Matan Falasdinawa A Gaza Suna Fama Da Yunwa Mai Tsanani Da Kuma Hare-haren HKI
Published: 11th, May 2025 GMT
Falasdinawa mazauna yankunan Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza suna fama da matsananciyar yunuwa, a lokaci daya suna fuskantar hare-hare masu tsanani daga sojojin HKI.
Mata mazauna yankin sun fi fuskantar matsaloli saboda kananan yaran da suke tare da su, alhali kuma an rushe gidajensu.
A tsawon yakin kisan kiyashin da HKI take yi, matan da su ka yi shahada sun kai 12,000 da 400.
A cikin wani tanti a Khan-Yunus da akwai wata mace mai suna Ummu Muhamad da take rayuwa da ‘ya’yanta 7, bayan da maigidanta ya yi shahada sanadiyyar harin sojojin HKI.
Matar ta bayyana cewa, baya ga mijinta da akwai wani daga cikin ‘ya’yanta da ya yi shahada, kuma su da suke a raye suna da bukatuwa da magungunan da samunsu yake yin wahala saboda halin yaki da ake ciki.
Ta kuma bayyana cewa; Muna fama a yunuwa mai tsanani,babu wanda zai taimake mu, kuma fulawar da ake da ita, ta yin burodi ta kare.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Colombiya Ta Birnin New York A Amurka Ta Dakatar Da Karatun Daliban Jami’ar Fiye Da 65
Hukumomi a Jami’ar Colombia dake birnin NewYork na kasar Amurka sun bada sanarwan cewa, sun dakatar da karatun daliban jami’ar fiye da 65 saboda shiga cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da babban dakin ajiyar littafai ko karatu a Jami’ar a ranar Laraban da ta gabata.
Tashar talabijin ta Press tv a nan Tehran ta nakalto kakakin Jami’ar a jiya Jumma’a na cewa a ranar Laraba yansandan NewYork sun kama talibai kimani 80 inda suke tsare da su, a halin yanzu suke kuma ci gaba da gudanar da bincike a kansu. Amma duk da haka an dakatar da karatun wasu daga cikinsu zuwa wani lokaci nan gaba.
Labarin ya kara da cewa akwai wasu karin mutane 33 wadanda Jami’ar ta dakatar saboda hannun a cikin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawar.
Labarin ya bayyana cewa hotunan bidiyo na tsaro a dakin karatu na Jami’ar sun nuna daliban suna shiga dakin sannan jami’an tsaro suna binsu suna kamawa, sannan wasu daga cikinsu na sanye da ‘Keffiyeh’ wani kelle wanada yake nuna alamar Falasdinawa.
Jami’o’ii da dama a Amurka suna gudanar da irin wannan zanga-zangar, don nuan rashin amincewarsu da kissan kiyashen da HKI take yi a gaza tun shekara ta 2023 ya zuwa yanzu, da kuma tallafa mata wanda gwamnatin kasar ta Amurka take yi.