Jami’ar Colombiya Ta Birnin New York A Amurka Ta Dakatar Da Karatun Daliban Jami’ar Fiye Da 65
Published: 10th, May 2025 GMT
Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata.
Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran ta nakalto kakakin Jami’ar a jiya Jumma’a na cewa a ranar Laraba yansandan NewYork sun kama talibai kimani 80 inda suke tsare da su, a halin yanzu suke kuma ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Labarin ya kara da cewa akwai wasu karin mutane 33 wadanda Jami’ar ta dakatar saboda hannun a cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawar.
Labarin ya bayyana cewa hotunan bidiyo na tsaro a dakin karatu na Jami’ar sun nuna daliban suna shiga dakin sannan jami’an tsaro suna binsu suna kamawa, sannan wasu daga cikinsu na sanye da ‘Keffiyeh’ wani kelle wanada yake nuna alamar Falasdinawa.
Jami’o’ii da dama a Amurka suna gudanar da irin wannan zanga-zangar, don nuan rashin amincewarsu da kissan kiyashen da HKI take yi a gaza tun shekara ta 2023 ya zuwa yanzu, da kuma tallafa mata wanda gwamnatin kasar ta Amurka take yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Kwace Kudaden Jami’ar Jahar California A Los Angeles Dala Miyon $584 Saboda Falasdinu
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar da gudanar da tarurruka da kuma gangami da zanga zanga na goyon bayan Gaza a jami’ar.
Labarin ya nakalto Dr Julio Frenk shugaban Jami’ar Calfonia a birnin Losangeles na 7th ya bayyana a jiya Laraba kan cewa rike wadannan kudin ba karami matsalace ga Jami’ar UCLA ba, ga kuma kasar Amurka kanta.
Gwamnatin nTrump dai ta bayyana cewa Jami’ar LosAngeles a Califonia, da, Columbia University a New Yrork da Stanford University, da wasu da dama a Amurka suna barin a gudanar da ayyukan na kin yahudawa a cikinsu. Wadanda suka hada da taron gangamin yin All..wadai da HKI da kuma gwamnatin Amurka wacce take goyon bayanta a kissan kiyashin da take yi a Gaza.
Wannan matsalar ta bullowa wadannan jami’o’I ne tun lokacin fara yakin Tufanul Aksa a shekara ta 2023.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya August 7, 2025 Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya August 7, 2025 Kasar Masar Tana Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka August 7, 2025 Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba August 7, 2025 Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Jamus: Shahararrun mutane da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Araqchi Ya Taya Larijani Murnar Zama Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 Japan: An Fara Juyayin Cikar Shekaru 80 Da Harin Amurka Na Makamin Nukiliya A Hiroshima August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci