Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Published: 7th, May 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa.
Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka masu muhimmanci wadanda ma’aikatar harkokin wajen ta aiwatar a cikin wannan lokacin.
Kasashen ya mamma karkashin jagorancin Amurka suka dorawa kasar Iran takumkuman tattalin arziki masu yawa, saboda hana JMI amfani da hakkinta na amfani da fasahar makamashin nukliya, da sunan wai iran tana shirin gina makaman Nukliya.
Don biyan wannan bukatarsu wadannan azzaluman kasashe suka sanya mafi yawan mutanen kasar Iran cikin matsaloli na rayuwa daban-daban. Amma jami’an gwamnatin JMI don tabbatarwa duniya da kuma wadannan kasashe kan cewa ba ta da wani shiri na mallakar makaman nukliya, ta bude tattaunawa da wadannan kasashe na tsawon shekaru biyu, har sai da bangarorin biyu daga ciki har da Amutka, suka cimma yarjeniya ta ganin JMI ta amfana da fasaha da kuma makamashin nukliya wanda yarjenyar NPT ta amincewa ko wace kasa a duniya ta yi amfani da shi. Wannan ya kaiga samar da yarjeniyar JCPOA a shekara 2015.
Inda JMI ta aiwatar da dukkan alkawulan da ta dauka a cikin yarjeniyar. Banda haka hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA ta bada rahoto har 16 kan cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran bai karkata daga yarjeniyar JCPOA ba,
Ana cikin wannan halin ne sai shugaban kasar Amurka mai ci ya hau kan kujerar shugabancin kasar Amurka, ya kuma fidda Amurka daga cikin yarjeniyar a shekara ta 2018, tare da dalilin cewa yarjeniyar bata yi masa ba.
Sai dai a dole JMI ta sake dawowa kan teburin tattaunawa dangane da shirin ta na makamashin nukliya. Sannan ta kara yawan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa JMI, don tursasa mata ta yi abinda take bukata. Banda haka ta sha alwashin sai ta maida cikinin danyen man fetur na JMI a kasuwar duniya ya zama sifir.
Amma bukatar kasar Amurka a lokacin bata ga rana ba har wata gwamnati ta maye gurbinta, sannan a dayan bangaren kasashen turai wadanda tare da su aka kulla yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2015 suma sun saba alkawalunsu a wannan yarjeniyar suka ci gaba da dorawa JMI takunkuman tattalin arziki ba iyaka. Wadanda duk wanda ya nazarcesu zai fahinci cewa suna son faduwar gwamnatin JMI ne. Amma har yanzun basu ga hakan ya auku ba. Kuma da yardar All…ba zasu taba gani ba.
Don haka bayan ficewar Trump daga yarjeniytar JCPOA da kuma sabawa sauran kasashen Turai alkawulan da suka dauka a yarjeniyar, yarjeniyar ta zama babu wani amfani da JMI.
Amma bayan da Donal Trump ya sake komawa Fadar white House a farkon wanan shekara ta 2025 ya sake da ta wannan maganar sannan ya farfado da dukkan takunkuman tattalin arzikin da ya dorawa JMI a shugabancinsa na farko sannan yana kara wasu, daga lokaci zuwa lokaci. A wannan karon har da baraza na farwa kasar da yaki idan ta ki amincewa da sake tattauna shirin nukliyar kasar.
Ganin cewa JMI ta san cewa Amurka musamman Donal Trump ba mai cika alkawali ne ba, sai ta zabi tattaunawa ba kai tsaye ba da ita, saboda yaki zabi ne na karshe.
Don haka aka gudanar da zagaye na farko na tattaunawar a ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata a birnin Mascat na kasar Omman, sannan zagaye na biyu da na uku a ranar 12 da kuma 19 na watan Afrilu a biranen Roma da maskat, amma sai aka dage zaman a 4, wanda yaka mata a gudanar da ita a ranar 26 ga watan a birnin Roma.
Amma dan dan tsakanin nan sai muka fara jin maganganu daga jami’an gwamnatin kasar Amurka na cewa manufarsu ita ce hana JMI sarrafa makamashin nukliya kwatw-kwata, al-hali a zaman tattaunawa guda uku da aka gudanar Amuka bata kawo wannan batun ba. Amma an ji Trump da sakataren harkokin wajensa Rubio suna maganar hana JMI mu’amala da makamashin nukaliya kwata-kwata ne.
Sai dai wannan ketare jan layi ne, ga JMI, don ba zata taba amincewa da hakan ba, ko da za ta ga shiga yaki ne da wadannan kasashe.
Sayyid Abbas Aragchi ya fadawa Kajal Kallas jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na tarayyar Turai kan cewa bangarorin biyu zasu kai ga fahintar juna ne kawai idan dayan baranagren bai gabatar da wani abu wanda ya tabbatar da dayan bangaren ba zai taba amincewa ba. Ko kuma wani abu wanda ba zai taba yiyuwa ba.
Ya kammala da cewa Iran tana da tarjuba na saba alkalin Amurka, don haka idan ta kuskra da shigar da wani abu wanda ta san cewa JMI ba zata amince ba, ba inda tattaunawar zai je.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya kasar Amurka a yarjeniyar
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari
Sai dai, bisa batun gasakiya, karya ce tsagwaronta kan batun kisan kiyashin da ake yamadidin cewa, ana yiwa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya.
Bugu da kari, wannan batun ana wani yunkuri ne na son kawo rudadi a kasar nna, musamman duba da cewa, masu son kawo rudadin, a zahiri, sun jahilci irin yanayin sarkakiyar lamarin tsaro na kasar nan.
Wannan Jaridar, ta sha yin tsokaci, kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar nan, tare da kuma yawan gabatar da kira ga Gwamnatin kasar da ta tashi tsaye, domin daukar matakan da suka dace, na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
Batun aikata ta’addanci, yin garkuwa da mutane da kuma aukuwar rikici a tsakanin manoma da makiyaya, matsaloli ne, da ke shafar kowannen dan Nijeriya, wanda kuma Trump da masu ba shi shawara, suka jahilci hakan, musammman duba da cewa, akasarin wadannan matsalalin, na aukuwa Musulmi da Kirista ne.
Wani abin duba wa a nan shi ne, akasarin hare-haren ‘yan ta’addara Boko Hrama na kai wa kan Musulmi da ke Arewacin Nijeriya, wanda Trump, ya kafa hujar da cewa, ana kashe Kiristoci ne, inda kuma hare-haren, suka nuna cewa, anfi hallaka Musulmai, fiye da Kiristoci.
Ayyana matsalar tsaron kasar da Trump ya yin a yi wa Kiristoci kisan kare dangi wani abu ne, da yake da matukar hadari.
Martanin da shugaba Bola Tinubu ya mayarwa da Trump kan wannan ikirarin na sa, abu ne da ya dace, musamman cewar da ya yi a Nijeriya ana bai wa kowanne dan kasar, ‘yancin yin addininsa, ba tare da wata tsangwama ba, musamman kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar, ya tanadar.
Bugu da kari, idan har Trump na nuna damuwa kan ikirarinsa na ana yi wa Kiristocin kasar kisan gilla, to su kuma Kiristocin da aka hallak a zirin Gaza biyo bayan hare-haren kasar Isra’ila fa?
Kuma mai ya sa ba zai yi amfani da karfin ikon gwamnatinsa na dakatar da yakar kasar Ukraine, da kasar Rasha ke ci gaba da yi ba, duba da yadda aka kashe dubban Kiristoci a kasar?
Amsar a nan ita ce, Trump ba wai na da nufi bai wa Kiristocin kasar nan kariya bane, wani bakar manufa ce kawai da yake son cimma burinsa.
Tarihi ba zai sanya mu yi saurin manta wa da mamayar da Amurka ta yiwa kasar Afghanistan a 2001 ba don kifar da gwamnatin Taliban wadda ta alakantan, a matsayin ‘yan ta’adda.
A lokacin mamayar, sama da mutane 200,000 ne, suka rasa rayukansu, amma duk da hakan, Taliban ta sake dawo wadda a yanzu, ta ke ci gaba da jan ragamar shugabancin kasar.
Kazalika, Amurka ta mamaye kasar Iraki a 2003, ta cere shugaban sojin kasar kasa marigayi Saddam Hussein, inda sama da mutane 150,000 suka rasa rayukansu sabo da hare-haren Amurka.
Hakazalika, ta kai wata mamayar a kasar Lbiyia ta cere marigayi Gaddafi, wanda har yanzu, kasar ba ta saitu ba, inda kuma burbushin yakin na Lbiya ya haifar da shigar makamai cikin kasar nan da ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga daji da kuma wasu Fulani ke yin amfani da su, wajen kai hare-hare a Nijeriya.
Yin amfani da karin soji da Amurka ta yi barazanar yi kan Nijeriya ba sanya matsalar tsaron kasar nan, ta kau ba, sai dai ma, kara tabarbarar da tsaron kasar.
Idan har da gaske Amurka ta ke yi na taimaka wa Nijeriya ta magance kalubalen rashin tsaronta ba ta hanyar barazana ya kamata ta bullowa kasar ba, kamata ya yi ta taimaka wa Nijeriya da kudade da makamai domin kawo karshen matsalar da kuma yin musayar bayanan sirri.
Amma yi wa Nijeriya wannan barazar, tamkar wani cin fuska ne.
A zahiri barazanar ta Trump, ba wai yana nufin bai wa Kiristocin Nijeriya kariya bane, amma wani salon na ne kawai na son nuna karfin iko da kuma son kawo rabuwar kanuwanan ‘yan Nijeriya.
Ya kamata Trump ya mayar da hankali kan matsalolin da ke ci gaba da addabar kasarsa ne, ba wai yin shiga sharo ba shanu, kan batun da ya shafi Nijeriya ba.
Sai dai, a nan za mu iya cewa, wannan barazar ta sa, dole ne ta zama wata ankawarar ga masu rike da madafun iko a kasar nan, wajen lalubo da mafita kan matsalar tsaro da kasar da kasar ke ci gaba da fuskanta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA