2025-06-15@09:05:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 195
«kawo karshen»:
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa. Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa...
Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki. Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban. Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki. “Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya. “Martabar...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi da wani dalili da ya wuce a rufe bakin gaskiya wanda yake taimakawa al’ummar Falasdinu a Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, haka nan kuma taimakawa da goyon bayan gwgawarmayar Lebanon da dukkanin wannan yankin. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Wannan harin da wuce gona da irin za iyi tasiri mai girma a cikin wannan yankin, sannan ya kara...
Wani mummunan hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya ya yi sanadin mutuwar mutum takwas ’yan gida daya, yayin da wasu mutum biyu ke can kwance a asibiti rai a hannun Allah. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin a garin Barakallahu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, ana tsaka da bukukuwan Babbar Sallah. A cewar rahotannin, lamarin ya faru ne lokacin da wata mota da ke tsala gudu ta kwace sannan ta danne mutanen da ke tsaye a gefen hanya bayan dawowarsu daga yawon sallah. Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India A cewar mahaifin mamatan,...
Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu. A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin. Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Wasikar wacce ke dauke da sa hannun...
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga kasar Mali, abin da ya kawo kƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a wannan kasa ta Yammacin Afirka. “Mun taimaka wa ‘yan kishin kasa wajen gina wata rundunar sojoji mai karfi da tsari, wacce za ta iya kare kasarsu. Dukkan manyan biranen yankin sun koma karkashin ikon mahukuntan da ke da ikon tafiyar da harkoki a kasar,” in ji Wagner. Kasar Mali, da ke yankin Sahel, ta sha fama da hare-haren ‘yan tawaye tun daga shekarar 2012, kuma sojojin dake mulki a kasar sun nemi taimakon Rasha bayan sun katse dangantaka da Faransa da sauran abokan hulda. A farkon wannan shekarar, kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, da...
Kasar Ghana ta kawo karshen goyon bayan da take bawa kungiyar Polisario, sannan ta dawo tana goyon bayan kasar Morocco a kan wannan rikicin. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa, an kafa kungiyar Polisario ne a shekara 1979. Sannan rikicin Polisario yana komawa zuwa shekara 1975 a lokacinda turawan Espania yan mulkin mallaka suka fice daga yankin sai suka hadda fada tsakanin Polisario da kasashen Morocco da kuma Mauritania. Kungiyar dai tana samun goyon bayan kasashe kimani 80 a duniya, amma kuma a hankali-a hankali tana rasa goyon bayan da take da samu a duniya, na karshensu it ace kasar Ghana.
A wasu lokuta, matsalolin suna fitowa kai tsaye sakamakon rashin fahimta daga mataki na kasa, wadada a wasu lokutan ba su da wata alaka da sakatariyar jam’iyyun da ke mataki na sama. Ko a cikin jam’iyyar APC da ke mulki, akwai jayayya a cikin rassan jihohinta da ba su warware ba kuma suna barazanar ga damar jam’iyyar a jihohin da abin ya shafa. Wasu masana harkokin siyasa sun bayyana cewa rarrabuwar kawunan ta samu ne sakamakon nuna iko tsakanin wasu mutane a wasu jihohi. Akwai batun wanda ke da iko da tsarin jam’iyyar shi ne shugaban jam’iyyar a jihar. Yayin da wasu ke cewa wannan shi ne tushen da ya haifar da rarrabuwar kawuna da ke faruwa a cikin tsarin...

Limamin sallar Idi Al-Adha A Tehran Ya Jaddada Cewa: Imam Khomeini {r.a} Ya Kawo Sauyi Da Ci Gaba A Iran
Limamin da ya jagoranci Sallar Idi Al-Adha a Tehran ya bayyana cewa: Imam Khumaini (r.a) ya kawo sauyi mai girma da fadi a Iran Limamin da ya jagoranci Sallar Idin Al-Adha a birnin Tehran Hujjatul-Islam Hasan Abu Torabi Fard ya bayyana cewa: Imam Khumaini (r.a) ya share fagen kasancewar al’ummar Iran a fagage mafi muhimmanci na yanke shaawara, sannan kuma ya ba da damar samun gagarumin sauyi mai girma a Iran. Hujjatul- Islam Abu Torabi Fard ya kara da cewa: Muna tunawa da rasuwar wani fitaccen mutum kuma fitaccen mutum wanda ya taso kuma aka rene shi a cikin mazhabar hankali da ilimi da tauhidi na ubangijinmu Ibrahim Majibin Rahma (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Ya ci gaba...
“Idan za ku yi adalci a gare mu, a cikin makonni biyu da suka gabata, za ku ga cewa sojojin suna samun nasara wajen karya lagon ‘yan ta’adda, inda suka kashe su tare da tarwatsa sassaninsu,” in ji ministan. A karshen makon da ya gabata, wadanda ake zargi ‘yan ta’adda na Boko Haram sun dasa na’urorin fashewa a Unguwar Guzamala na Jihar Borno, inda suka kashe mutane tara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran. Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango. Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren gas da man fetur. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe dala $ 5bl daga cikinsu. Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don...
Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka. Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da...
Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata. Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Tinubu ta kaddamar ta ofishin mataimakin shugaban kasa a cikin shekaru biyu da suka gabata: Noma Ta bayyana karara tun farkon shekarar 2025, lokacin da Shugaba Tinubu ke neman mukamin shugaban kasar nan, cewa noma ne zai zama babban abin da gwamnatinsa za ta sa a gaba. Ba abin mamaki ba ne ganin shugaban kasa ya cika wannan alkawari. Gwamnatin ta tsara wani tsari na zaburar da sake inganta harkar noma, kamar yadda a cikin shekaru 60 lokacin da Nijeriya ke da dala na gyada a Arewa, da koko a yamma da kuma dabino a gabas. Sannan Nijeriya ta samu isashshen abin da za ta ciyar da al’ummarta da kuma fitar da...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Taron Kungiyar BRICS Zai Kawo Bunkasar Tattalin Arziki
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Taron kungiyar BRICS wata dama ce ta bunkasa alaka mai karfi ta tattalin arzikin duniya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Halartar tawagar wakilan majalisar dokokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a zauren majalisar dokokin BRICS wata dama ce mai kima ta bunkasa alaka da kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya da kuma fuskantar takunkumi. A wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Asabar kafin ya tashi zuwa wasu kasashen Latin Amurka uku da kuma halartar taron majalisar dokokin kasashen kungiyar BRICS, Qalibaf ya ce: Za su zagaya kasashen Latin Amurka, inda zasu fara da kasar Venezuela, bisa gayyatar da shugaban majalisar dokokin kasar...
Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata, sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa motar da ke ɗauke da ‘yan wasan, wadda ke ɗauke da mutane 30, ta faɗa gadar ta Dakatsalle da ke jihar ta Kano. “Yayin da nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwaki 19,” ya fada cikin tashin hankali. Ado Salisu, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida da ke kula da lamuran Wasanni ta Najeriya (SWAN), ya ce an kai...
Mazauna Babban Birnin Tarayya za su fuskanci katsewar ruwan sha na tsawon makonni biyu, kamar yadda Hukumar Kula da Ruwa ta yankin ta sanar. Rashin ruwan, wanda ya fara ranar Juma’a, 30 ga Mayu, ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar Juma’a, 13 ga Yuni. Matsalar ta samo asali ne daga ayyukan gyare-gyare da ake yi a tashoshin tace ruwa na madatsar ruwa ta Lower Usuma Dam. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, gyare-gyaren sun shafi muhimmin aikin haɗa kayan aikin lantarki da injiniya, wanda babban bangare ne na aikin inganta matatar. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno...

Macron : Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba
Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza. A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa su “tsaurara matsayinsu na hadin gwiwa” kan Isra’ila, “idan babu wani mataki da ya dace da yanayin jin kai, a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa” a zirin Gaza. Macron ya ce, “Katange ayyukan jin kai yana haifar da yanayi mara kyau,” yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Singapore Lawrence Wong. Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki. A cewar Gwamnan, bankuna da dama sun tunkare shi suna neman ya ci bashi amma ya ki saboda ba ya so ya ci gaba da dilmiyar da jihar a kangin bashi. Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su Gwamnan ya ce a maimakon haka, ya ma rage kudaden alawus-alawus na Sakataren Gwamnatin jihar da...
Kazalika, tashar teku ta Duisburg dake kasar Jamus ta kasance cibiyar sufurin layin dogo a tsakanin Sin da yammacin Turai, inda yawan kwantenonin da ake hada-hadarsu a tashar duk shekara suka kai miliyan hudu. Bugu da kari, sufurin layin dogo da ya sada Sin da Turai ya kara bude hanyoyin zuba jarin kamfanonin Sinawa a Duisburg. Sannan ana ci gaba da inganta sufurin dogo ta hanyar sabbin tsare-tsaren da ake kawowa kamar su na jirgin Tea Train da na dakon motocin sabbin makamashi da ake fitarwa zuwa waje, watau New Energy Vehicle Export Train, domin raya cinikayyar Sin da Turai. Har ila yau, layin dogo na Budapest zuwa Belgrade da ya sada kasashen Serbia da Hungary mai kusan tsawon kilomita...
Bayan an bari Amer, ya shiga jirgin, suka kama hanyarsu ta tafiya har suka sauka lafiya wanda hakan ya sa ma’aikatan jirgin suka ɗauki hoton da shi don tarihi, inda a ɗayan ɓangaren mutane da dama ke suffanta lamarin a matsayin hujjar ƙarfin niyya da ikon Allah. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Francesca Albanese tana fadar haka a shafinta na X a jiya Litinin. Ta kuma kara da cewa an kashe mutane da yawa, kuma an kashe yara da yawa. An kona su da ransu, a cikin makarantar inda suke mafaka a ciki. Albanese ta hada da hotunan bidio wanda suke nuna irin yadda wuta take kona Falasdinawa a cikin makarantar, ta turasu a shafin nata....
Shugaban kasar Iran wanda ya karbi bakuncin Fira ministan Pakistan da marecen jiya Litinin, ya bayyana cewa; Kasar Pakistan, makwabciyar jamhuriyar musulunci da muhimmanci, ta dubban shekaru. Shugaban kasar ta Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda yake Magana a lokacin taron manena labaru na hadin gwiwa da Fira ministan na Pakistan, ya kuma ce; Da akwai haduwar mahanga a tsakanin kasashen biyu akan batutuwa masu yawa da su ka shafi wannan yankin da kuma duniyar musulunci da kuma a fagen siyasar kasa da kasa.” Shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya kuma ce: “A yayin ganawar da mu ka yi da dan’uwana Fira minisan Pakistan da tawagar da taek tre da shi, mun jaddada yadda za a bunkasa alaka ta siyasa, tattalin arziki da al’adu.”...

Masu Zanga-Zanga A Mafi Yawan Kasashen Turai Sun Bukaci Kasashen A Kawo Karshen Kissan Kiyashi A Gaza
Dubban daruruwan masu zanga-zanga a biranen Barlin Paris da kuma Stockholm ne suka bukaci gwamnatocin kasashensu su kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a gaza, su kuma tabbatar da cewa abinci ya isa gaban Falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga-zangar sun kira ga gwamnatocin kasashensu su dakatar da bawa HKI makaman da take kishe falasdinawa da su. A birnin Berlin da kasar Jamus dubban Jamusawa sun hadu a dandalin at Oranienplatz inda suke rera taken ‘a bawa Falasdinawa yenci, HKI yar ta’adda ce, kuma gwamnatin Jamas ta dakatar da tallafin da take bawa HKI. Labaran sun kara da cewa hatta mutanen kasar Jamus yan asalin yahudawa sun fito sun bayyana...
Mutanen kasar Lebanon sun gudanar da zabubbukan larduna a kudancin kasar a ranar Asabar da ta gabata duk tare da barazanar tsaron da kasar take fama da sun\ Jiragen yakin HKI sun ci gaba da yin luguden boma bomai a kudancin kasar Lebanon duk tare da yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da suka cimma da kungiyar hizbulla a karshen shekarar da ta gabat. Kafafen yada labarai sun nakalto mutane suna zabe a garin Jwayya kilomiya 15 kacal kan iyaklar da kasar Falasdinu da aka mamayae. Sunce bas a jin tsoron HKI zata kawo hirik o ba zata kawo ba saboda zabe wajibinsu ne .
Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so. Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu. Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen laifukan da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan fage da Amurka akan Shirin kasarsa na Nukiliya, ya ziyarci fadar Vatican, inda ya gana da ministanta na harkokin wajen Cardinal paul Gallagher, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Fafaroma Farancis sannan kuma da murnar zabar sabon Fafaroma Leo na 14 Abbas Arakci ya yi wa shugabannin fadar ta Vatican bayani akan matsayar Jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, da...
Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa an kawo karshen cutar shan inna, mai nakasa yara a Madagascar. Tun daga shekara ta 2020, tsibirin ke fuskantar karuwar nau’in cutar shan inna na 1, da har yanzu ke yaduwa. Wakiliyar UNICEF a Madagascar, Christine Jaulmes, ta yi farin ciki da matakin. UNICEF ta ce manyan matakan gwamnati, ciki har da hukumomin gargajiya da masu aikin sa kai a kasar ta Madagaska sun taimaka gayan wajen kawar da cutar ta inna ko kuma Polio. Masu ruwa da tsaki a kasar sun bukaci da kada a yi watsi da matakan da ake dauka na dakile cutar a sahun gaba da kamfen allurer kafin cutar da ake gudanarwa lokaci zuwa lokaci. A shekarar...
Wani jami’in hukumar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa tsare-tsaren da hukumar ta ɗauka sun taimaka sosai, inda komai ke tafiya cikin kwanciyar hankali a Saudiyya. An fara jigilar maniyyatan ne a ranar 9 ga watan Mayu 2025 a filin jirgin sama na Owerri da ke Jihar Imo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen duniya 22 sun bukaci Isra’ila da ta gaggauta dawo da cikakken tallafin da take baiwa zirin Gaza. Tireloli tara na taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ne aka ba su izinin shiga zirin Gaza a ranar Litinin, wanda ake wa kallo a matsayin digo ‘’ digo a cikin teku,” in ji shugaban kula da ayyukan jin kai na MDD, Tom Fletcher. Al’ummar Zirin Gaza suna “fuskantar yunwa” kuma “dole ne su sami taimakon da suke bukata,” in ji ma’aikatun harkokin waje na kasashen Australia, Canada, Denmark, Estonia, Finland, Faransa, Jamus, Iceland, Ireland, Italiya, Japan, Latvia, Lithuania, Luxembourg, Netherlands, New Zealand, Norway, Portugal, Slovenia, Spain, Sweden, da United Kingdom. Kasashen da suka rattaba hannu kan bukatar sun ce, “Bai...
Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan a zirin Gaza, yana mai kira da a kawo karshen kisan kiyashi da rashin hukunta shugabannin gwamnatin ‘yan shayoniyya da kuma gurfanar da su a gaban kuliya don hukunta su. Baqa’i ya yi ishara da laifuffukan da ba a taba ganin irinsa ba da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi kan al’ummar Falastinu da ba su da kariya a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ya...
“Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi. Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.” Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu. “Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban...
Dangane da sake fasalin dokar zabe, shugaban hukumar INEC, ya ce hukumar na yin cudanya da majalisar dokokin kasar, inda ya ce makwanni biyu da suka gabata, ta yi wani taro a Legas tare da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan sake fasalin zabe. “Majalisar dokoki ta kasa za ta shirya taron jin bahasin jama’a, bayan nan za a samar da kudirin doka, a karshen zancen za a mika wa shugaban kasa domin sanya hannu,” ya shaida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan. Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa. An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu ƙirar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Bikin ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin. Ya ce Najeriya na...
Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato. A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa. Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kai hari kan kasuwar ce mai tara ɗaruruwan mutane da ke zuwa daga gari-gari makwabtaka domin baza hajoji iri-iri musamman kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, fulawa, wake, lemuka da sauransu. Shafi’i Sambo, wani shugaban matasa...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane. Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka —...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana. An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan...

Yemen Ta Jaddada Cewa: Idan Amurka Ta Kai Mata Hari, Tabbas Yarjejeniyar Kawo Karshen Bude Wuta Tsakaninsu Zata Ruguje
Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...
Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200. “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan. Don haka, a da muna da likitoci 96, amma bayan karin albashin da gwamnan ya yi, uku da suka bar aikin sun dawo. Saboda haka, a halin yanzu muna da likitoci 99. Kazalika, muna da bukatar kari, domin kuwa kimanin likitoci 180 zuwa 200 muke bukata.” Saboda haka, hukumar ta ce; tana kokarin samar da wata manhaja da za ta bai wa marasa lafiya,...
Ta ce: “Zargin da aka yi na cewa na shirya ficewar matan daga bikin Uwargidan Gwamna a ranar 2 ga Mayu 2025, karya ce kawai. Ba ni da hannu a cikin wannan lamirin kuma wannan ƙarya ce ta masu tada hankali. “Na kasance na mai da hankali ne kan karatuna na digiri na uku a lokacin da aka dakatar da ni, ba tare da shiga cikin wani yunkuri ba. Ina kira ga duk masu ruwa da tsaki su taimaka wajen inganta zaman lafiya a jihar.” Ta kara da cewa ta kasance tana aiki don ci gaban jihar kuma ta bukaci mutane su guji yada jita-jita maras tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Likitoci wadanda basa goyon bayan kissan kare dangi wanda HKI tare da taimakon Amurka suke yi a Gaza, sun fito zuwa majalisar dokokin kasar Capotol tare da bukatar a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa likitocin sun bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta kawo karshen kissan kare dangin da ke faruwa a gaza, kuma a gaggauwa kawo karshen kissan falasdinawa da kuma bude kofofin shigar da agaji zuwa cikin yankin. Inda miliyoyin Falasdinawa daga ciki har da yara miliyon guda suke mutuwar yunwa ga kuma kissa da makami ta sama.
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi. Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na 11 da ya gudana a Jalingo. Shugaban SSANU ya dage cewa ya kamata a yi wa ’ya’yan kungiyar adalci, domin wadanda ba aikin koyarwa ba na daga cikin bangarori hudu da suka kafa jami’a. Sai dai ya yi gargadin cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani memba da ya sabawa ka’idojin jami’a ba. Tun da farko, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka,...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali. Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai. A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita. Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu....
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba. A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.” Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.” Watanni 9 da su...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya. Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka. Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje. (Mai fassara: Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel. Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji. A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas. Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi...
Bugu da kari, game da amincewar da gwamnatin shugaba Trump ta yi da aikin hako ma’adinan karkashin teku, Guo Jiakun ya ce ba wata kasa dake da ikon karya dokokin kasa da kasa a wannan fanni, ta yadda za ta iya keta dokokin bincike, da bunkasa ayyukan hako ma’adinan karkashin teku ba bisa ka’ida ba, domin kuwa hakan zai haifar da illa ga moriyar daukacin al’ummun kasa da kasa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
”Wannan lokaci ne na bakin ciki, kuma a cikin irin wadannan lokutan ne kuka san wadanda ke kulawa da ku da gaske.” Ribadu ya bayyana cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tashin hankali da ke fama da shi a kasar nan, kuma tana aiki tukuru don gyara abubuwan da suka lalace. Ya ce, “Na zo nan ne don in jajanta muku da sauran mutanen kirki na Benuwai kan asarar rayuka da aka yi da kuma tabbatar muku da cewa muna tare da ku. “Benuwai jiha ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya. Ta kasance daya daga cikin jihar da ake samar da abinci a kasa, ita ce ta farko wurin samar da abinci, kuma muna alfahari da hakan....
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara. Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashe a jihohin da abin ya shafa. “Ya isa haka,” in ji Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin tir da kai hari ga ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba. Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa cikakken bayani kan halin da...
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC “Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi. Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa. Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya...
Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin. Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar...
A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa. “Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin. Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun fara komawa harkokinsu na yau da kullum. “Muna gode wa sojojin bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa,” inji shi. Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a Buni Yadi ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a game da buƙatar ƙarin tsaro a yankin. Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta tura ƙarin sojoji don hana faruwar irin...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga. Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi. Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Yayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi....
“Mun zo nan ne a madadin gwamnatin tarayya domin ganowa da kuma jajanta muku rashin da aka yi, muna so mu tabbatar muku da cewa jami’an tsaro za su kawo karshen wannan kashe-kashen na rashin hankali. “An yi mini cikakken bayani, kuma ina so in tabbatar muku cewa mun fahimci tushen wannan batu. Zamu kama wadanda suka aikata wannan aika-aika. “Shugaban kasa ya damu matuka, kuma ya umarce mu da mu nemo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci shari’a, muna aiki tare da gwamnatin jihar domin daukar tsarin da zai hana faruwar wannan mummunan lamari, lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan hauka,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar. Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”...
Kasar Yemen ta sanar da cewa: Amurka ta kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan garuruwan Sana’a, Sa’dah, da Al-Jawf Mahukuntan Yemen sun sanar da cewa: Amurka ta ci gaba da kai hare-hare kan kasar Yemen, inda ta kaddamar da wasu jerin hare-hare kan garuruwan Sana’a, Sa’dah da Al-Jawf. Wakilin Al-Alam ya ruwaito a yammacin jiya Juma’a cewa: Jiragen saman yakin Amurka sun kaddamar da hare-hare har sau shida a gundumar Bani Hushaysh dake arewa maso gabashin birnin Sana’a fadar mulkin kasar Yemen, inda suka yi luguden wuta a wurare da dama. A lardin Al-Jawf, an kai wasu hare-hare 4 ta sama a gundumar Bart Al Anan da yankin Al-Yatmah da ke gundumar Khab da gundumar Al Sha’af...
Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom. Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata...
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mayar da dan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar, Shamsudeen Hassan Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Arewa, bayan da ya nemi gafarar majalisar. Hakan ya fito ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Bello Madaro ya raba wa manema labarai a Gusau. A zaman da aka yi, Kakakin Majalisar, Alhaji Bilyaminu Ismail Moriki, ya karanta abin da ke cikin wasikar neman afuwar Basko, inda daga nan ne ya nemi shawarar majalisar ta gamayya inda ‘yan majalisar suka amince da dage dakatarwar. Shugaban majalisar ya jaddada bude kofar majalisar na karbar irin wasikun neman afuwa daga sauran ‘yan majalisar bakwai da aka dakatar, inda ya ce irin wadannan...
Ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dawo gida nan take domin tunkarar matsalar rashin tsaro da ke ƙara ƙamari. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a jihohin Filato, Zamfara, Borno da wasu sassan ƙasar. Shugaba Tinubu ya tafi Faransa a ranar 2 ga Afrilu don “tafiyar aiki” na makonni biyu. Daniel Bwala, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Manufofi, ya ce tafiyar na da nufin yin yin bitar tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da kuma sauye-sauyen, gabanin cikar shekaru biyu na gwamnatin. A cikin saƙonsa na ranar Laraba, Obi ya ce ya zama...
Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu. Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a Kano Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa. Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na yin garambawul a fannin kiwon lafiya ta hanyar sanya tubalin gina sabbin cibiyoyin lafiya guda uku, da suka hada da Cibiyar Gwaji ta zamani, da Cibiyar kula da lafiyar Zuciya, da cibiyar samar da iskar numfashi (Cryo-Oxygen Plant) a Fanisau, da ke Dutse, babban birnin jihar. Wadannan ayyuka, wadanda za su ci biliyoyin nairori, wani bangare ne na hangen nesan gwamnatin na mayar da Dutse cibiyar yawon bude ido kan kiwon lafiya a yankin. A yayin bikin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana ta shiga kundin tarihi a ci gaban jihar. Ya bayyana cewa an tsara wadannan cibiyoyin ne domin kara karfin jihar wajen samar da ingantaccen...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga al’ummar duniya da su ba da himma wajen shiga wani gangami na tsawon mako guda domin ganin an kawo karshen mummunan yakin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yi wa kawanya. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, Hamas ta yi kira ga “kasashen Larabawa da na musulmi da kuma ‘yantattun mutane” na duniya da su halarci gangamin na ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi (18, 19 da 20 ga Afrilu). Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta ayyana wadannan ranaku a matsayin “ranakun nuna fushin duniya dangane da mamaya.” Hamas ta sake nanata bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa don kawo karshen “ci gaba...
Gwamnatin Amurka ta amince da shirin mikawa HKI dubban boma-bomai saboda kashe falasdinawa a Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, sojojin HKI suna jiran isowar boma-bomai daga kasar Amurka don fara wani aikin soje na musamman a Gaza. Saboda kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Wata majiyar HKI, yahudawa ta fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Ynetnews’ kan cewa sojojin sama na HKI su na dakon isowar boma-bomai har 3000 daga kasar Amurka a cikin yan makonni masu zuwa. Labarin ya kara da cewa rundunar ta na son ta gudanar da ayyukan soje mai fadin gaske a kan Falasdinwa wanda ya zai kawo karshen Hamas ya kuma kawo karshen samuwar Falasdinawa a yankin. Labarin ya kara...
Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya. A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan. A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra’ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa. Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno A cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525...

Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya. A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba. Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan...
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...

Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Jihar
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata. Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa. Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa. Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu. “Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba...
Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci, har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa. Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin. A ranar lahadin da...

Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu. Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza. Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can....
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya lashe zabe da kawo 90.35% kamar yadda sanarwar ma’aikatar cikin gida ta sanar. Brice Nguema ne dai ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Ali Bango a watan Ogusta na shekarar 2023, ya kuma shiga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar a wannan zaben. Dan takara na biyu da yake binsa a baya, shi ne Alain Claude Bilie Bie Nze da ya sami kaso 3.02% na jumillar kuri’un da aka kada. An sami halartar kaso 70.4% na jumillar wadanda su ka cancanci kada kuri’a da ya zama mai muhimmanci da zai kawo karshen mulkin rikon kwarya na soja. Zaben na wannan lokacin shi ne irinsa...
Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI. Amma sojojin sun kammala da cewa a...
Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Sakkwato ta yi barazanar sanya ƙafar wando da waɗanda ta yi zargi suna ƙoƙarin kawo mata cikas a yaƙin da take yi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Jihar. Ta gargaɗi mazauna da su shiga taitayinsu game da yin kalamai da za su iya kawo cikas ga ƙoƙarinta na magance matsalar rashin tsaro a jihar. Wannan gargaɗin ya biyo bayan wata sanarwa da ake dangantawa wani mai suna Basharu Altine Guyawa wanda ya yi ƙoƙarin nuna cewa gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba a fannin tsaro. Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yi wannan gargaɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a...
Assalamu alaikujml/m masu sauraro, sharhin bayan labarummu zai yi magana danagne da zanga-zanga masu yawa wadanda ake yi a kasashen larabawa a dai dai lokacinda HKI take kara tsananta kisan kiyashi a yankin Zirin gaza, wanda ni tahir amin zan karanta. ////.. Madalla, a dai-dai lokacin da sojojin HKI suke kara yawan hare-haren da suke kaiwa Falasdinawa a Gaza, da kuma yadda suke kara kissan kiyashi a yankin, an gudanar da zanga-zanga a kasashen larabawa da dama a ranar litinin, inda mutane a birnin Damaskus na kasar Siriya suka fito kan tituna a birane da dama a kasar suke allawadai da HKI da kuma karin dauke rayukan falasdinawa da take yi a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran...
Jam’iyyar Labour (LP) ta yi barazanar dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da ɗan takarar shugaban kasa na 2023, Peter Obi, idan ba su daina abin da aka kira “aikin da ba a goyon baya” ba. Wannan barazanar ta fito ne bayan taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda aka zargi Otti da shirya taron ba bisa ƙa’ida ba da kuma shirin raba jam’iyyar gida biyu. LP ta kuma nuna damuwa kan shirin Otti na kiran wani taron NEC a ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda aka ce zai kawo cikas ga haɗin kai na jam’iyyar. Haka kuma, jam’iyyar ta gargaɗi Peter Obi game da matakan da za su iya kawo rushewar jam’iyyar, tana...
Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da wadannan hare-hare tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin jama’ar Jihar Filato. ACF ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da hada...
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da ƙananan yara. ’Yan sanda sun soke gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da waɗannan hare-hare tare da miƙa sakon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma ɗaukacin jama’ar Jihar Filato. Ƙungiyar...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu nay au zai yi magana kan cewa “Amurka ba zata taba zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da Falasdinawa ba” wanda ni tahir amin zan karanta. A dai dai lokacinda rikicin gaza ya zama matsalar ta duniya a halin yanzu, da dama daga cikin masana suna ganin gwamnatin Amurka wacce ta kasance mai goyon bayan HKI na asali ba zata kuma zama mai shiga tsakanin don kawo karshen rikicinta da falasdinawa ba. Dangane da wannan shafin yanar gizo mai suna “Alkhanadik’ ya rubuta wani sharhi dangane da yakin na gaza a jiya Asabar yana cewa, a dai dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka ta kasance bangare babba a cikin haddasa matsaloli ga al-ummar Falasdinu na...
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka. Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman...
A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027. An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi. An tuhumi Le Pen tare da wasu manyan yan jam’iyyar tata guda 20 da daukar masu taimaka musu aiki wadanda suka yi wa jam’iyyarta aiki maimakon Majalisar Turai wadda ita ce ke biyan ma’aikatan albashi. Ms Le Pen, mai shekaru 56, ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2027 ba, inda a yanzu ake ganin ita...