Da yake tsokaci game da wasan na karshe na jiya, Mark Williams daga yankin Wales, ya ce Zhao abokin karawa ne mai hazaka. Don haka ba abun da zai fada game da shi illa jinjinawa. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.

Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ajax ta kori kocinta John Heitinga

Kungiyar kwallon ƙafa ta Ajax da ke ƙasar Netherlands ta sanar da sallamar kocinta, John Heitinga, a sakamakon rashin kataɓus da a yanzu ƙungiyar ta maƙale a ƙasan teburin gasar Zakarun Turai ta Champions League.

A wata sanarwa da ta Ajax ta fitar a ranar Alhamis, ta ce tana neman sabon koci, inda a halin yanzu, Fred Grim zai riƙe aikin Heitinga har zuwa lokacin da za a naɗa sabon mai horarwa.

Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8

Heitinga, wanda ya sanya hannu kan kwantiragi na shekaru biyu a watan Mayu, ya gaza sauya akalar ƙungiyar, lamarin da Ajax ɗin ta tabbatar cewa ta kawo ƙarshen yarjejeniyar.

Daraktan fasaha na kulob ɗin, Alex Kroes, ya bayyana cewa wannan mataki “yana da raɗaɗi”, amma ya ce ya zama dole don ci gaban ƙungiyar.

“Mun san yana ɗaukar lokaci kafin sabon koci ya daidaita tawagar da aka yi mata zubin sabbin ‘yan wasa. Mun ba John wannan damar, amma yanzu mun ga ya dace mu naɗa wani sabon mutum,” in ji Kroes.

Mummunan sakamako na ƙarshe shi ne rashin nasarar da Ajax ɗin ta yi har gida a hannun Galatasaray a gasar Champions League, wadda ta doke ta 3-0 a ranar Laraba. Wannan na zuwa ne bayan da kwasar kashinta a hannun da ta yi yayin da Chelsea ta doke ta 5-1 a baya.

Haka kuma, Ajax ta sha kashi a hannun Marseille wadda ta doke ta 4-0, sai kuma ci 2-0 a hannun Inter Milan, lamarin da ya sa ta gaza samun ko da maki ɗaya a babbar gasar ta Turai.

A lig ɗin gida kuwa, Ajax tana matsayi na huɗu a teburin Eredivisie, da tazarar maki takwas tsakaninta da Feyenoord da PSV Eindhoven.

Magoya bayan kulob ɗin sun yi zanga-zangar rashin jin daɗi saboda yawan sauye-sauyen da Heitinga ke yi yayin wasanni, yayin da wasu ke ganin lokaci ya ƙure masa.

Sai dai ƙungiyar magoya bayan Ajax ta bayyana rashin jin daɗi bisa korar Heitinga, tana mai cewa: “Duk abin da muke so shi ne mu ga Ajax tana samun nasara, saboda haka rabuwa juna ba zai kai ga nasara ba.”

Heitinga dai tsohon ɗan wasan Ajax ne da ya buga wa ƙasarsa Netherlands wasanni 87.

Haka kuma, ya taɓa murza leda a Atletico Madrid, Everton da Fulham.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
  • Dan Wasan Taekwando Na Kasar Iran Abulfazl Zandi Ya Zamo Shi Ne Na Daya A Duniya
  • Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko
  •  Jirgin Kasan Dakon Kaya Na Farko Daga Rasha Ya Iso Kasar Iran A Yau Asabar
  • Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
  • Ajax ta kori kocinta John Heitinga
  • A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu
  • Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
  • Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja