NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis a al’aurarta
Published: 12th, May 2025 GMT
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta sanar da cafke wata mata da ta ɓoye hodar iblis tana shirin tafiya ƙasar Iran.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama matar ce a filin jirgin sama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Muna bayan Tinubu a Zaɓen 2027 — Patience Jonathan Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670Babafemi ya ce matar ta ɓoye hodar iblis ɗin a cikin al’aurarta da cikinta da kuma a wata jaka.
A cewarsa, matar mai suna Ihensekhien Miracle Obehi, wadda ta saka hijabi domin ƙoƙarin tsallake binciken jami’an tsaro, an cafke ta ne a Lahadin da ta gabata lokacin da take yunƙurin shiga jirgin Qatar Airline zuwa Doha, kafin ta wuce Iran.
Ya ƙara da cewa yayin bincike, an gano matar ta saka ƙunshin hodar iblis har uku cikin al’aurarta, sannan ta saka wani a jakarta sai kuma ta haɗiye ƙwayoyi 67 a cikinta.
Sai dai mai magana da yawun hukumar ya ce an tilasta wa matar yin aman ƙwayoyin da kuma ƙunshin waɗanda ta haɗiye a cikinta da na ɓoye a al’aurarta.
Obehi ta yi iƙirarin cewa an buƙaci ta haɗiye ƙwayoyin hobar iblis 70, sai dai bayan haɗiye 67 ta kasa haɗiye sauran — inda ta yanke shawarar saka su a al’aurarta, a cewar Babafemi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: al aurarta hodar iblis hodar iblis
এছাড়াও পড়ুন:
Matan Falasdinawa A Gaza Suna Fama Da Yunwa Mai Tsanani Da Kuma Hare-haren HKI
Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI.
Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu.
A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da su ka yi shahada sun kai 12,000 da 400. Bugu da kari wasu matan da sun kai 14 sun bace ba a gano su ba, sai kuma wasu matan masu ciki da sun kai 60,000 da suke fuskantar hatsari mai tsanani saboda rashin kula da su, da kuma rusa asibitoti da sojojin HKI su ka yi.
A cikin wani tanti a Khan-Yunus da akwai wata mace mai suna Ummu Muhamad da take rayuwa da ‘ya’yanta 7, bayan da maigidanta ya yi shahada sanadiyyar harin sojojin HKI.
Matar ta bayyana cewa, baya ga mijinta da akwai wani daga cikin ‘ya’yanta da ya yi shahada, kuma su da suke a raye suna da bukatuwa da magungunan da samunsu yake yin wahala saboda halin yaki da ake ciki.
Ta kuma bayyana cewa; Muna fama a yunuwa mai tsanani,babu wanda zai taimake mu, kuma fulawar da ake da ita, ta yin burodi ta kare.