Shugaban Amurka Ya Ce An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Indiya
Published: 10th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, wanda Amurka ta shiga tsakani wajen kulla ta.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, da aka samu, inda ya yaba da amfani da hankali da basirar da kasashen biyu suka nuna wajen daukar wannan mataki.
Wannan sanarwar ta zo ne a wani lokaci mai muhimmanci, yayin da alakar Indiya da Pakistan ke samun tangarda da kuma bullar takun-saka a tsakaninsu a ‘yan shekarun nan, musamman kan batun Kashmir.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
Aƙalla jami’an tsaro 53 aka kashe a sassa daban-daban na Nijeriya cikin makonni biyu da suka wuce, bisa ga ƙididdigar da muka tattaro daga rahotannin kafofin yaɗa labarai.
Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da sojoji da ’yan sanda da jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula (NSCDC), jami’an shige da fice da na kwastam, da ma jami’an sa-kai da ke taimaka wa jami’an tsaro, ciki har da ’yan sa-kai na JTF da na ƙungiyoyin tsaro na al’umma da gwamnatocin jihohi suka kafa.
Yawancin waɗanda aka kashe, ’yan bindiga ne suka halaka su yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma a lokacin hari, yayin da wasu kuma aka kashe su ne a wuraren binciken tsaro da sansanoninsu.
Wannan adadi ya taƙaita ne kan alkulman da muka tattara daga rahotannin kafofin yaɗa labarai, bai haɗa da wasu hare-haren da ba a bayyana su ba ba.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a KogiWani bincike da muka gudanar a watan Disambar bara ya nuna cewa, daga watan Janairu 2023 zuwa Oktoba 2024, aƙalla jami’an ’yan sanda 229 aka kashe a faɗin ƙasar nan.
Binciken ya bayyana cewa ’yan bindiga, ’yan ƙungiyar IPOB da ’yan Boko Haram da ’yan fashi da makami da kuma ’yan ƙungiyoyin asiri ne suka kashe jami’an tsaron.
Sabbin hare-haren sun faru ne a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe ’yan sanda bakwai da wasu jami’an tsaro a lokuta daban-daban a ranar Juma’a da kuma jiya Lahadi.
Baya ga waɗanda aka kashe, an kuma sace wasu jami’an tsaro a harin da aka kai a Binuwai.
A ’yan kwanakin nan, Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar da mutane tara a gaban kotu bisa zargin hannu a kisan gilla da aka yi a jihohin Binuwai da Filato.
An kai su gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda kuma aka tuhumi wani da ake zargi da fataucin makamai bisa mallakar bindigogi ƙirar M16 guda bakwai ba bisa ƙa’ida ba.
Cikin waɗanda aka gurfanar har da Haruna Adamu da Muhammad Abdullahi, ’yan asalin Karamar Hukumar Awe a Jihar Nasarawa, da ake tuhuma da laifuka huɗu kan kashe-kashe a Abinsi da Yelewata a Ƙaramar Hukumar Guma ta Jihar Binuwai a ranar 13 ga watan Yuni.
Haka kuma an gurfanar da Terkende Ashuwa da Amos Alede, dukkansu daga Guma, kan zargin kai farmaki don ramuwar gayya da kuma lalata dukiya, wanda ya haddasa salwantar shanu 12 a garin Ukpam.
Daga:
Sagir Kano Saleh, Abdullateef Salau, Idowu Isamotu (Abuja), Hope Abah (Makurdi), Tijjani Labaran (Lokoja) & Abubakar Akote (Minna)