-
Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro. Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a waɗannan ƙasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da...
-
Kungiyoyin ma’aikata na Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, Kafanchan sun bayyana aniyarsu na fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku. Sun ce za su shiga yajin aikin ne daga ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Wannan matakin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da suka yi bai wa gwamnatin jihar, wanda zai kare ranar Laraba, 18 ga watan Yuni. Majalisa ta aike wa Tinubu...