Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba
Published: 7th, May 2025 GMT
Duk da yadda Amurka ke haifar wa tattalin arzikin duk fadin duniya da barazana da kalubale bisa matakin harajin kwastam da ta kara kakkaba wa sauran kasashen, da yanayi maras tabbas da Sin take fuskanta a waje, ingancin tattalin arzikin Sin yana shaida abun da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, wato tattalin arzikin Sin tamkar teku ne ba karamin tabki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasashen duniya sun damu da rikici tsakanin Indiya da Pakistan
Kasashen duniya na ci gaba da nuna matukar damuwa game da rikicin da ya barke tsakanin Pakistan da Indiya.
Iran na daga cikn jerin kasashen da a baya bayan nan suka nuna damuwa.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce “Jamhuriyar Musulunci ta bayyana matukar damuwarta kan yadda takun saka tsakanin Indiya da Pakistan ke ci gaba da ruruwa.
Iran ta ce a matsayinta na kasa mai iyaka da Pakistan wacce kuma ke da kyakkyawar alaka da Indiya, ta yi tayin shiga tsakani a rikicin tun cikin watan Maris.
Kasar Turkiyya ma ta yi gargadin game da rikicin.
Inda a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa fararen hula da kayayyakin more rayuwa.
A nata bangaren gwamnatin Jamus ta yi kira da a dakile duk wani tashin hankali da kuma kare fararen hula.
Moscow ta yi kira ga kasashen Indiya da Pakistan da su yi taka-tsan-tsan.
Inda ta bukaci bangarorin da su yi taka-tsantsan don kaucewa tabarbarewar lamarin.