“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.”

 

Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro.

A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a.

 

Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri don dakile matsalolin tsaro.

 

Gwamna Buni ya kara da cewa, “Dole mu hada kai mu yi aiki tare, tsakanin jami’an hukumomin tsaro wajen bayar da gudummawa tsakanin rundunonin tsaron Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Ce Ana Yin Nazari Kan Lokacin Gudanar Da Zagaye Na Hudu Na Shawarwari Tsakanin Iran Da Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.

Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai dangane da haka da zarar an tantance lokaci da wuri.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Har yanzu ba a sanya ranar karshe da za a gudanar da shawarwarin na gaba ba, amma ana duban shawarar da Oman ta gabatar na gudanar da tattaunawar a farkon mako mai zuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jakadan Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Najeriya
  • Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Tattaunawar Cinikayya Da Za A Yi Tsakanin Babban Jami’inta Da Na Amurka
  • Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum
  • Nijar Ta Soke Yarjejeniyar Tattara Bayanai Da Rasha Da Turkiyya, Ta Fara Neman Sabbin Abokan Hulɗa
  • Iran Ta Ce Ana Yin Nazari Kan Lokacin Gudanar Da Zagaye Na Hudu Na Shawarwari Tsakanin Iran Da Amurka
  • Gwamnan Bauchi Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Banga A Alkaleri
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu
  • Yadda ’yan fashi suka yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi
  • ’Yan fashi sun yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi