2025-12-07@21:44:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8302
«lafiya»:
Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da...
An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun...
Rahotanni daga Jamhuriyar Benin na cewa am kama wasu 12 bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da jijjibin safiyar Lahadin nan. Tun da farko dama fadar shugaban kasar ta ce har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin. Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin din...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa har yanzu Amurka ba ta nuna sha’awarta ta shiga “tattaunawa mai ma’ana ba,” yana mai sake nanata cewa dole ne Washington ta fara amincewa da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin Yarjejeniyar hana yaduwar Makaman Nukiliya ta (NPT). A...
Kasar Masar ta sake jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da hanyar shiga iyakar Rafah don korar Falasdinawa daga gidajensu ba, tana mai jaddada bukatar sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza. Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da Al...
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
168-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen...
167-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen...
166-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen...
Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji. Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai...
Gwamnatin kasar Rwanda ta rattaba hannu a kan yarjeniya na dalar Amurka miliyon $228 a karkashin sabon tsarin taimako na gwamnatin kasar Amurka. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa kasar Rwanda ta kyautata harkokin kiwon lafiya a kasar ta Rwanda a yayinda tallafin kudaden zai ci gaba a...
Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
Tsohon Shugaban Hukumar Kaɓar Koke-koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama shi. Ya ce an kama shi ne saboda jagorantar shari’ar almundahanar biliyoyin Naira na Dala Inland Dry Port, wadda ta shafi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin...
Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce...
Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce...
Sabon bashin, ya nuna yadda Bankin ya bai wa kasar bashin da ya kai jimlar dala biliyan 5.1 tun daga ranar 31 na watan Okutobar 2025. Kazalika, wannan sabon bashin, zai taimaka wa kashi na biyu na shirin habaka tattalin arziki a bangaren samar da makamashi da sauye-sauye, a fannin makamashin da cimma burin da...
Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar...
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar. Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar...
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...
Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano. A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo. Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take...
Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS. A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban...
Majiyar ma’aikatar tsaron kasar Rahsa ta bada sanarwan cewa garkuwan sararin samaniyar kasar ta kakkabo jiragen Drones na yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar Ukrai har guda 116 a daren jiya kadai. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar ma’aikatar tsaron na cewa, rasha ta kakkabo jiragen 116 ne a yankuna...
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200. Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta...
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin...
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da...
Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani. Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu...
Pars Today – Hanieh Rostamian, jarumar harbin bindiga ta Iran, za ta fafata a wasan karshe na gasar cin kofin duniya. Za a fara gasar cin kofin duniya ta 2025 gobe, Asabar, a Qatar. A cewar Pars Today, tunda manyan ‘yan wasan harbi na duniya suna shiga wannan gasar, Hanieh Rostamian—wanda a halin yanzu yana...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya yi zargin cewa ƙasashen waje na taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda Najeriya. Sheikh Ahmad Gumi ya danganta ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan da irin maganganun da ƙasashen waje suka riƙa yi a kai. A yayin wata hira da BBC Hausa, malamin ya bayyana...
’Yan sanda sun kama tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado. Rahotanni sun nuna cewar wasu ’yan sanda ɗauke makamai ne suka kama shi a ofishinsa da ke Kano, bayan tafka jayayya a ranar Juma’a. Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026 Na kashe...
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026. Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP. Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a...
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare...
Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya...
Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na Naira tiriliyan 12.8 daga watan Agustan 2024 zuwa Oktoba 2025, bisa ga bayanan da Hukumar Kula da Rarraba Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta fitar. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ƙoƙarin ƙara samar da man fetur a cikin gida, duk kuma da...
Pars Today – Vladimir Putin ya yi tafiya zuwa Indiya don ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Vladimir Putin, shugaban Rasha, ya isa New Delhi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba, a ziyararsa ta farko zuwa Indiya tun bayan fara yakin Ukraine a 2022. Ziyarar ta kwanaki biyu na da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin tsaro da...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa kuma tsohon Kantoman jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin Jakadan Najeriya. Tinubu ya kuma naɗa Ita Enang, tsohon sanata da uwargidan tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim da tsohon ministan cikin gida kuma tsohon shugaban rundunar sojin ƙasa Abdulrahman Dambazau, a matsayin jakadun....
Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka...
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda...
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, ba ta shafi batun sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC ba, sai dai a kan shugaban ’yan awaren ƙungiyar Biyafara, Nnamdi Kanu. Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fayyace cewa ziyarar ta biyo bayan...
MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya. Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu. Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka...