hanya ce don ita ce kadai wacce zata kai da gamsuwar ko wani bangare a cikin al-amuran da suke sabani a cikinsu. Aragchi ya fadawa Kallas kan cewa da wannan dalilin ne JMI ta dauki hanyar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da cewa Iran a shirye take a ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar, da sake farfado da yarjeniyar JCPOA ta shekara ta 2015 amma kuma ba zata taba barin hakkinta na mallakar fasahar nukliya da luma sarrafashi a hanyoyin da yarjeniyar NPT ta amince da su ba. Kuma da alamun tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ya daki dutse, saboda sun sami sabani a...
Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata. Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu. Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma...
A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura rukuni na biyu na tawagar a tsakiyar watan Mayu. Kasar Sin ta aike da tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa ta farko zuwa yankin Abyei a watan Mayun shekarar 2024. Tawagar tana dauke da bangarori da dama da suka hada da bangaren tuki, sadarwa, bincike, da kiwon lafiya, wadanda ke yin sintiri da makamai, da kula da wadanda suka jikkata, da kuma...
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon wannan shekarar, don tunkarar zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 25 ga watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki. Kawancen CAP gamayyar jam’iyyun adawa da dama ne na kasar, in banda Jam’iyyar da Lauranta Bagbo a kafa don tunkarar zaben na watan Octoba. Har’ila yau kawancen na zargin hukumar zaben kasar da rashin adalci a yadda take amincewa da yan takara a...
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta fitar da alƙaluman sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda ta bayyana cewa yawancin daliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Litinin. JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200. Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414. A matakin maki tsakanin 250...