Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci
Published: 9th, May 2025 GMT
Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama mai dadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya.
Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu dabbar da zai yi ba, sai ya yi azumi na kwana uku a Makka kafin a fita zuwa Arfa idan zai yiwu.
Amma kuma kar ya zama Alhaji yana da halin yin hadayar sai ya yi wa Allah rowa ya ki yi ya ce shi azumi zai yi. Wannan babu kyau. Ana samun wadanda suke da halin kudi su ki yi, sun gwammace su kullo kudin guzurinsu su dawo da shi gida, wannan yi wa Allah rowa ne. Azumin da aka ce a yi na kwana uku a Makka da kwana bakwai a gida, ya ta’allaka ne ga wadanda ba su da halin yin hadaya kwata-kwata. Ko ya kasance idan suka sayi dabbar hadayar za su galabaita saboda karancin kudin abincinsu. Don Allah jama’a mu kiyaye. Rowa haka kawai ma babu kyau a addini ballantana kuma wurin yin ibada.
Malamai Fakihai, Allah ya yarda da su, sun yi sabani a kan a cikin nau’o’in Aikin Hajjin nan uku; wanne ne ya fi. Shafi’awa sun tafi a kan cewa Ifradi da Tamattu’i sun fi Kirani a wurinsu. Domin a fahimtarsu, Kirani kamar Tamattu’i ne kawai. Har ila yau, a cikin su Shafi’awan akwai wadanda suke ganin yin Tamattu’i ya fi, akwai kuma wadanda suke ganin yin Hajjin Ifradi ya fi sauran.
A wurin Malikawa, Ifradi ya fi sauran. Hanabilawa kuwa sun tafi a kan cewa yin Hajjin Tamattu’i ya fi Kirani kuma ya fi Ifradi. Saboda Tamattu’i ya fi sauki ga mutane, domin musamman mutanen da suke kasashen da ke nesa da Makka, ba za su iya kore dabbobin hadayarsu zuwa can ba (musamman a wannan zamanin). Kuma sun ce Tamattu’i ne Annabi (SAW) ya yi burin yi, ba domin ya taho da dabbobin hadayarsa ba.
Imam Muslim ya ruwaito Hadisi daga Ada’u ya ce “Na ji Jabir bin Abdullahi (RA) ya ce ranar da muka zo Aikin Hajji (lokacin farko da Annabi (SAW) ya ce a zo a ga yadda zai yi), mu Sahabbansa dukkanmu mun yi niyyar Aikin Hajji ne kadai – ba tare da Umura ba. Sai Annabi (SAW) ya zo mana kashe-gari ya umurce mu mu warware haramarmu, mu sadu da iyalanmu. A wannan lokaci ba wai tilasta mana ya yi a kan haka (saduwa da iyali) ba. Amma ya halasta saduwa da su ne don nuna warware harama. Sai muka ce ma sa – Ya Rasulallah (SAW) – tsakaninmu da ranar Arfa bai fi kwana biyar ba. Yanzu za mu iya zuwa Arfa alhali mun sadu da iyali? Sai Annabi (SAW) ya mike a cikinmu ya ce, “Jama’a ku sani fa na fi ku tsoron Allah, na fi ku gaskiya fa, ni kaina ba don wannan hadayar tawa ba; ni ma da na warware kamar yadda za ku warware. Idan na sa gaba kan abin da Allah ya ce in yi ba na juya baya, don haka ku warware.” Sai muka ce mun ji mun bi.”
Daga ma’anar wannan Hadisin, Hanabilawa sun fi kusa kenan da abin da Annabi (SAW) ya so wa al’ummarsa a cikin wadannan nau’o’in Hajjin guda uku.
Ya halasta idan wani Alhaji duk bai san wadannan nau’o’in Hajjin ba, a gwaggwada ma sa yadda zai yi Aikin Hajjin (ko da bai ambaci nau’in da zai yi ba), bayan an gama sai a yi ma sa aski ya warware haramarsa kuma Hajjinsa ya yi.
A nan za mu dakata sai mako mai zuwa, Insha Allah. Allah ya amshi dukkan ibadunmu albarkar Sayyidina Rasulullah (SAW), amin.
– Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci
Daga lokacin da mutum ya yi harama da aikin Hajji, duk wani abu na kayan ado ya haramta gare shi, sai dai abin da ba a rasa ba.
Daga cikin abubuwan da aka halasta ma sa akwai yin wanka idan ya yi dauda, watakila saboda doguwar tafiya ko kuma wanda yake Hajjin Ifradi ne da zai kwashe wasu kwanaki cikin harama ko ga wanda ya samu janaba.
A cikin Muwadda, Imam Malik ya ruwaito daga Nafi’u, daga Abdullahi bin Umar (RA) cewa shi (Abdullahi bin Umar) ya kasance yana yin wanka kuma har ya wanke kansa alhali yana cikin harama. Abin da ya sa ake tsoron wanke kai shi ne don a kiyaye cire gashi.
Har ila yau, a cikin Muwaddan, Imam Malik ya ce Abdullahi bin Umar ba ya wanke kansa idan ya zo yin wanka bayan ya yi harama har sai idan ya samu janaba.
Imam Malik ya karhanta mutumin da ya yi harama ya game kansa da ruwa (kurmani).
Malamai sun ce ya halasta a yi wanka da sabulu bayan an yi harama domin cire dauda. Kuma ya halasta a goge baki da makilin da sauran su. Wannan ma ya halasta a wurin Hanabilawa da Shafi’awa ba ga Malikawa ba kawai, koda kuwa sabulun yana da kamshi.
Ya halasta mai harama ya rufe fuskarsa saboda warin wani abu ko kura.
Idan mai harama ya rufe kansa da mantuwa ko saboda rashin sani, babu komai a kansa. Sai dai kawai a ce ma sa ya cire. Haka nan wanda ya yanke farcensa da mantuwa ko rashin sani, sai ya yi Istigfari.
Ya halasta ga mai harama ya yi kaho idan ya kamu da rashin lafiya. Zai iya matse kurji ko cire hakori ko yanke wata jijiya a jiki ko wani abu da za a yi wa mai harama a asibiti don ya samu lafiya. Ya tabbata cewa an yi wa Manzon Allah (SAW) kaho a tsakiyar kai alhali ya yi harama da Hajji.
Imamun Nawawi ya ce sun tafi a kan cewa za a iya yi wa mai harama kaho koda kuwa za a yanke gashi a wurin. Yin hakan babu laifi, amma kawai haka mutum ya sa a yi ma sa ba tare da wata bukata ba, wannan laifi ne.
Ya halasta ga mai harama ya yi susa a jikinsa. An tambayi Ummul Mumina Aisha (RA) cewa mai harama zai iya yin susa? Ta ce “eh, zai ma iya kai isa matuka wurin susan jikinsa”.
Babu laifi ga mai harama ya shaki kamshi ko ya kalli madubi. Sai dai Malikawa da Hanafiwa sun karhanta zama a wurin da yake akwai turare mai kamshi.
Haka nan, babu laifi mai harama ya daura jakar kudinsa a jikinsa ko sanya zobe a hannu. An ruwaito wannan daga Abdullahi bin Abbas (RA).
Ya halasta mai harama ya sanya kwalli na magani (idan idonsa yana ciwo), matukar kwallin ba mai hade da turare ba ne.
Babu laifi mai harama ya yi amfani da lema saboda ruwa ko rana ko kuma ya shiga cikin wata rumfa.
Mace za ta iya yin kunshi (lalle) kafin ta yi harama da Hajji, amma ban da bayan yin harama. Domin Malaman Malikawa da Hanafiyawa sun ce yin lalle bai halasta ba a ko wane bangare na jiki bayan an yi harama, walau a wurin mace ko namiji.
Wakazalika, babu laifi mai harama da Hajji ya kashe dabbobi masu cutarwa. Annabi (SAW) ya lissafa wasu dabbobi a matsayin fasikai da za a iya kashewa wadanda suka hada da: Hankaka, Shirwa, Kunama, Vera da Kare Mai Cizo.
Haka nan za a iya kashe maciji, zaki, damisa, kura da sauran abubuwa masu cutarwa. Masu dabbobi za su iya kashe kaska. Shi ma dan fashi za a iya yakarsa.
A takaice dai duk wani abu mai cutarwa za a iya kashe shi, amma idan ba ya c
utarwa ko an gan shi kar a taba shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: mai harama ya ya yi harama
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Muhimmin Aikin Makarantar “Hauza” Shi ne Isar Da Sakon Addini
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa, ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.”
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga cikin ayyukan cibiyar ilimin ta Hauza da akwai Shata muhimman layukan da za a gina ci gaban musulunci na zamani akansu, da kuma isar da sakwanninsa a cikin al’umma, kamar kuma yadda aikin Hauzar ne ta yi tarbiyyar mutane su zama masana.
Tun da fari, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fara da bijiro da takaitaccen tarihin kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza a Kum, da rawar da Ayatullah Haj Sheikh Abdulkarim Ha’iri ya yi, har zuwa lokacin da ta rika bunkasa da ci gaba.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya bayyana Imam Khumaini ( q.s) a matsayin daya daga cikin malaman da Hauza ta haskaka da su, wanda ya yi nasarar kawo karshen tsarin sarauta na maha’inta.