2025-12-06@20:16:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9463
«mataimakin gwamna»:
Sabon bashin, ya nuna yadda Bankin ya bai wa kasar bashin da ya kai jimlar dala biliyan 5.1 tun daga ranar 31 na watan Okutobar 2025. Kazalika, wannan sabon bashin, zai taimaka wa kashi na biyu na shirin habaka tattalin arziki a bangaren samar da makamashi da sauye-sauye, a fannin makamashin da cimma burin da...
Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar...
Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas. An ɓoye hodar cikin ƙananan jakunkuna biyar. ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista...
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar. Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar...
An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo. Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa. ’Yan...
Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...
’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno. An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa. Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar...
Kungiyar kwallon kafa ta Iran “Time Milli” Ta Fada ‘Group H’ a rabon da aka yi na gasar kwallon kafa ta FIFA 2026 wanda za’a gudanar a kasashen Amurka Canada da kuma Mexico a shekara mai zuwa. Group H dai ta kunshi Iran,Masat Belgium da New Zealand. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya...
Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS. A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban...
Kasashen Larabawa da musulmi 8 ne suka gamu suka ki amincewa da shirin HKI na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tanakalto ministocin harkokin kasashen waje na kasashen Saudia, Masar, Jordan, da UAE Pakisatan Turkey da kuma Qatar sun bada bayanin hadin giwa daga kasashen Saudiya kan cewa...
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin...
Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da...
Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani. Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu...
Pars Today – Hanieh Rostamian, jarumar harbin bindiga ta Iran, za ta fafata a wasan karshe na gasar cin kofin duniya. Za a fara gasar cin kofin duniya ta 2025 gobe, Asabar, a Qatar. A cewar Pars Today, tunda manyan ‘yan wasan harbi na duniya suna shiga wannan gasar, Hanieh Rostamian—wanda a halin yanzu yana...
Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 20, kwangilolin haɗin gwiwa na fasaha guda biyar
Pars Today – Ziyarar da tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai Rasha a fannin sadarwa da fasahar sadarwa ta zamani ta haifar da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatoci guda 20, da kuma kwangiloli biyar tsakanin kamfanoni daga kasashen biyu. Meysam Abedi, Mataimakin Ministan Sadarwa da Fasahar Sadarwa ta Duniya kan Fasaha...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya yi zargin cewa ƙasashen waje na taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda Najeriya. Sheikh Ahmad Gumi ya danganta ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan da irin maganganun da ƙasashen waje suka riƙa yi a kai. A yayin wata hira da BBC Hausa, malamin ya bayyana...
Makwanni biyu bayan da masu garkuwa su ka sace kananan yara ‘yan mamaranta an bayyana cewa;har yanzu da akwai 250 a hannun barayin mutanen. A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai masu dauke da makamai su ka kutsa cikin wata makaranta ta majami’ar Roman Katolika, su ka yi awon gaba da dalibai 300 da...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin wanda ya kai ziyarar aiki kasar India ya bayyana cewa kasar tasa da kuma abokiyar kawancenta India za su bunkasa kasuwancinsu. Ziyarar ta shugaban kasar Rasha a Indiya, tana a karkashin taron da kasashen biyu suke yi ne daga lokaci zuwa lokaci wanda wannan shi ne karo na 23 da...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da...
Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda
Fadar gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar. Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da...
Limamin Juma’ar Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi Ishara da yadda tsarin tsaron ‘yan sahayoniya ya rushe a yayin yakin kwanaki 12, yana mai kara da cewa; A wancan yakin na kwanaki 12 an murkushe abokan gaba, don haka idan har su ka sake yin wani gigin to za a sake murkushe su.” Ayatullah...
Daga Usman Muhammad Zaria Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa. Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare...
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026. Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta...
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP. Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama. Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa...
Wasu magidanta a garin Malam-Sidi, da ke Ƙaramar Hukumar Kwami a Jihar Gombe, sun yaba da aikin haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Gombe da UNICEF sula yi wajen rage matsalar ƙarancin abinci a tsakanin ƙananan yara. Shirin, wanda ake kira PARSNIP, yana bai wa yara masu shekaru 6 zuwa 23 wani nau’in abinci na musamman mai...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar maharba, sun samu nasarar tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da aikata laifuka a Jihohin Gombe, Bauchi, Yobe da Adamawa. Rundunar ta samu nasarar ne bayan kama Abdullahi Ibrahim, mai shekaru 40 daga ƙauyen Tilde a Funakaye, a...
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke...
Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa...
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka...
Kasashen Iran da Pakisatan sun amince sun dawo da zirga-zirgan jiragen kasa tsakanin birnin Istambul na kasar Turkiyya zuwa birnin Tehran na kasar Iran da kuma birnin Islamabda na kasar Pakistan a cikin wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran yanakalto jakadan kasar Iran a Islamabad Dr RezaAmiri Moghaddam yana fadar haka a...
Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya...
Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na Naira tiriliyan 12.8 daga watan Agustan 2024 zuwa Oktoba 2025, bisa ga bayanan da Hukumar Kula da Rarraba Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta fitar. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ƙoƙarin ƙara samar da man fetur a cikin gida, duk kuma da...
Pars Today – Vladimir Putin ya yi tafiya zuwa Indiya don ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Vladimir Putin, shugaban Rasha, ya isa New Delhi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba, a ziyararsa ta farko zuwa Indiya tun bayan fara yakin Ukraine a 2022. Ziyarar ta kwanaki biyu na da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin tsaro da...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya...
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya...
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Olmert da kuma ministan harkokin waje Tzipi Livni bisa rawar da su ka taba a baya a laifukan yaki a Gaza a tsakanin 200-2009. Kungiyoyin...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin bude tayin bada kwangilar samar da wutar lantarki a wasu garuruwa dake kananan hukumomin Jihar. A lokacin da yake jawabi a yayin gudanar da bikin daya gudana a sakatariyar Jihar dake Dutse, Shugaban hukumar, Injiniya Zubairu Musa ya bayyana cewar tayin bada kwangilar samar...
Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka...
Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda...
Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) shiyyar Kano, ta kama wani mutum da ya yi yunƙurin safarar wasu mata bakwai zuwa Saudiyya. Jami’an NAPTIP sun kai samame wani gida a Kano a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2025, bayan samun bayanan sirri, inda aka ɓoye matan da ake shirin safararsu. Na gana da Tinubu kan Kanu...
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, ba ta shafi batun sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC ba, sai dai a kan shugaban ’yan awaren ƙungiyar Biyafara, Nnamdi Kanu. Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fayyace cewa ziyarar ta biyo bayan...
MDD ta bukaci a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma janyewa daga Tuddan Golan na Siriya
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya. Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu. Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin...
Rundunar Sojan Ruwa ta IRGC ta fara wani atisayen soji a yankin kudancin Iran a Tekun Fasha, wanda ya kunshi rundunonin sojoji da dama. An yi wa atisayen lakabi da “Eightedar” (Ikon Kasa), domin girmama kwamandan da ya yi shahada Mohammad Nazeri, wani babban jami’in sojin ruwa na IRGC. Ana gudanar da atisayen a cikin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka...
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene. Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja. Jirgin fadar shugaban ƙasa...
Dan wasan taekwando na kasar iran Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center...