HausaTv:
2025-11-08@15:45:11 GMT

 Hare-haren Hizbullah Sun Jazawa HKI A Fagen Gona Asarar Dala Miliyan 108

Published: 7th, May 2025 GMT

Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023.

Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon.

Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman manoma yin hijira.

Bugu da kari, binciken ya ce, barnar da yakin ya haddasa akan gonaki, ya haddasa koma baya a fagen samar da abinci, da kuma kawar da daidaito a kasuwanni.

Shugabar zartarwa ta kungiyar “ReGrow Isra’el” Danil Abraham,  ta sanar da cewa; Barnar da aka samu a kan iyaka da Lebanon tana da girman gaske, da kuma rikiritarwa, ta kuma shafi yanki mai girma fiye da fagen dagar Gaza.

Abraham ta kuma ce; Sai 9000 aka kai wa arewacin “HKI” hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki, da hakan ya sa gonaki masu yawa su ka kone. Haka nan kuma kaso 60% na manoman a Arewacin HKI, sun dakatar da ayyukansu baki daya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
  • Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
  • Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
  • Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
  • Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
  • Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu
  • Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah
  • Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama
  • Sojin Amurka sun gabatar da shirin ƙaddamar da hari a Najeriya
  • Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai