Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.

 

A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu.

Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye adalci da daidaito a duniya, da kuma kare ka’idar WTO da tsarin ciniki tsakanin mabambantan bangarori. Har ila yau, ya ce Amurka ita kadai ta tayar da takkadamar haraji, kuma Sin ba za ta yarda da fuska biyu da Amurka ke nunawa ba ko kadan, balle a keta matsayi da ra’ayin da take dauka ko take adalci da daidaito a duniya, don a kai wa ga matsaya daya. (Amina Xu)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasashe Da Dama Sun Amince Da Kafuwar Kasar Falasdinu Yayin Da Amurka Ta Ci Gaba Da Kau Da Kai

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashe Da Dama Sun Amince Da Kafuwar Kasar Falasdinu Yayin Da Amurka Ta Ci Gaba Da Kau Da Kai
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • Sin Tana Maraba Da Kwararru Daga Bangarori Daban Daban Na Kasa Da Kasa Su Zo Kasar
  • Nau’o’in Jirage Uku Sun Kammala Sauka Da Tashin Farko Bisa Taimakon Majaujawar Maganadisu A Jirgin Dako Na Fujian Na Kasar Sin
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • Li Qiang Ya Gana Da Tawagar Membobin Majalisar Wakilai Ta Amurka
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru
  • Kasar Sin Na Son Karfafa Hadin Gwiwar Masana’antu Da Dukkan Bangarori